page 8

2.4K 175 2
                                    

*HASKE WRITER'S ASSO.*(Home of expert and perfect writers)

*BABU WAIWAYE*

BILLY GALADANCHI

Sadaukarwa ga K'awata
*HAFSAT ELHAM*

08
Ganin yaa Bg ya wuce ya sanya deeyah ta fito gwiwar ta a sace tazo suka gaisa da Hisham cikeda mutunci ya kalleta yana murmushi yace

"Deeyah durling muje na direki a gida ko?" rausayar da knata tayi

"Hisham kayi hakuri zan je a motan haya, jiyan ma nasha wuya a wurin mommy wlhy basa so" murmushin mugunta yayi ya sosa kanshi

"Mommyn ita bata san suruki? Muje na gaidata nace mata yayan kine kuma her suruki to be ko bakya san d'an baki?" dariya ta bushe dashi itadai tana yawan samun nishad'i da zantukan Hisham shiya sanya takejin wani abu a can qasan zuciyarta game dashi, kasa yi masa musu tayi ta fad'a motar kurun suka hau hanya,d'an waigowa yayi ya kalleta a kaikaice yace yana shafa gemunshi yayinda dayan hannunshi yake kan staring motar yace

"Muje state out na siya miki milkshake ranar naga kinsha da yawa kinga daganan semu wuce gida gun momy" Batace masa komai ba illah murmushi kawai yana karb'o milk shake din ya kaikaci idanta dayake tana mota ya mata barbadin wani abu, ya kawo mata ba komai a ranta ta karba ta zuqeshi ta tas,kan kace meye wannan ta soma ganin biyu biyu, murmushi yayi aranshi yace "Naje gidanku a ganni gobe a kamani? Aiba daniba wlhy shegiyar banza yau oga zeyi dinner dake daganan nayi brkfast da safe" a haka dai harta rasa tunanin ta bacci me nauyi yayi awaon gaba da ita, a haka ya jata ya daura hannunta a saman wuyanshi yana janta seta bude idanta se kumabtabrufe jikeda nauyin da suke mata,mutane kuwa kallon mara lapiya ya dakko suke musu, Bg da dama biye yake dasu ya kula da she's not ger help dt means drink daya bata ba daidai yake ba lallai ma, binshi yayi har wurin room din da ya shiga, yana jinsu suna shewa ogan yace

"Wacece wannan kuma?"

"Oga wannan danyar yarinyar ce ba yar hannu bace seda dabaru" murmushi yayi yace "Kayi daidai a mata tsirara a sanya mata turaren danafi so zanje inga wani friend a qasa in dawo" Yana fita kuwa Hisham yayiwa Deeyah tsirara haihuwar uwarta ya shafe jikinta da turarukan ban mamaki,shi kuwa yana ganin wannan mutumin yabi bayanshi yaje ya karbi dakin dake manne da nasu hisham na barin dakin yayi saurin shiga yaje ya daukota yana labe labe kar wani ya ganshi da mace tsirara ko a turai se an masa wani zargin yayi sa'a ba kowa yayi saurin shigewa d'akin ya dire ta a gado yaja bargo ya rufe mata jiki, fitowa yayi ze rufe ta a dakin da sunan yaje ya kwaso mata kayan ta sabida jakarta kawai ya dakko seyaga wannan alhajin ya shige cikin dakin,har after 10 na daren ranar yana jiran yaga an fito yaje ya dakko amma shiru tun shiga alhajin be fito ba se Hisham dake ta yawo hankalinshi duk a tare se kuma sukayi checking out suka kwashe komai nasu kuma ya binciki cleaner din an tabbatar masa basu bar komai a dakin ba ma'a na dai sun kwashe har kayan nata,dafe kanshi yayi dole yaje ya siyo mata jallabiya black me hade da mayafinta gaba daya,da bra da pant da under, ya dawo koda ya dawo pass 12,haka ya kwanta a qasa har gari ya waye har akayi kiran sallan asuba sannan yaje yayi sallah ya dawo tanata bacci, yawa momy qarya dama tun jiya akan deeyah ta sanar masa zasuyi wani karatu over night kuma yaje skul d'inma ya bincika hakanne,da wannan momy bata nemi deeyan ba,ya zauna yana kallonta tana bashi tausayi sumar kanta duk a bace ta rufe mata fuska,hannu ya sanya ya janye mata sumar da murmushi dauke a fuskarsa, kamar ya tsikaleta se ta farka, shikuma tamkar mara gaskiya seya ja da baya da sauri, bude idanta tayi sosai danta tabbatar da abinda take gani da sauri ta zabura zaune ganin ta babu kaya ajikinta ya sanya ta rud'e ta soma ban baki "Yaa Bg dan Allah kayi hakuri wlhy bazan qara maka lab'el ba qaddane ko wannan,ka rufamun asiri dan yaa rasulullah wlhy kaji na rantse bazan qara ba,karka cutar dani ka rufan asiri,tasowa yayi yazo kusa da ita yana so ya mata bayani cikin nutsuwa aikam ta zabura ta sauka daga saman jikinshi da duvet a hannunta tana kakkare jikinta dashi

"Allah nace fa yaa Bg nashiga daddy kazo ka taimakeni dan Allah ina kake daddy,kaga abinda nakewa gudu kace i should stay on ma own, dan Allah Yaa Al'ameen kayi hakuri" dafe kanshi yayi ya qara matsowa kusa da ita wannan karon wurgar da duvet dinma tayi cikeda tsoro tayi hanyar barin dakin, aikam yana qarasawa gunta ya wanka mata wani lafiyayyen mari seta taga taurari, yace cikin tsawa "Ke mahaukaciyar ina ce ki nutsu mana" tama kasa rufe jikinta gaba daya a rude take sauka tayi a saman gwiwowinta ta hade hannayenta tana murzawa cikeda tsoro

"Yaa Bg Allah nace,karka wulaqantar mun da yanci na, idan nayi haka banwa daddy adalci ba,ba haka yakeso na zama ba yace in riqe mutuncin kaina,in nutsu insan me nakeyi dan Allah ka tausayawa maraicina,bansan kowa nawa ba karka zama sanadiyyar gurbacewar rayuwa ta dan Allah" rasama yayi me zaice ya fahimci kuskurensa na barinta tsirara lallai wani tunanin zatayi ya kuma kula bata masan cewar bashi bane ya kawota nan, dakyar yace

"Shi Hisham din da kika bi mesa baki neme shiba anan?" zare ido ta qarayi tace
"Ni cewa yayi dani zeje dani gun momy,bansan cewar hada baku kukayi amun wannan abinba,banmasan kunsan juna ba,se dazu dana ganku tare dan manzan Allah kayi hajuri" gano ma yayi ambatar hisham da yayi ya qara cabe al'amuran da sauri yace

"Ke ki nustu kiji bayanin dazan miki kina jina" ganin yayi maganar a hankali ya sanya ta qara rud'ewa ta miqe tsaye

"Banso in saurareka wlhy, dan Allah kamun rai ka maidani gun momy karka cutar dani yaa Bg dan Allah" hannu ya sanya ya riqo kafadunta ya jijjigata yace

"Calm down Deeyah,ba abinda zan miki yanzu maza jeki ga doguwar riga can da inners da komai ki saka na maidaki gun momyn,kuma yanzu safiyane tun jiya na sanar mata cewar kunada karatun da zakuyi over night a school shiyasa zaki kwana, and karki sauya wannan maganar, kuma karkiji tsoro ba abinda na miki wlhy a qasan ma na kwana,aike qanwa nane bazan iya zaluntar kiba" da sauri taje ta dauki kayan ta saka tazo ta zauna ta kasa ce masa komai,Yayinda shi kuma yana tunanin yanda ze warware mata komai zuciyarsa se zafi takeyi kasancewar sam beji dad'in yanda ta dauki abin a kaikace ba bema taba tunanin abin ze juye masa haka ba, wato jiyan ta ganshi da Hisham shiya qara cabe komai, dafe kanshi yayi dake barazanar tsagewa gida biyu yace "Yaa Allah " kallonshi tayi tace murya na rawa

"Yaa Bg im so sorry plss wlhy bazan qara ba" bece komai ba yafi 30 mnt a haka,sannan yace daga baya "Tashi muje gida" koda sukaje gidan jikinta a mace, kai tsaye part nasu ta wuce tayi wanka se dube duben jikinta takeyi,tsanar yaa bg me tsanani ya taso mata a gaba, lallai wannan man din anyi macuci da ban farka ba sedai ya gama hallakani,tunda ko ya bullo da hakan lallai barin ya sameta da gaggawa......

Mom Nu'aiym

BABU WAIWAYEWhere stories live. Discover now