page 1

8.6K 378 16
                                    

*HASKE WRITER'S ASSO.*(Home of expert and perfect writers)

*BABU WAIWAYE*

BILLY GALADANCHI

Sadaukarwa ga K'awata
*HAFSAT ELHAM*

*Wannan shafin kuma nakine Zainab s Abdul,keta dabance tawan*
01

Duk yawan hada hadar da yaran makarantar keyi da murnar dasuke deeya kallonsu kawai takeyi ita sam batasan wani abu waishi farin ciki ba,kallan kowa take yanda yake yawo acikin family dinshi dasuka zo masa murnar kammala karatunsa na secondry amma ita ko kurege be zo mata ba,towama take dashi wa kuma ta ajiye a rayuwarta dazezo mata? Meye ma abun farin ciki a wannan kammala karatun nata, qara d'ago kanta tayi ta kalli harabar makarantar ta Dambo intl school, bata ga mutum daya tak dayake ba cikin family din shi ba se ita kadai, wani yaro ta hango ya rugo da gudu ya rungume qanwarshi da mamarshi,maman ta qanqameshi sosai yace "I miss u mom" murmushi ta sakar masa tace "Miss you more my son" d'auke kanta tayi daga dubansu tanajin wani zafi a qasan zuciyar ta,a yau dai ta karanci me ake cewa hasada lallai koda ake cewa hasada batada kyau yau kam tana hasadar daukacin yaran da iyayensu suka zo musu, wayanta ne yayi ringing ta d'aga ganin dad dinta ne muryanta na rawa tace

"Dad am all alone" tausayinta yaji ya kamashi sosai yace "Deeyah gani a school naku ban ganki bane ai" hannu ta sanya ta share kwallan daya silalo mata sannan tace "Ina field ne ai kowama yana nan da vendor nasu daya daya" katse wayan yayi kawai ya kamo hanyan wurin......

Bayan an gama yamma tayi sosai lokacin ma dad ya dad'e da wucewan shi office akan ze turo tahir ya dauketa idan an gama, wasu yan mata suka zo mata dayake class d'insu daya dayar ta kalleta tace

"Deeyah duk wannan shagalin damuke ke banda ke,kinacan gefe ke kadai kina ganin kinfi qarfin kowa har yau ma da bamuda tabbacin qara ganin juna sekin nuna halin ko in kula da kowa?" Murmushi kawai ta mata wanda ya qara kular da ita, dayar tace

"Rabu da ita danla humaira, gani take tamkar wai tafi kowa,banza kawai" nanma murmushi kawai ta musu sanin halinta akan bawai qala zatace dasu ba ya sanya suka wuce suna mitar tsabar wulaknaci da rainin hankali irin na sadeeya, gaba daya wannan yarinyar ta gama rainawa kanta hankali,ko kaine musailamu sarkin qarya bazakace wai kaji bakin deeya tana magana ba,wasu lokutan ma idan ka isheta har kuka take saka maka, koda zaginta kayi kuwa iya kacinta murmushi,mutane d'aid'ai kune take magana dasu acikin school ma d'inma da Hafsat kawai take magana,shima din bawai hira ba kuma akayi dace hafsat dinma bawai yawan surutu ne da ita sosai ba, koda tahir yazo ba wanda tawa sallamar bankwana se hafsat, anan zamu iya cewa ita hafsat din har kuka sukayi sanda zasu rabu kasancewar ita hafsat yar skt ce,karatu ne kawai ya kawota kd.

Zaune take a parlor din gidansu bata uhm uhm uhm,ita dai shiru kawai baiwar Allah ba yawan magana atare da ita sam,dady ne ya shigo da sallamarsa lokacin ya dawo da office,amsa sallamar kawai tayi sam babu walwala a tattare da ita,ta miqe ta gaidashi sannan ta karbi jakar hannunsa zuwa sashen sa a parlor ta dawo ta sameshi yana cin abinci kan dining taje tq zauna kusa dashi amma batayi magana ba kallonta sosai yayi

"Deeyah yaya dai?" marairaice fuskarta tayi,lokaci daya idanta ya cicciko da k'walla ta kalleshi da fuskar tausayi tace dashi cikin murya me ban tausayi

"Daddy bakaga ba wurin candy namu kowa family dinshi sunazo anata murna,momyn kowa yazo amma ni banda tawa,dan Allah daddy ka kaini gun momy na,idan ma ta rasu ne ka nunamun hotonta idan bakadashi kabani labarin ta kuma ka kaini gun danginta in gansu, kaima kuma ka nunani agun naka dangin" sauke chokalin hannunshi a kan plate dayake cin abincin dashi sannan yace

"Amma Deeyah menene kika nema kika rasa arayuwa ne wai? Wane kalan gata ne bana baki,iyayen kowa sunje candy kema ba naki iyayen sunje ba? Koni ba iyayen ki bane? Nine mamanki nine babanki kuma nine dangin ki" zuwa yanzu kam Deeyah ta soma kasa haqura da kukan daya zo mata, cikin kukan tace

BABU WAIWAYEWhere stories live. Discover now