ZABIN ALLAH

825 42 1
                                    

💦💦 *ZABIN ALLAH*💦💦
              ~nake nema~

*True life story*

*💦Talented writers forum*💦

          *{T.W.F}*
    
    
*Written by husnah mb*

*🙏🏻Dedicated to Teemah jalo*🙏🏻
   Thanks for ur support All the tym...

*5⃣-6⃣*

_I will like to use this opportunity to say a big thank You to Teemah jalo. Nd to all readers of ZABIN ALLAH? husnah love You all_.

A akan dakalin tsakar gida suka zauna sukata surutu aiko har nasreen ta manta da zuwa gidan kaka dan dama indai ta samu yaya naseer mantawa take da komai saboda yanda yake bata labarai kala kala, agogon hannunta ta dago da sauri danta duba worch ganin da tayi har 12:30 yasa tayi saurin mikewa naseer ne yace lafiya kuma baby nasreen murmushi tayi sannan tace wlh bro ina zaune sai surutu mukeyi harna manta da yau zanje gidan kaka kasanfa yau ranarta ne murmushi Naseer yayi sannan yace lil sis tare zamu tafi yanzu muje na rakaki inkinje gida kika shirya ina kofar gida saiki zo ki sameni mu tafi kinji lil sis dina murmushi tayi sannan tace to bro inna shirya zanzo na sameka.

Har kofar gidansu ya raka ta shiga gida sannan shi kuma ya juya gida,
  Tana shiga a tsakar gida ta tarar dasu Anty amarya da ummy.
Ummy ne tace yau ya akayi kika dade habibty tun 12 aka tasheku ina kika tsaya,
"Ummy naje gidansu Yaya Naseer ne na gaida umma tacema waina gaisheki dariya ummy tayi sannan tace habibty Yaya naseer kenam sannu da kokari to ina amsawa maza kije ki canza kaya abincinki yana kan dinning table to nasreen ta masa tare da shiga dakin ummy da gudu.

Dining area ta nufa bayan ta gama cin abinci ta fito dakinta ta nufa direct sai yanzu ta tuna da tab dinta da abba ya saya mata da sauri ta nufi inda tab din yake ganin da tayi harya cika yasa taketa Allah, Allah affan ya dawo dan shigowanta kaman taga dakinshi a rufe ajiye tab din tayi tashiga wanka uniform dinta ta cire tasa Atamfa red ba karamin kyau atamfan tayi mata ba abunka da farin mutum kwalliya ta zauna ta chaba kaman wata mai zuwa party dan nasreen uwarson kwalliya ce.

Zaune take a bakin mirriow sai kuma taji kaman ana kwalla mata kira da sauri ta leko waje Affan ne yace kekam wai meyasa kike hakane ata kiranki kaman kurma jibi yadda naketa kwalla miki kira amma bakijini ba
Murmushi nasreen tayi sannan tace ayya am so sorry bro wlh ina cikin dakine shiyasa,
Ina Tablet din affan ya tambayeta yana daki harma ya cika ai tun dazu nake naimanka kamin settings sai kuma naga bakana na fita ne ya fada yana dariya,
Dakin ta shiga shima ya bita a baya zama yayi bakin gadonta yana tsokananta wannan irin kwalliyan fah ina zataje haka yaya affan harka manta yaufa ranan kaka ce gidan kaka zanje manah na yini, to sannu yar gidan kaka ya fada tare da lakuce mata hanci,

Settings din komai da komai yayi mata sannan ya bata tablet din yayi tafiyarsa fitowa tayi cikin zumudi dakin Anty amarya ta fara shiga ta nuna mata sannan ta nufi dakin ummy a falo ta sameta tana kallon _Twince of heart_ da gudu taje ta fada jikin ummy tana nuna mata tab din da abba ya saya mata karba ummy tayi ta gani ta kuma mata gargadi inhar ta yadda Tab din ya dauke mata hankali ta daina kokari a school kwacewa zatayi to tace ta karba tana dariya,

ummy ne tace ni na mantama ban tambayeki ba wannan kwalliyan kuma habibty ina zakije haka murmushi
La la ummy nah yanzu harkin manta yau ranar kaka ce dariya ummy tayi tare da cewa to yar gidan kaka saikiyi sauri ki tashi ki tafi ai dan la'asar zatayi kuma kinsan abbanki bayaso kina kaiwa magrip a waje da sauri ta miki tare dayiwa ummy sallama

Dakinta tashiga ta dauko hijab mai hanu red ta saka ba karamin karbanta yayi ba sanda taje dakin anty amarya tayi mata sallama akan zataje gidan kaka sanna ta kama hanya.

gidansu Naseer ta fara nufa a kofar gida ta sameshi kaman daman tasan jiranta yakeyi, yana hangota ya fara dariya da gudu ta karisa inda yake naseer ne yace haba lil sis ki daina gudun nan dan Allah bakiga yanzu kin girma bane gashi kinci kwalliya kaman wata cele Queen murmushi tayi tare da cewa

   "Are You serious nayi kyau bro
  Am very serious u look extra-ordinary dear murmushi sannan tace
Thank You so much dama abunda yasa nayi gudun ina sauri ne na nuna maka Tab din da abba ya sayamin wow ya fada tare da karban tablet din a hannunta,

Suna tafiya yana dannan tablet din Nasreen ne tace gsky bro am tired mu shiga napep ga kudi ummy ta bani kuma munata treaking

Haba lil sis wlh kin cika son jiki gidan kaka kuma wani napep zamu shiga abunda babu nisa ma munkusa isa fah ya fada yana mata dariya

Tumburo baki tayi tana cewa Allah nikam da nisa saidai in zaka goyeni harmu isa tuntsurewa da dariya naseer yayi
''Haba lil sis so kike duk inda muka wuce ana kallon mu bakyajin kunya ki hadu da friend's dinki su ganki big dake an goyeki itama kyalkyalewa da dariyan tana fadin to ai duk friend's dina yayansu suna goyansu kaga nima inka goyen kosun ganni bazasu mun dariya bah

To shikenam ki bari saimun dawo saina goyeki ba yanzu ba yanzu kiyi sauri ai munkusa isa sauda kadan.

   "Haka sukaci gaba da tadi har suka isa.

Kaka zaune take a tsakar gida tanashan iska da gudu nasreen ta kariso inda kaka take jikinta ta fada tana haki, kaka ne tace kekam dai bansan yaushe zaki girma ba wlh so kike kidan karisa kafar tawa mai ciwon koh kelkyalewa da dariya nasreen tayi sannan tace haba ke yar tsohuwan nan wlh kin cika mita na gaji ne shiyasa nakeson sauke gajiyana akanki

Allah ya shiryaki kaka ta fada tana dariya shidai naseer tsaye yake yana kallon ikon Allah

Juyawa kaka tayi dan taju kaman motsin mutum a kusa da ita ganin naseer da tayi ne yasa tayi saurin cewa ha,a dana tare kuka taho ne yau kuma, dariya yayi tare da cewa eyii wlh kaka ai naga keda yar jikartakin sai rikici kukeyi shiyasa na tsaya kallon ikon Allah

  _Mikewa kaka tayi tana fadin ni bani waje na kawowa bakona ruwa tashi nasreen tayi tana tumbura baki ciki ta shiga Nasir ya bita a baya waje a falo suka zauna
    "Waje nasreen ta samu itama ta zauna ta kurawa tv ido dan film din da takeso akeyi a _mbc bollywood_ Kabhi alvida nah kehna.
     "kaka ne tace ke dallah ki tashi ki kawowa bako ruwa kinxo kinsa tv a gaba kina kallon
dariyan shakiyanci Nasreen ta farayi tana fadin yanzu kaka Yaya naseer dinne bako shima dariyan yakeyi ganin yanda take maganan in a funny way.

Ganin yanda nasreen take zaune batada niyyan tashi yasa kaka ta mike ta bude fridge ta dauko malt guda 2. ta ajiyewa Naseer godiya yayiwa kaka sannan ya dauki guda daya ya bude
  Aiko nasreen na ganin kaka ta dauko malt yasa tayi saurin durkowa daga kan kujera ta dauki dayan da Nasir ya bari kaka ne tace eyeee shakiyiya wato kinason sha kikaki tashi ki dauko koh

ah to dama bazansha ba, ai keya kamata ki kawo manah ba gunki mukazo ba dariya kaka tayi ta tashi tabarsu a wajen dan tasan nasreen da baki yanxu zata kureta......

_Husnah mb ce_ ✍🏻

ZABIN ALLAHWhere stories live. Discover now