*HASKE WRITER'S ASSO.*(Home of expert and perfect writers)
*BABU WAIWAYE*
BILLY GALADANCHI
Sadaukarwa ga K'awata
*HAFSAT ELHAM*03
Deeyah yanzu kusan 2 months da zuwanta beilin, ta kuma samu nutsuwa sosai,bata wasa da karatunta sedai kawai abinda bata fahimta ba shine yawan kashe ba nata bane kud'i komai yawansu indai babu imcome kullum fita suke toko lallai dole ne sesun ja baya,ganin kud'ad'en hannunta nada yawa ya sanya taketa rizgar su ba qaqqautawa, gata da yawan san suturu na gayu da kuma cin qwalam, amma dai tana cikin damuwar yanayi na rashin gata aganinta duk yawan dukiyar dake hannunka bazaka moreshi ba indai ya kasance rayuwarka kana yintane kai kadai, ko a can batada qawa ko daya se wata mata dake ai a makarantar su dasuke matuqar shiri da ita kuma ta kasance yar Niger a jihar maiduguri, sunanta malama zainab,wannan kenann.*Nigeria*
*Tun bayan da Deeyah ta tafi da kwana biyu hankalin daddy ya matuqar tashi,ganin ita bata kirashi ba kuma wayanta baya tafiya,hankalin shi ya dan kwanta ne da tunanin kota sauya layine yazo masa,wannan ya sanya ya dan huta akan seta kirashi haka aka share wata ba labarin Deeyah da haka ya kuma tunanin cewan lallai tayi hakanne sabida kawai ta mayarda hankalinta sosai da karatunta ta kuma dauki magarshi ta dogaro dakai, da wannan mahaukacin tunanin kuma ya sake kwantar da hankalinshi.......Yau shekarar Deeyah biyu da watanni hudu a Beilin, har wannan lokacin batada kowa,kuma a wannan lokacinne aka turasu London domun qarasa course nasu na phermacy,kasancewar wanna qa'idane a tsarin karatunsu, Daddy tun karshen zango na karshen shekarar ta ta farko yazo mata hutu ga mamakin shi sam babu record nata a school din,abin ma dayaji shine sam batama yi registration ba a school din,ya zaga duka schools dake birnin london babu record nata,har airport yaje akan record na saukan jirgin nasu aka tabbatar masa sun sauka a wannan date din,kuka kam ya shashi se a sannan yake ganin matukar wawtarshi na barinta tabar qasa ita kadai yakuma qi mata magana me dadi, bank nasu yaje inda yasan ya sanya an buda mata acc,namaki yasha jin wai saukar ta garin batafi kwana biyu ba tayiwa acc din qanqat, tunda ya dawo Nigeria ko sam bashida kwanciyar hankali haka ya kwanta ciwo babu me jinyar shi......
Tunda Deeyah ta dawo london kama hayar gidan zama ya soma gagararta ga shi batada kudi da yawa hannunta sannan kuma registration ma ya mata tsada ga abinda ta fahimta london garine na kashin kudi komai na masu haline,haka dai ta kama hayar shekara daya a wani gidan ta soma sabuwar rayuwa,batafi watanni biyu ba kud'ad'en hannunta suka qare kaf, abincin ci ma gagararta yake duk ta soma sauyawa, ranar wata monday da yamma ta fito shan iska zuciyarta fal damuwa ga rashin abinci ga rashin na transport zuwa school ta hadu da Aunty Zainab, rungume juna sukayi sosai suna murna ta kalli Deeyah tace cikeda mamaki
"Gayu gayu yanaga kin rame haka ne wai?" idanta ne ya cicciko tamkar zata saka kuka, hannunta Aunty zainab taja zuwa wasu kujeru dake a wurin, suka zauna sannan tace
"Gayun Aunty zee lafiya dai?" Sadda kanta tayi qasa sannan tace
"T zee wlhy ina cikin damuwa, ki taimakamun da aiki ko wane irine wlhy zanyi indai zan samu kudin cin abinci da registration na school,kudin hannuna ya qare kuma banida mafita?" kallon mamaki zainab ta mata
"Ki kira babanki mana ki sanar masa kekam wane irin aiki zakiyi kina zuwa school" dagowa tayi ta kalleta cikin idon
"Auntu zainab ina rokonki karkice xaki binciki rayuwata karkice zakimun tambaya gameda family na,nidai taimako daya nake nema awurinki shine ki nemamun aiki koda na gyaran gidanae da girki,tunda lectures nawa 3 times in a week,kuma 2 hour only i can manage,tunda muke baki taba ji nace dake wai inasan taimako ba wannan ma kamawa tayi dan Allah ki taimakamun" dafa kafad'arta tayi tace
"Deeyah kinfin karfin aikatau wlhy, bawai banida me neman aikin bane ma yanzu haka Auntyna madina datayi sanadiyan zuwana wannan country din tana neman house help amma shiru, zan iya kaiki can gashi sam banisa da school naku amma anya zaki iya rayuwa acan kuwa deeyah? Kefa yar gatace gaba da baya meze hadaki da aikatau?"
"T zee aini nace zan iya indai akwai albashi me tsoka" cikin tausayawa zainab ta girgiza kanta,ta dade tanajin tausayin deeyah tunba yauba takula yarinyar tana rayuwar takura ita daya......"
Aunty Madeena ta buqaci deeyah ta dawo gidanta da zama amma duk se suke mamakin yanda take wannan makarantar me tsada kuma tace wai tana aikatau,da kamar wuya kam wai gurguwa da auren nesa.....
*Bayan kwaba biyar*
Mopping deeya keyi cikeda jin zafin zuciyarta sosai take missing daddynta har yau number wayanshi na zuciyarta zaune rad'am amma ba yanzu ta shirya kiransa ba,seta kammaka karatunta sannan zata masa waya ta sanar dashi cewar ta cika burinshi amma bazata dawo gareshi ba, batasan sanda kwallah ya zubo mata ba ta share su,ta gabanta taji ance
"Ke" da k'arfi d'agowa tayi ta kalli shi bata tab'a ganinshi ba tun zuwanta gidan kallo dayan datamai kuwa taji ta tsaneshi mesa ma ze mata wannan kiran sekace wata tabba? Tana tsakiyar eannan tunanin taji yace
"Wacece ke?" kawar da kanta tayi gefe sannan tace "Me aikin gidan ce" tsaki yaja ya bita da kallo sannan yace bayan ya gama qare mata kallo
"Se in rasa meke damun yan Niger wlhy, kina kyawunki ki tsaya kiyi aure kinzo london karuwanci" bata d'ago ba dukda kalamanshi sun daki zuciyarta yace da ita, kan wani yayi magana cikinsu Humaina tazo da gudunta ta rungu meshi
"Yaa BG oyoyoooo, nayi missing naka sosai wlhy" kallonta yayi yace "Haba dai humaina nima sosai nayi missing naki,momy fa?"
"Tana gun aiki,ni kadaice a gidan se Aunty Deeyah" juyowa yayi ya kalli deeyah dake tsaye tamkar an dasata yace
"Momy wai bazata dena ebo karuwai da b'arayi a matsayin yan aiki ba? Bazata dadara ba sam ko?" kwab'e fuska humaina tayi
"kai yaa BG Aunty deeyah sam ba haka take ba wlhy" dage kafadunshi yayi ya shige ciki batare dayayi magana ba"
Mom Nuaiym ce
Kuyi hakuri ina busy
YOU ARE READING
BABU WAIWAYE
General FictionBugun zuciyar tane ya qaru, ganin shigowar Al'ameen gidan, ktchen take qoqarin shigewa sanda ya qaraso gabanta ya murtuqe fuska hade da ce bayan ya qura mata manyan idansa "Ina sanin meye asalinki? Wacece ke? Wannan aikin dakike beyi kamada jikinki...