*HASKE WRITER'S ASSO.*(Home of expert and perfect writers)
*BABU WAIWAYE*
BILLY GALADANCHI
Sadaukarwa ga K'awata
*HAFSAT ELHAM**Aunty saudat wannan page din nakine kyauta ke kadai kiyi yanda kikeso dashi*
02
Bayan daddy ya dawo da kwana biyar yayi kiran Deeyah tazo ta zauna kusa dashi,tattare nutsuwar shi yayi zuwa gareta yace
"Little dama ina sone in sanar dake cewar zuwa nxt month zaki wuce london, agarin Bumpa karatu, na neman gurnin karatu a jami'ar N A C dake can, kuma sun baki phermacy" qirjinta ne yayi mugun dokawa ta dago kanta da sauri ta kalleshi,tama rasa me zatace tunani take anya daddy na santa kuwa? Anan babu makarantu ne kokuwa shi bayasam zama da ita ne?
"Little bakice komai ba?" ya sake cewa,gyaran zama tayi tace kanta a qasa
"Daddy kai kadai nake dakai a duniya, dan Allah karkace zaka nesanta ni da kai, ka barni anan kd nayi karatuna bana san barin garin ma bare qasar gaba d'aya" kallonta sosai yayi shifa dama sabida kawai ta rage damunshi da zancen mamanta da dangi yake so ya tura ta can,sabida bashida amsar bata duk sanda ta tambayeshi seya takura ya rasa nutsuwarshi gaba d'aya,Karatu me inganci nakeso kiyi Little,mesa duk sanda namiki abin kirki seki bashi wata manufar? Dan Allah ki dena mun haka kuma ki sani karma ki bata bakinki sabida tafiya london ba fashi" sadda kanta tayi qasa cikin damuwa me yawa ta kasa furta komai se zuciyarta dake tafarfasa tamkar ta fasa qirjinta ta fito takeji,tashi tayi zuwa d'akinta rai a b'ace tama rasa meyake damunta arayuwa,lallai yau ta dad'a tabbatar da zarginta akan cewan lallai daddy bashi bane ya haifeta,inko shine ya haifeta toko lalllai akwai ta hanyar datazo duniya wataqil ba hanyar halak tazo duniya ba, kwana tayi kuka ko abinci bata iyaci.
Haka Deeyah ta share wata d'aya cur tana cikin bakin ciki,ko abincin kirki bata iya ci, rokon duniya kuwa tayiwa daddynta amma fir ya kafe akan lallai setaje karatun turai, koda lokacin tafiya yazo gaba d'aya ma bata fasa roqarshiba amma fir yaqi ranar da zata tafi kuwa tasha uban kuka mara misaltuwa sannan kuma yasha roqo na gasken ma sosai akan ya hakura amma fafir yaqi,koda taji cewar sema taje da kanta zatayi registration ranta ya qara b'aci, zaunar da ita yayi yace
"Little nasan ke qaramar yarinya ce sosai kuma na tabbatar kobaki fahimci abinda nake nufi ba yanzu zaki fahimta ne nan gaba inshaa Allah, Zan zuba miki kudade a acc naki ko wane wata wanda zasu taimakeki harki kammala karatunki nakuma zauna nayi tunani naga cewar tunda kike rayuwarki ni kadai kika sani gashi rayuwa sam batada tabbas zanyi iya mutuwa yau ko gobe,wannan ya sanya na yanke shawarar baki kudi masu yawan gaske wanda zaki taimaki kanki a rayuwa ba yan bana raye kuma nasani daddy baqi baze tab'a bari rayuwar ki ta salwanta ba ko bayan ba raina,amma dukda haka zan baki kudade, bance kije turai ki yi shashan ci,aduk inda kike kiji tsoron Allah ki roqe mutuncin kanki da nawa ko bayan idona,banda biye biyen qawayen banza,bankumace ki dauki aqidar yahudawa ba sabida ba aqidun kirki bane,ban yarje miki dawowa hutu ba harse kin kammala karatunki gaba daya,sabida bansan me zaki zo kiyi anan ba,zan riqa zuwa dubaki dankaina,duk sanda hutu yazo zanzo na miki shi acan,kina jina ko? " da sauri ta d'ago ta kalleshi shikuma ya kauce kanshi da sauri murya na rawa tace
"Daddy Amma dukda haka ai inada friends anan dan Allah ka taimaka koda qarshe shekarane ina dawowa tunda kanada halin yin hakan" cikin takaici yace
"Haleemah na sanar dake baza muyi wannan ba sam, ba dawowa hutu,ina sone ki koyi yin rayuwarki ke kad'ai ba tare da saka hannun dangi ko wasu yan uwa ba, ki yi taki rayuwa irin tawa, zan zuba kudade da yawa a bnk acc naki kafin ki isa london zasuyi, kiyi first year registration naki kiyita karatu ga kudi nan masu yawa bazakiyi talauciba,bazakiyi rashin komai ba arayuwa zan baki dukiyar da zaki manta tambayata kudi ma bare wanina" Kallonshi tayi zuwa yanzu kam ya qara dagula lissafinta tace cikin dakiya
"To Daddy na maka alqawarin dogaro da kai dakuma koyon rayuwa nikadai ba tare da dangi ko yan uwa ba har abada" sam be fahimci kalamanta ba ya zata ta sakko ne,ya dinga zabga mata albarka ba adadi,wani kallo ta bishi dashi harya bar wurin kallon da ita kad'ai tasan ma'anarshi.
Deeyah yarinyace wacce batada surutu ko kadan, hasalima sam bata magana,tanadq saurin fushi da kuma riko wanda bashida kyau ko kadan, a yau dai ta qudurta aranta zatawa daddy yanda yakeso zata zauna ita kadai a rayuwa zata rayu rayuwa mara y'anci kamar yanda yakeso, wato bayan yarabata da duk wani dangi yanzunma so yake ya raba da friends da family friends nasu gaba daya..........
*LONDON*
Koda Deeya ta sauka a london acc nata acike yake damkal da billions of dollars, Gaba daya ta kudurta wa ranta baiwa daddyn nata mamaki,ta shiryawa kanta rayuwa me tsafta, sauya gari tayi daga garin da mahaifinta ya san ya turata anan uk wato london, ta koma E.U university dake Beilin, ta nemi gurbin karatu a phermacy d'in ta kama hayan gida ta tunkari rayuwarta ita kadai bayan sauyawa kudadenta ma'a dana zuwa sabon bank acc da kuma wurgar da layukan wayarta........
Allah sarki Deeyab ta kudurta ranta cewar babu waiwaye acikin rayuwarta har abada, bazata tab'a neman daddy ba tunda ta fahimci sam bashida burin daya wuce yaganta ita kadai,bashida niyyar sadata ga yan uwanta ko mahaifiyarta wata qil ita din yar tsuntuwa ce.......
Masu karatu koyaya kuke ganin zata kaya? Lallai ina tsammanin akwai matsala babba agaba....
Mom N'uaiym ce
YOU ARE READING
BABU WAIWAYE
General FictionBugun zuciyar tane ya qaru, ganin shigowar Al'ameen gidan, ktchen take qoqarin shigewa sanda ya qaraso gabanta ya murtuqe fuska hade da ce bayan ya qura mata manyan idansa "Ina sanin meye asalinki? Wacece ke? Wannan aikin dakike beyi kamada jikinki...