page 9

2.4K 182 0
                                    

*HASKE WRITER'S ASSO.*(Home of expert and perfect writers)

*BABU WAIWAYE*

BILLY GALADANCHI

Sadaukarwa ga K'awata
  *HAFSAT ELHAM*

                          09
Me aikinsu gidansu tayi tafiya, wannan ya sanya gaba daya ayyukan gidan suka dawo kan deeyah dukda yake humaina takan tayata, gashi sam bata san ganin Bg musamman kallon dayake mata tun faruwar abun, sannan tarasa dalilin daya sanya sam wani tsanarta take hangowa acikin idanshi duk sanda ya kalleta, Ga uban tambayoyi,yaudai mopping take yi ita kadai a parlor ya zo ya sameta ya qura mata ido bayan ya had'e girarsa ta sama data qasa yace

"Har yanzu zuciyata ta kasa nutsuwa dake Deeyah, na gagara yarda cewar ba wani mugun abun kike shiryawa family na ba, meya kawoki london? Tayaya akai kikazo nan? Mesa ma duk fadin garinnan baki zauna gidan kowa aiki ba senan, inada tabbacin batun yauba kike bibiyar gidanmu, idan ma wani mugun abun aka turoki ki mana ko maqiyan daddyn mu sukayi hayar ki to wlhy ki kama kanki ki ruga a tukunya me tafasa, sabida bazan taba baki qafaba" d'ago jajayen rinannun idanta tayi ta kalleshi ido cikin ido sannan batare datayi magana ba ta juya zata shige kitchen dake cikin parlor d'in, hannun shi ya sanya ya janyo ta da qarfi ta fad'i a qasa gabanshi yace cikin tsananin qara da fad'a bayan ya wanketa da mari

"Ke har kin isa ina miki magana ki wuceni batare dakin kula ni ba,yau wlhy ko uban wa ya miki tsaye sekin sanar dani dalilin  zuwanki london da yanda akayi kike makaranta me tsada dama mafarin fara aikatau a nan gidan" Miqewa tayi cikeda fusata itama yaukam ya kure ta ya kuma kaita bango sannan,yaune tayi danasanin sauya tunaninta da tayi akan barin gidan tun watanni biyu da suka wuce, adaidai lokacin da ilalahirin jama'ar gidan suka dannowa parlor din kai ta sanya iyakacin karfin ta ta daki qirjinshi seda yayi baya tamkar zesha qasa,ta furta cikin qaraji,su kuwa ganin wannan abin sukayi cirko cirko suna kallon ta

" Ka matsa akan san sanin mafakata,tarihin rayuwata da kuma dalilin zuwana london,to yau zan sanar dakai, kai azatanka kai kad'ai ne aka haifa a cikin gata kowa ma a wahale ya taso to bari kaji, Sunan Mahaifina Musa Muhammad Dange, sananne sosai a kaduna kuma me kudin gaske, da kanshi ya biyamun kudi nazo london nice na gujeshi da kaina,badan ya gazawa lalurata ko daya ba,sedan kawai ya gagara nunani a wurin dangina na uwa dana uba,ko mahaifiyata ban saniba bare hotonta koma wannan dayafi komai sauqi shine sunanta, gidan danake rayuwa aciki wlhy ko a shekarun baya dana baroshi yafi wannan gidan komai, ina me shawartarka daka yi nesa nesa da rayuwata kakuma guji b'acin raina wlhy, neman tabbatar wa kai koni din wacece bazaka burgeni ba sekaje unguwar rimi a kaduna ka binci ki wacece wanene musa muhammad dange kai baseka sha wahala bama a garin kawai kowa ya sanshi, sabida shidin me haline gaba da baya ka gane kamko?" shiru yayi yana kallonta seda suka jiyo ana sa lallami a bayansu Aunty maryam ta suma, sukayi can dukansu asibiti aka kaita aka bincika bugawar zuciyane sedai bame rauni ba, na wani abune daya bata mamaki,kuma tabbas ko Aunty madina da Aunty zee sunji faduwar gaba dajin an ambaci sunan Musa muhammad Dange, tsohon mijin Maryama wanda shine maosyinta tun asali, koda ta farko kuka ta saka tasanya a kira mata Deyyah kallon deeya  tayi tace

"Sadeeyah yaushe ne date of birth dinki?" kallon mamaki ta mata sannan tace

" 1st january 1999" Da sauri ta zabura zaune tace "Naji kince wai sunan mahaifinki Musa muhammad Dange ko?" gyad'a mata kai kurun tayi cikeda qosawa da tambayoyin dama kuma bamesan yawan tambaya ko magana bace diyya, maryama ta sake cewa "Ya tab'a gaya miki cewar yayi zama a nan london?" kallonta deeyah tayi tace cikin kuka

"Mutumin dabe tab'a had'ani da familyn shi ko na mahaifiyata ba,ko kuma ya gayamun koda sunan mamana idan ta mutu ne,ko ya nuna mun hoton ta tayaya ze sanar mun tarihin rayuwarsa? Ni bansan komai ba game dashi, kullim idan na nemi sanin danginsa seya ce dani babu waiwaye a lamuranshi kalmar kenan ko wane lokdaci, sannan kuma bayaga gayamun dayayi an haifeni a ranar Juma'a a asinbitin Marwa clinic bansan komai ba game da kaina ko game dashi ko danginshi kona mahaifiyata,rayuwa tamun qunci shi kadai nake nake dashi shine shi kuma ze dakkoni ya kawoni karatu bangon duniya haba mana ina zan iya wannan rayuwar" tashi tsaye maryama tayi tana kuka

"Itace wlhy Madeena 'yatace Haleematu, nice na haifeta da cikina" ta rungume Aunty madeena tana kuka,madeena cikin mamaki tace "Hankalinki d'aya kuwa dagaji d'an sakkwato nada 'ya sekice takice ke yaushe ma kika tab'a haihuwa?" kallonta itama Maryama tayi cikin kuka tace

"Inajin kunyarki madeena,inajin kunyar iyayen mu inajin kunyar Musa,ina jin kunyar Haleematu ina jin kunyar Allah fiye da komai da kowa,ina tsoron Allah na sani lallai haqqin mijina da 'ya tane yake bibyata har yanzu, wlhy madeena akwai b'oyayyen al'amari daya faru tsakanina da Musa,nice na hanaku saurarenku sabida karkuji kumun fada amma wlhy sharri nawa musa abinda nace yanayi dinnan na fashi da makami, na kuma tsoratar daku akan cewar yace ya sakeni idan na fada kowani yace agidanmu na sanr masa seya kashemu duka, tunfarko kinsan iyayen musa basan auren nan namu suke ba,kamar yanda kuma bakwasan aurena dashi kunfi sona da Haruna, Tun kafin muyi aure dashi mukai yarjejeniya akan bazan haihu ba se munyi shekaru takwas zuwa goma da aure,kunsan Alllah ba'a masa ganganci katsam segani da juna biyu kuma bamu san dashiba seda yayi wata uku,hankalin mu ya tashi sabida nida musa bamasan nayi loosing shape nawa, mukaje asibiti akan a ciremun aka tabbatar mana cewar mahaifata tana da rauni idan aka cire zan iya rasa raina gaba daya,wannan ya tsoratar damu muka fasa akan idan na haihu bazan shayar da 'yarba sabida kar nonuwana su zube,cikin ikon Allah na haifi 'yata  mace sak me kama dani, Tunda aka haifeta Musa yace lallai sunan mahaifiyar sa ze saka Haleematu sadeeyah, abin mamaki kuma se kawai Sadeeyah taqi karbar madara wannan abin ya tashi hankalin musa sosai ya soma magiya akan na baiwa Haleema nono amma qememe naqi, Musa har kuka yamun naqi kai daga bisani ma nace seya sakeni, kuka kam ya shashi ya nuna mun akan san da yakemun ya baro iyayenshi da tushensa yazo gareni ninkadai, yamun alqawarin baze taba bari naba amma na shayar da Mamanshi, haka na dage naqi, dole ya sakeni naje ban gayawa kowa na haihu ba agida namuku karyan wulaqanci yake mun harda duka nace dan kawai nakama shi da makamai yana magana da yara akan suna fashi da makami, dole kowa ya qyaleshi zuwanshi na qarshe kuwa ya sanar mun lallai banda waiwaye ya sanar mun hakan yafi sau goma sannan ya tafi, abinda yafi bani tsoro da halayena ban ji komai game da rashin Haleema ba hasalima ban wani dauketa wata aba ba,seda na rasa haihuwa,kullum ina san na nemeta amma ba halin yin hakan tunda babu wanda agidanmu yasan da zancen haihuwarta seni kadai" tana kaiwa nan ta kwanta a qasa tana kuka me ban tausayi,Deeyah kasa gaskata zancen ta tayi lokaci daya taji tama tsani uwar tata,akan wani banzan shape na jiki taqi ta shayar da ita,ta gwammaci ma a saketa kenan? Lallai ma bazata taba kallon ta matsayin uwaba, da gudu ttabar asibitin zuwa gidan ta soma shirya kayanta sabida barin gidan,ta gudirta a ranta zata guji mahaifiyarta yanda itama ta gujeta a sanda take tsananin buqatarta......

Mom Nu'aiym

BABU WAIWAYEWhere stories live. Discover now