page 14

2.4K 164 5
                                    

*HASKE WRITER'S ASSO.*(Home of expert and perfect writers)

*BABU WAIWAYE*

BILLY GALADANCHI

Sadaukarwa ga K'awata
  *HAFSAT ELHAM*

                            14
Kallonta mahaifin nata yayi yace

"Mamana ki sani bazan tab'a bari  maryama ta rab'eki ba dukkuwa da yake itace da kanta ta haifeki,sabida irin wulakantar dani dake da tayi a lokacin da muke tsananin buqatarta, amma ki sani uwa uwace komai lalacewar ta, bazan lamunci kici zarafin mahaifiyar kiba bakuma zan lamunci kici gaba da mata hakan ba, dukda yake yana cikin sharud'ana akanki akan karki zure mata, abu me muhimmanci danakeso ki sani shine akanki na dawo da maryama gidannan kina buqatar family atare dake,dangin mahaifiyarki basu miki komai ba,hasalima basuda labarin samuwarki sannan qazafin da tamunne yasanya basu nemeni ba, mahaifinta mutum ne me nagarta sabida haka ki rayu acikin aminci da su kina jina ko" Turo baki tayi sosai tace

"Ni wlhy daddy gidan zan bari indai tana nan,matar data gujemu yanzu me zata dawo ta mana?" kan ma ta sake cewa wani abu Yaa Bg ya wazga mata mari me zafin gaske cikeda fusata ya furta

"K'addara wacce bata wuce ranar ta itace ta rabaki da Anty Maryam ni nan a hannun ta na tashi kuma na shaida uwace ta gari,idan har ke bakya ganin girmanta da qimarta ki sani ni nan ina gani, kuma lallai bazan bar nan gidan ba sena saisaita miki nutsuwarki na kula sam bakida ita" murmushi daddy yayi sabida yaji dad'in ganin Babangida me hankali bece komaiba ya juya ciki maryama ta bishi, Deeyah ma cikin ta wuce zuwa part d'inta tanata faman kuka da qunquni, Bg zama yayi ya dafe kanshi aranshi yace

"From one problem to another".

    *Bayan kwana biyu*

Haka dai kwana biyu ta wuce Deeyah banda gaisuwa ba abinda yake had'a ta da Mamanta har yaa Bg ma dake mashi baya matsa zuwa cikin gidan kasancewar masaukinsa na bayan gidan, lissafi yakeyi ta yanda ze kwance ya kuma k'ulla,da kanshi yaje ya roqi daddy akan sunaso suje da Deeyah maiduguri taga dangi daddy be hanasu ba sam,se fatan Alkhairi daya musu yace shi yayan nasu ya sanar mata da kanshi......

     Sanye take da riga doguwa har qasa wacce ta d'ameta sosai, se wani siririn mayafi ga gashin kannan dukya firfito ta waje ata bayaan ma ya sauka har gadon bayanta dan kwalin kanta be rufe shiba, waqa take saurare da headphone a harabar gidan take zaune ta rufe idanta tana murmushi alamar lallai tanajin dad'in waqar datake saurare, qura mata ido yayi yana kallonta shi sam bayasan irin wannan shigar datakeyi ba kunya,yanaso tasan da zuwanshi amma bayaso ya tab'a jikinta hannu ya sanya ya zare mata d'aya daga cikin kunnenta, a hankali ta bud'e idanta ta saukesu a kanta cikeda kasala, ganin yaa Bg ya sanya ta zabura sarai ta sani ya hanata saka irin wayannan kayan yakuma ma haneta da zaman gaban gidan, b'ata fuska tayi tace dashi cikeda fad'uwar gaba

"Ba wuta fa kuma kaga ana zafi sosai, zafinne ya fiddani waje" qura mata ido kurun yayi se can kuma yace

"Ki shirya kayanki zamuje maiduguri gun danginmu, Sadeeyah saura kuma muje maid din kice zaki nuna musu halin naki na banza,sannan kuma banasan wannan kayan naki, jebi zamuje so ki soma shiri tun yau" Rausayar da kanta tayi, tunda ya wazga mata mari dama take shakkar sa,ta kalleshi tace

"Nifa yaa Bg duka kayana haka suke wlhy, ko wani atamfa bani da se qwaya uku kawai" kallon takaici ya mata,shi kanshi ya sani maryama bata kyautawa Deeyah ba, if ace bata mata hakan ba ba yanda za'ayi ma ta taso sekace ba 'yar hausawa ba, komai nata gashi nan dai kawai, gyaran murya yayi yace

"Jeki ki shirya yanzu zamuje wani wuri mu dawo" batayi musu ba kurun ta mike taje ta dawo sanye da doguwar rigar abaya baqa da mayafinta,tayi kyau ba laifi duk da yake ba wani makeup ta saka ba, beyi magana ba kurun yaja suka tafi, a k'ofar wani katafaren gida ya paka sannan ya d'aga wayarshi ya kara a kunne

"Girl friend ki fito muje ina waje" ajiye wayar yayi,ita kuwa Deeya ta tab'e baki aranta tace kanka akeji koma dai boyfriend ce" wata kyakyawar yarinya tafito daga cikin gidan sanye da atmafa ja da black,d'inkin riga da skirt,yarinyar ta had'u ba qarya, doguwar gaske ce me bak'ar fata amma me sheqi da sulb'i kallo d'aya zaka mata ka fahimci lallai akwai abu biyu a tattare da ita, na farko dai zaka fahimci tsantsar hutu a tattare da ita,na biyu kuma zaka tabbatar wa kanka yarinyar tana cikin gata, tana tinkaro motar ta soma washe  baki, a take qayataccen fararem haqwaranta suka bayyana, ta sauke musu manya manyan fararen idanuwan ta, Al-ameen dake waje dama ya fita seya soma tattaki suna had'uwa suka rungume juna tamkar a turai,kai kace ba 'ya'yan hausawa ba

"U look gorgeous ashe dama niger ze k'arb'i black skin d'innan haka" murmushi ta masa suka k'arasa mota kallon Deeyah yayi yace

"Ki koma baya Deeyah" wani takaici ne ya tarnak'e ta,amma sabida kada ta bayar da kanta ta miqe tsaye tace "Sannu sister ina wuni"

"Yauwa shine abinda kawai fareedah tace da ita ta kame a gidan kaban motar shima ya zaga ya zauna Deeyah ma ta shiga baya kallonshi tayi suka sakarwa juna murmushi sannan yace

"Reedah MU yadai kwana biyu" murmushin ta qarayi tace

"wacece wannan?" sosa kanshi yayi sannan yace "Qanwata ce sunanta Deeyah,ita nake sanar miki akanta,kuma ai na sanar miki inda zaki rakamu" wani  wal tayi da ido tace

"Are u kidding me boifriend, ya zakace batasan kayan hausa ba,ina tashin kd ne?" takaicine ya kama Deeyah shi kuwa yace

"MU zaki rakani shope dinne ko kuwa sekin baqan tamun rai?" murmushi kurun tamasa taja bakinta ta tsuke sabida sarai tasan halin sa yanzu se ya b'ata shirin dama tun barowarta london rabonta dashi ko waya basayi,hanyan kasuwan ta nuna masa suka je suka ebi atamfofi da laces da materials da mayafai masu d'an girma kala kala, bayan sun dawo mota ya sake duban Fareeda yace

"MU muje gun tailor kinnan dayake miki d'inki kina shanawa a london zewa qanwata ko guda 10 ne nanda kwanaki biyu zamuyi tafiya" Murmushi tayi kawai har wannan lokacin kuwa bakinta dana Deeyah ba qara had'uwa ba ita sam Deeyah setaji yarinyar batai mata ba,ta fiya iyayi da kaudin tsiya yayinda ita kuwa M-U ke ganin masoyinta kuma abokinta nasan wannan qanwar tasa kamar me yayinda ita ko oho bemasan tana haukan taba, tailor din ya kwashi kud'i aka aunata aka biyashi kuma ya tabbatar da yaranshi shope nashi ze rarrabawa yaran shi jibin by 10 za'a samu.

*Dange shuni local government, sokoto state NIGERIA*
   
    Tunda suka shigo wannan qauyen qirjin maryama ke dokawa,abubuwa da yawa suke dawo mata,qirjinta se dokawa yakeyi ba kad'an ba,shekaru ashirin da watanni bakwai kenan a lissafinta da barinta garin na mahaifin sadeeyah, wanda takeda yaqinin shi d'inma tun wannan lokacin be sake waiwayar garin ba, bazatace ba sauyi ba kam sabida akwai sosai ma tun daga kan yanayin gine ginen,batasan yaya za'a k'arb'esu ba gashi ta shiryawa wannan cewar setaga daidaituwar me gidanta da mahaifansa da danginsa wannan kad'ai zata masa ta wanke masa bak'in cikin data dasa masa,dukkuwa dayake sam besan sokoto suka dosa ba a zatonsa me dugurin zasu, ko Deeyah ma batasan sokoto zasu ba azatonta meduguri zasuje.....

Mom Nu'aiym

BABU WAIWAYEWhere stories live. Discover now