*HASKE WRITER'S ASSO.*(Home of expert and perfect writers)
*BABU WAIWAYE*
BILLY GALADANCHI
Sadaukarwa ga K'awata
*HAFSAT ELHAM*15
A k'ofar wani gida sukai parking datake saka ran lallai nan ne gidan dasukazo itada musa alokacin dayake muradin aurenta kasancewar gidan ko a wannan lokacin gidane na masu hannu da shuni da suke da sarautar ta Dange a hannu bawai gidan talaka ba, gidan kam ya canja ba kad'an ba,qirjinta ne ya doka a lokacin data hango wannan tsohon dabazata tab'a manta kalamanshi akan taba, dukda ya qara tsufa sosai amma hakan be hanata ganeshi ba, tunawa tayi da kalamansa lokacin tana shirin auren d'ansa kamar haka
"Yarinya nifa nayiwa yarona mata tunkan ya dawo Nigeria, kuma bazan sauya ba akan zuwanki, babu alamu akan cewar ma kekam daga babban gida kika fito, sabida idan da daga babban gida kika fito bazaki tab'a biyo namiji har gidansu ba batare da aurensa akanki ba, kuma kai Musa wlhy sallama ka zanyi indai ka dage akan seka auri wannan feqaqqiyar" qirjinta ne ya wani doka lokacin data sake kallon fuskar tsohon qara tunowar datayi sanda yace cikin fusata
"Aina sanar dakai na sallama wa duniyar kai indai ka auri wannan matar,kuma tunda ka kafe ka kuma auretan sekaje can kaida ita, bazan maka baki ba bazan kuma bika da mummunar adu'a ba,abu d'aya zan sanar maka daga ranar daka shuri k'afa kabar gidannan lallai idan ka waiwa yomu bazan tab'a yafe makaba kadai zab'eta to har cikin raina ina maka fatan Alkhairi ubangiji ya taimaki rayuwarka ya sanya alkhairi da albarka acikinta,amma daga sanda ka tako qafarka da sunan ka dawo mana,tsinuwa zata hau kanka" hawayenta ta share tunawar datayi cewar qiri qiri Musa ya zab'eta sama da danginsa da kowa nasa ma yakuma tabbatar wa kanshi babu waiwaye acikin lamuran sa,baze tab'a waiwayar gidan suba,amma ta butulce masa tunkan suyi shekara d'aya tak da aure, tana tsakiyar wannan tunanin ta tsinkayi muryan Al-ameen yana cewa
"T marry ba nan kikace bane hala?" d'agowa tayi da sauri tace "Nannne kam,ku muje mana" sauka sukayi a motar sannan ta juyo tankalli deeyah Tace
"Sadeeyah nan sokoto mukazo ba maiduguri ba, a yanzu haka muna qofar gidansu mahaifinkine kuma wancen tsohon dakike hangowa riqe da alqur'ani me girma shine mahaifin daddyn ki,banaso muje ki nuna halin banza a wurin su wlhy, idan ba haka ba zan sassab'a miki kinji na gaya miki" Dukda tayi mamakin hakan amma ba qaramin dad'i tajiba kallo daya kuma ta ma dattijon ta hango tsananin kamannin dake tsakanin daddynta da shi, kan wani yayi magana acikinsu se jiniya sukaji motocine sunfi 30 manya manya suka doso su a harabar gidan sukayi parking, mutumin dataga ya fito ana rufa masa bayane ya sanya ta riqe hannun Deeyah tace da Bg "Babangida muje gaba kansu qaraso" Da sauri suka tattaka zuwa gaban tsohon dukkansu durqusawa sukayi suka gaidashi ya dubesu sannan ya qara qurawa maryama ido, janye madubin idanshi yayi yace da ita
"Bayin Allah daga ina ban gane ba?" kan wani yayi magana me girma gwamna ya qaraso,zubewa yayi agaban mahaifin nashi yana kwasar gaisuwa, seda suka natsa sannan ya kalli maryama yace
"wannan kamar maryam?" sadda kanta tayi qasa tace "Nice yaya khamees ya aiki ya kuma kwana biyu?" miqewa tsaye yayi ya kalli muqara banshi yace dasu "Kowa ya koma mota akwai abinda nakeso in gabatar anan" miqewa sukayi suna banba d'ancin 'yan siyasa........Tsohon ne ya kalli kameess yace "Kasan tane hameesu?" sadda kanshi yayi qasa sannan yace
"Baba matar Musa ce fa maryama" zabura tsaye yayi yace "Wane musa kake nufi kaddai Babana?" amaimakon ya baiwa dattijon ansa seya kalli ta yace
"Ina labarin d'an uwana na tabbatar yanda nayi suna a wurin siyasa dole indai yana raye zeji sunana amma sam be neme niba,ve kuma waiwayi gida ba,ina fatar tare kuke" gyaran zamanta tayi tace
"Babu yanda za'ayi mutum ya kira tsinuwsr iyaye da knshi,musa bema san munzo nan ba, dama nace ni barin zo da qoqon barana akan a yafe mana dagani harshi in kuma nunawa Sadeeyah dangin mahaifinta datake ta neman gani tuni,dan Allah na roqeku akan ku gafarta masa ku barshi yadawo yaji sanyi zamansa acikin yan uwansa wlhy yana cikin damuwa me tarin yawa" Cikeda zumud'i dattijon yace
"Wlhy ni tuni na gafartawa musa na kima lamunce masa ya ziyarci gida duk sanda yaso, ya dawo ayita zumunci nasha wahalar rashinsa mahaifiyarsa ma haka tafini damuwa akan rashin sa take kwance tana ciwo shekara da shekaru, shine bezo gida ba da tuni an wuce wurin sanar dani inda yake dan Allah naje da kaina" kuka dattijon ya saka inda atake aka soma gayawa dangi isowar matar musa da yarsa ta cikinsa mahaifiyar tasha kukan murna,ta kama Deeyah da runguma tanata suma, lokaci daya kwaya bayan sun kwana aka kwashi dangi masu tarin yawa zuwa kaduna ciki kuwa harda gwamnan jihar sokoto meci a wannan lokacin........
Mom Nu'aiym
CZYTASZ
BABU WAIWAYE
General FictionBugun zuciyar tane ya qaru, ganin shigowar Al'ameen gidan, ktchen take qoqarin shigewa sanda ya qaraso gabanta ya murtuqe fuska hade da ce bayan ya qura mata manyan idansa "Ina sanin meye asalinki? Wacece ke? Wannan aikin dakike beyi kamada jikinki...