ZABIN ALLAH

380 20 0
                                    

💦💦 *ZABIN ALLAH*💦💦
              ~nake nema~

*True life story*

*💦Talented writers forum*💦

          *{T.W.F}*
    
    
*Written by husnah mb*

*🙏🏻Dedicated to Teemah jalo*🙏🏻
   Thanks for ur support All the tym...


*2⃣5⃣-2⃣6⃣*

http://husnahmb.blogspot.com

_Washe gari_

Nasreen ce zaune a parlon ummy tana kallo yanzu ba karamun girman nasreen tayi ba dan duk kirorin budurci sun sauka mata dan inka ganta indai bawai an fada mata yar 15yrs bace to zata zata takai 18 dan yanda kirjinta ya cika ga wani hips mai daukan hankali"

Sallaman yaya Naseer ta jiyo da sauri tayi yunkurin tashin jin da tayi maranta ya murda yasa tayi saurin dawowa ta zauna tana kallon kofar falo.''

Sallaman naseer yayita dokawa amma babu wanda ya amsa da dukkan alamu babu kowa a kusa ne shiyasa' direct kofan dakin ummy ya nufa sallama yayi nasreen ne ta amsa masa fuskanta dauke da fara'a sakai yayi ya shiga kujeran da yake kallon kusa da wanda take zaune ya zauna yana murmushi " Nasreen ne tace bro ina kwana' lfy qlau lil sis yaya jiki wani kunyane taji yazo ya rufeta duk da kuwa tasan naseer baisan me yake damunta ba' da sauki ta amsa masa dashi kanta a sunkuye murmushi naseer yayi tare da cewa lil sis jiya nazo after magrip ai ummy tacemun kina bacci wai bakyajin dadi' eh wlh bro banajin dadi ne shiyasa" salon da nasreen tayi amfani dashi wajen magana ne yayi matukar burge naseer,

"Ganin da nasreen tayi Bollywood sun gama film din da take kallo ne yasa ta mike danta dauko remote ta canza Chanel din" yanda take tafiya ko ina ajikinta yana girgiza ne yasa naseer ya shagala da kallonta dan salon da take amfani dashi wajen tafiya ba karamun burgeshi yayi ba hakan yasa ya tsinci kansa cikin farinciki' remote din ta dauko ta canza chanel din zuwa arewa24'

Ganin da tayi duk motsin da tayi naseer yana kallonta ne yasa tajita duk a tsarge" kokarin kallon jikinta tayi don taga meyene baiyi ba ganin da tayi hannun riganta yanata sumbulewa wanda kuma hakan ya bayyana suran kirjinta a waje" yasa tayi saurin gyarawa.

  "Ya naseer! Ya naseer!! Ta kira sunanshi ganin da tayi hankalinshi baya jikinsa ne yasa ta matso kusa dashi hannunsa ta rike tana fadin lafiya kuwa bro? Tunanin me kakeyi haka' sai yanzu hankalinshi ya dawo jikinsa firgit ya firgita" Tambayan da nasreen ta jera masa ne yasa yayi murmushi tare da cewa  "lfy qlau lil sis meye kika gani shiru tayi kusan na 2 minutes sannan tace naga ai bro kana tunani ne shys, babu tunanin da nakeyi lil sis kawai banjiki bane ya amsa mata dashi'

A'a bro fadamun gsky tunanin meye kakeyi haka 2 times fah ina maka magana amma bakaji ba murmushi naseer yayi yace kinaso kiji tunanin meye nakeyi ne daga masa kai tayi alaman eh" Shirun daya ratsa parlon ne na yan mintuwa yasa nasreen tace bro tunanin meye kakeyi'

Wani murmushin ya karayi sannan yace ina tunanin _Lil sis dina ne_ dariya nasreen ta kelkyale dashi tare da cewa kaidai bro fadi gsky kodai kana tunanin anty nane' nan take ya tsume tamkar bai taba dariya ba sannan yace ai lil sis ke bakida wata anty kece anty kanki' murmushi tayi kawai ta kauda maganan dan dama bata fahimci me yake nufi bah
     "Hira sukasha sosai sai kusan 12 O'clock tukun naseer ya tafi gida.

Around 4:00pm affan ne ya shigo dakin ummy yana kiran nasreen ummy ne tace tana dakin anty Amarya suna kallo juyawa yayi da sauri ya nufi dakin anty amarya

  _"Affan ne ya shigo palon da sallama yace liltle sis amsawa tayi da na'am bro' hankalinta nakan T.v murmushi affan yayi ganin yanda gabaki daya nasreen ta bada hankalinta akan kallo' yace yau kuma bazama a juyo a kalle niba murmushi nasreen tayi tace bro banson film din nan ya wuceni ne shys kuma sun kusa gamawa tana maganan but still hankalinta nakan tv.
   "Affan ne yace tunda bazaki juyo ki kallen ba barin koma da abuna aiko da sauri nasreen ta juyo tana karewa ledan da ta gani a hannunshi kallo
da sauri ta taso ta nufo inda yake tana fadin bro mena samu haka murmushi yayi sannsn yace a,a ba bakiso ba inata miki magana kin shareni dan haka jeki zauna kiyi kallonki barin tafi nima da abuna"

Langwabe fuska tayi kaman zatayi kuka tace haba bro kayi hakuri murmushi yayi tare da mika mata ledan da yake hannunsa" da sauri ta karba tare da zazzage ledan akan kujera kwalin iphone ne ta fado da sauri ta dauka tana washe baki' budewa tahau yi iphone 6+ ne pink da sauri tace bro wannan kuma na waye haka murmushi affan yayi sannan yace nakine little sis sayo miki nayi" da sauri ta ajiye wayan taje ta rungumeshi tana fadin"

_Thank You so much bro i really appreciate❤ am so thankfull for having some1 like You as a bro, am so greatful that ur part of my life,❤ur such a darling, loving and caring bro❤Ur one in the sweetest person in the world❤_

Runguman da nasreen tayiwa affan ne yasa ya tsinci kansa cikin wani bakon yanayi hakan yasa yayi saurin raba jikinta da nashi' tare da cewa _Never mind sis deserved more_" murmushi tayi shima murmushin ya mayar mata dashi sannan yace akwai sim card aciki kuma na riga nayi plugging dinta charger kawai amfani zaki fara da ita" saura kuma ki bawa samari number ki duk randa na gani sai nayi seizing din wayar zanyi murmushi tayi tace babu wanda xan bawa number mah bro karka damu shima murmushin yayi ya karbi wayan ya fara mata setting's _WhatsApp, instagram da snapchart_ ya bude mata" mika mata wayan yayi tafiyarsa" cikin zumudi ta dauki wayan dakin Anty amarya taje ta fara nuna mata sannan ta nufi dakin ummy"

Kwance ta sameta saman gado tana waya da Anty fareeda saida ta jira suka gama wayan sanan tayi sauri hawa gadon tana fadin ummy nah kiga wayan da yaya affan ya sayomun murmushi ummy tayi tasa hannu ta karbi wayan jujjuyawa tayi tace habibty yaya affan kenam nayi miki murna lafiya ta kashe' karba tayi ta nufi dakinta"

Tablet dinta da tayi plugging a jikin charger ta dauko number naela dana ashfat ta kwafa saida ta fara kiran ashfat ta shaida mata yaya affan ya saya mata waya sannan ta kira neal mah haka dukkansu kawayen natan murna sukayi mata sosai abunda ya bawa nasreen mamaki shine taga sun dade suna surutu dasu ashfat amma kuma har yanxu kudin cikin bai kare bah"
  Account balance ta duba sai kuma taga har yanxu akwai sauran 2 thousand's 5 hundreed aciki"
Number yaya abdul ta dauka dialing tayi cikin sa,a ring daya yayi picking

Nasreen ne tace _" Hlo

Abdul ne ya amsa da "lil sis ykk gida ya kowa da kowa

dariya nasreen tayi sannan tace_" lafiya qlau bro ya school
  "School alhamdullh lil sis ina yaya affan yana nan ta fada tana dariya

"Abdul ne yace sis yadai yau najiki kinata dariya kaman wanda aka miki kyautan aljanna"

Murmushi tayi sannan tace bro bakaga na kiraka da new line bane" yaya affan ne ya sayamun sabuwar waya iphone 6+"

Wow sis am happy for You abdul ya fada yana dariya _Thank bro_ nasreen ta amsa masa

Surutu sukayi kadan daga nan suka katse layin.

Wayanta ta dauko number yaya affan ta kwafa tana dialing sai taga sunanshi ya bayyana akan wayan sunan dataga an rubuta ne yayi matukar bata mamaki" cikin sautin suprise tace...

_Husnerth mb ce_✍🏻

ZABIN ALLAHWhere stories live. Discover now