ZABIN ALLAH

533 26 0
                                    

💦💦 *ZABIN ALLAH*💦💦
              ~nake nema~

*True life story*

*💦Talented writers forum*💦

          *{T.W.F}*
    
    
*Written by husnah mb*

*🙏🏻Dedicated to Teemah jalo*🙏🏻
   Thanks for ur support All the tym...

*1⃣1⃣-1⃣2⃣*

Abba ne yace haba mama na meye kuma na kuka kiyi shiru abunki nama canza miki shi kinji
"Zansa a duba miki wani teacher wanda ya iya teaching sosai

Da sauri nasreen tace a,a abba yaya nasir yace zaina yimun kuma kaga shima teacher ne
Shiru abba yayi sannan yace nasir dinne ya fada ko kuma ke kikeso da sauri nasreen tace shiyace xaina yimun

Dariya abba yayi sannan yace to shikenam babu matsala ki tambayeshi nawa zanna biyanshi per mouths
To shikenam abba nah na gode sosai ta fada tana dariya

Abba ne yace shikenam ina ko mama na daga masa kai tayi alaman eh tashi tayi ta fita da gudu tana tsalle.

_Washe gari_

Da Nasreen taje islamiyya kin kula kowa tayi sai wani shan kamshi takeyi yan class dinsu kuma wanda basa kulata dama sai wani binta sukeyi waisu a dole sun samu mai tsare musu fada, ganin da Naela tayi kowa ya koma gun nasreen shiya kara bakanta mata rai haka dai har aka tashesu kowa ya watse.

_2 weeks later_

*Nile university abuja*

Saurayine dan kimanin shekaru ashirin a duniya
fari ne dogo mara kauri
yanada kyau daidai gwargwado suna matukar kama da nasreen dan kaman an tsaga kara saidai tadan fishi haske da kuma kyau, yana sanye da bakin jeans trouser da white polo shirt kafansa sanye yake da takalmi _Batozi_ Abdul kenam. Brother Nasreen wanda take binsa.
Abdul yarone mai hankali da nutsuwa, duk yanda yan mata da dama suke binsa amma kwata kwata baya harkansu hasalima tun bayan soyayyan da yayi a secondary school bai kara tunkarar wata mace da sunan so ba har 'ah yanzu.

Ko,a cikin school mutane da dama inya wuce xaginsa sukeyi saboda bai ciki shiga harkan mutane bah abunda ya kawoshi kawai yakeyi koh room mate dinshi complain dinshi sukeyi yanda baya biye musu suna zuwa party cikin dare.

Yau suka kare exams dinsu na first semister Abdul ne da sauran room mate dinsa suke jera kayansu a cikin trolly 

_The following day_

Around 10 o'clock su nasreen ne zaune a palo sunayin breakfast itada ummy, Anty amarya da yaya affan Sallama momy ta jiyo kaman anayi anty amarya ne tace Nasreen maza tashi ki duba da sauri ta mike dan taji kaman muryan Yaya naseer ne tana fitowa sukayi kicibus da Nasir a bakin kofa da sauri ta karisa inda yake Bro 2days ta fada tana dariya naseer ne yace lil sis lafiya 2days na daina ganinki dariya tayi sannan tace bro ai kwana 2 ban zuwa islamiyya shiyasa kasan anbamu hutu two days owk ya amsa dashi yana tambayanta ina ummy tana falo ta bashi amsa dashi oya muje na gaisheta gaba tayi ya bita a baya sallama yayi anty amarya ce ta amsa tsugunawa yayi ya gaidasu duka sannan ya mikawa Affan hanu suka gaisa.

Waje suka fito tare da Nasreen yana rike da hannunta a dakalin kofar gidansu suka zauna sai surutu sukeyi dan kwana 2 basu haduba nasreen ta tara masa labarai.

Nasreen ne tace bro kasan meyene girgiza mata kai yayi ranan naje gun abba nacemai kai zakana min lesson yanzu har uncle sagir ma ya daina zuwa dariya nasir yayi sannan yace haba dai eyii ta fada tana dariya
  "Naseer ne yace to yaushe zamu fara kenam sis shiru tayi alaman tana tunanin yau ta fada tana dariya naseer ne yace yau kuma lil sis kin shirya ne eh tace tana kallonsa
  Bro kasan hutun mu ya kusa karewa fah so nake kafun na koma school na gama iya duk abunda za,a mana a term din da zamu shiga murmushi Naseer yayi yana jaddada wayo da basira irin na nasreen yarinyar akwai brain ya fada acikin zuciyarsa.

Ganin da tayi yayan natan yayi shiru ne yasa ta tabashi tana cewa bro lafiya kuma murmushi yayi sannan yace sis to maza jeki dauko textbooks din nakin ina jiranki da sauri ta tashi tana dariya tashiga gida.

Tana shiga dakinta tayi direct textbooks da note books dinta ta kwasho harda chalk ta fito tana sauri a hanya sukaci karo da yaya affan tsokananta yahauyi sun shirya da uncle sagir dinna dariya tana sannan tace a,a yanzu yaya Nasir ne zai namin lesson oh ya fada tare da wucewa ya barta a wajen, ita kuma ta nufi  hanya waje.
Saida ta fito ta tuno baka dauko key din class din da ake mata lesson dinba

''Fitowa tayi ta bawa nasir books din sanna ta koma cikin gida ta karbo key din agun ummy.

Saida suka zauna suka tsara abunda zasunayi kullum sannan kuma fara lesson english kadai yau yayi mata ba karamin dadin lesson dinshi nasreen taji ba dan duk yafima uncle sagir iya teaching da yake shi inskayi karatun 20 mints sai sunyi labarin ten mints kafun suci gaba shiyasa karatun yafi shiga.

Lesson din 2hours sukayi sannan Nasreen ta tattara books da chalks din duka, harzai tafi ta tuna abba yace ta tambayeshi nawa zaina biyanshi da sauri ta nufo inda yake naseer ne yahau tambayanta lil sis lafiya bro abba ranan yace na tambayeka nawa zai biyaka kudin lesson murmushi naseer yayi sqnnan yace sis kicewa abba nace kyauta zanna miki aike kanwatace dariya tayi sannan tace
Thank You bro insha Allahi inya dawo i will tell him waje ya fita ita kuma tashige cikin gida.

Yana tafiya yana tunanin brain irinta Nasreen dan tunda yake koyarwa bai taba ganin yarinya mai ilimi da saurin daukan abu ba irinta a ranshi yana fadin tabbas duk malamin da yayi wasa nasreen kureshi zatanayi dan irin sune student masu kure teacher's dinsu a class yana tafiya yana tunaninta yana dariya shi kadai kaman wani mental harya isa gida.

Nasreen tana shiga gida ta tarar da ummy a kitchen dakinta ta nufa direct a ajiye books din da suke hannunta sannan ta nufi kitchen ganin da tayi ummy sai faman aiki takeyi yasa tace ummy yau kuma kene da kanki a kitchen murmushi ummy tayi sannan tace bakisan yau Yaya abdul zai dawo daga school bako kinsan anyi hutu kyalkyalewa da dariya nasreen tayi sannan tace haba dai ummy dama yau yaya abdul zai dawo harsun gama exams murmushi ummy tayi sannan ta daga mata kai alaman eh da gudu ta nufi dakinta tana tsalle.

_few minutes later_

Ummy ne tahau kwallawa Nasreen kira da sauri ta fito tana fadin ummy lafiya kuwa ummy ne tace maza kije ki gyarawa Abdul dakinsa kinsan yana hanya to ummy nasreen ta amsa dashi tare da nufa dakin abdul

Share dakin nasreen tayi tas tayi morphing burner ta dauko a dakin ummy tasaka turare wuta nan da nan dakin ya dauki kamshi tamkar dakin amarya,  dakin ummy ta nufa sabon zanin gado a leda ta dauko warewa tayi ta shimfida. _(Niko cewa nayi lalle baby nasreen mijinki zaisha tsafta, irin wannan gyra haka. 🤣 lol)_

bayan ta gama da gudu ta nufi kitchen tana dariya kaman an mata kyautan aljanna ummy ne tace kedai har yanxu bazaki daina wannan gujegujen bako, bakiga yanzu kin girma bane dariya nasreen tayi sannan tace ummy na gama muje kiga dakin yaya abdul yanzu haryafi naki kyau dariya ummy tayi sannan tace to sannunki fa aiki bari inna gama abunda nakeyi a kitchen zanje na gani to tace tare da barin wajen.

Husnah mb ce✍🏻

ZABIN ALLAHWhere stories live. Discover now