💦💦 *ZABIN ALLAH*💦💦
~nake nema~*True life story*
*💦Talented writers forum*💦
*{T.W.F}*
*Written by husnah mb**🙏🏻Dedicated to Teemah jalo*🙏🏻
Thanks for ur support All the tym...
*2⃣3⃣-2⃣4⃣*http://husnahmb.blogspot.com
Nan take sukayi calling atention din mutanen yan department dinsu" duk wanda yasan halinsu sai Allah yashi kara yake musu yayinda wasu suke ke tausaya musu dan sunsan kaddarace ta sauka a kansu da kyar mustapha da abdul suka rarrashesu sunfi 20 minutes suna rarrashinsu kafun su tsagaita kukan nasun su koma hostel dan capteria da basuje ba kenam.
Tunda suka dawo hostel su haidar babu abunda suka sai aikin kuka abdul da mustapha kam sunyi rarrashi harsu gashi da suka fahimci ba sauraransu sukeyi ba haka suka hakura suka barsu.
_The next day_
First thing in the morning nasreen ce kwance saman gado sai sharan baccinta take hankali kwance danko yau babu school islamiyya kuma dama tace bazataje ba dan revision akeyi"
Sanye take da white nd pink din night gown wanda da kadan ta wuce gwiwanta dogaye fararan kafafunta a bayyane suke inda gashin kanta kuwa ya rufe mata fuska gabaki daya"
Affan ne ya shigo cikin gida yana gwalawa nasreen kira" kiran da ummy tajine yasata tayi saurin fitowa, affan ne yace ummy ina baby nasreen tun dazu na shigo ina kiranta but bata amsa ba kodai ta tafi school ne murmushi ummy tayi sannna tace babu inda taje tana dakinta' may be tana bacci ne shiyasa."Dakinta ya nufa direct handle din kofan ya murda cikin sa'a kuwa sai yaji a bude ne hakan yasa yasa kanshi kawai ya shiga ba tare da sallama ba" lil sis! Lil sis!! Shiru bata amsa ba daga kanshi da zaiyi saiya hangota saman gado tana bacci, cikin yanayin daya gantane yasa ya tsinci kansa a wani irin bakon yanayi a hankali ya karisa shigowa dakin bakin gadon ya zauna zura mata ido yayi yana kallonta tundaga saman kanta har tafin kafanta" haka kawai yaji ya tsinci kansa cikin nishadi da shauki wanda shi kanshi baisan daga ina yazo bah, harya bude baki zaiyi magana sai kuma yayi saurin sa hannunshi a bakinsa dan yanayin da yaga tana baccin hankalinta kwance' so shiyasa bazaiso ya katse mata shiba'
Haka yaja jiki ya fita kwata kwata jikinsa babu kwari dan duk yanayin daga nasreen aciki ya saukar masa da kasala, hakan yasa bai zarce ko inaba sai dakinshi' saman gado ya kwanta sai tunanin nasreen yake wanda tunda ya dawo dakinshi tunaninta ya hanashi sukuni ko kulle idonshi yayi saiya ganta duk motsi kadan yayi kawai saiya fara wani murmushi" har bacci barawo ya saceshi.
*Monday morning.*
Abdul, haidar da sauran yan rooms mates dinsu ne suke zaune salees ne yayi tagumi' abdul ne yace _What happen with u_ my guy murmushin takaici salees yayi sannan yace my guy am in big trouble yanzu ace nayi failing 6 courses meye zanje na fadawa daddy nah sai kuma ya fashe da kuka.
A yanzu su haidar sunyi nadama dan sun gane illar rashin karatu dan haka sundau aniyar gyarawa hakan tasa yanzu karatu suke sosai babu kakkyautawa shiyasa koda yaushe suna tare da mustapha da abdul duk inda basu ganeba ba sai su abdul suyi musu explaninig saidau a kullum insu tuni carry over da suke dasu da kuma sabawa Allah da suka dungayi sukanyi kuka danma su mustapha suka kwantar musu da hankali a koda yaushe sun kuma nuna musu dasu dage da addu,a dan Allah gafurur rahim ne.
A haka har suka fara teses sosai suke karatu saidai wani lokacin insu shiga hall sukan manta abunda suka karanta musamman mah salees da damuwa yayi mishi yawa hankalinshi yana matukar tashi amma babu yanda ya iya addua, kawai yakeyi a koda yaushe.
_After Two years_
_Lokaci nata tafiya abubuwa da yawa sun faru ciki koh harda gama junior su nasreen yanzu haka suna Ss1" yanzu su Nasreen an zama yan mata._
Yanzu su nasreen sai shirye shiryen sauka akeyi dan yanzu haka sun gama shirya komai kawai rana suke jira dan har an buga Calender, memo, da jakakkuna jikinsu an rubuta _Congratulation for Qur'anic graduation._ Balkeesu abbakar sadeeq _(Nasreen)_, Aysha (Ashfat) & maryam (Naela). Tofah yanzu su Nasreen an girma har an zama malamai.🤣 lol
_The next day_
First thing in the morning Affan ya dauki nasreen zuwa saloon _Returching_ aka mata ba karamun kyau tayi ba affan ne ya biya kudin daga nan suka dawo gida.
Yau akayi sauka' Saukan daya samu halartan manya manyan malamai, yan siyada da masu fada aji any sauka lafiya Nasreen ne ta karbi kyautan datafi ko wata daliba gwazo da hazaka Naela da ashfat ma sun karbi tasu kyautan, a haka aka tashi daga taron kowa ya tafi gida cikin nishadi da farinciki.
Washe gari
Nasreen ce kwance a dakinta tana bacci cikin baccinta taji maranta yana mata ciwo a gigice ta tashi ta zauna jin abun yana karuwand yasa tayi saurin saukowa kasa ta xauna jin abun gaba yakeyi yasa ta fara zubda kwallo durkusawa tayi kasa hannunta kan maranta tana wash Allah"
Ihun data sakeni yasa ummy dake salla a dakinta tayi saurin yanke sallan ta fito da gudu dan yanda taji nasreen na ihun ba karamun razana tayi bah."Da gudu ummy ta karisa dakin nasreen durkushe ta hangota hawaye nabin kuncinta inda take ta karisa tare da tallafo fuskanta' habibty _what's wrong_ nasreen ta bude baki zatayi magana kuka ya kufce mata' momy ne tace habibty kiyi magana manah meya faru?
Kasanta tahau nunawa ummy dan gabaki daya jinine yake bin sawunta" murmushi ummy tayi sannan tace sorry habibty maza tashi kije kiyi wanka barinzo koh" to tace ummy ne ta kaita bandaki sannan ta fito ta gyara wajen daya baci"
Dakinta ta koma ledan pads guda daya ta ciro ta saka 'a jikin pants zama tayi tana jiran fitowan nasreen daga wanka"
_After 15 minutes_
Nasreen ne ta fito tana tafiya a hankali tamkar tana tambayan kasan kafun ta takashi kusa da ummy tazo ta zauna tanata kokarin harde kafa' ummy ne ta mika mata pant din tace ta saka tsayawa tayi tana karewa pants din kallo wanda yake dauke da pads aciki, ummy ne ta girgiza mata kai alaman ta saka" bata mata musu ba ta saka bakan doguwar riga ta dauko acikin wadrop blue nd white ta saka ba karamun kyau yayi mata ba duk da kuwa fuskanta ya jajjeme dan kana ganinta kasan batajin dadi.
"Ummy ne tace habibty cikin bada hankalinta inda ummy take magana tace na'am ummy nah
Habibty kinga wannan jinin da kike gani koh ba wai bakida lafiya bane' lafiyanki qlau wannan jinin shi ake kira da jinin haila' sunkuyar da fuskanta nasreen tayu wani kunya taji ta kamata wanda tunda take bata tabajin kunyan ummy ba irin na yau'
Ummy ne tace nasan basai nayi miki bayani ba kinsan komai dan an muku a islamiyya' ummy ne tace ko akwai abunda baki gane bah' a,a na gane komai ummy nasreen ta amasa mata dashi kanta a sunkuye"Ummy ne tace Allah ya miki albarka Maza tashi kije kici abinci zan kawo miki magani kisha zaki danji saukin ciwon cikin koh toh tace tare da tashi ta nufi dakin ummy.
Add dis no to join my whatsapp group
08109990994_Husnah mb ce_✍🏻
YOU ARE READING
ZABIN ALLAH
RomanceWannan labari ne akan wata yarinya data fada tarkon soyayya wanda ya kunshi abubuwan da suke faruwa da dama a duniya musamman mah" ga ma'abota soyayya