*HASKE WRITER'S ASSO.*(Home of expert and perfect writers)
*BABU WAIWAYE*
BILLY GALADANCHI
Sadaukarwa ga K'awata
*HAFSAT ELHAM*10
Duk wani abu datasan zata buqata ta gama tattare abinta gu daya, ta sakkowa cikeda azama se kuka take tanajan akwatin nata cikeda qunan zuciya, Bg ne yasha gabanta yasha mur sosai yace
"Me hakan yake nufi Deeya?" kallon shi tayi se kawai tarasa mekw mata dad'i tafada jikinshi bayan tayi wurgi da akwatin ta soma rera wani kuka me tsuma zuciya sanda tayi me isarta be hanata ba sannan ta dago tace dashi
"Tun tasowata nake rayuwa ni kadai kamar mayya, tunda nasan girman kaina nake begen ganin mahaifi yata, wlhy danasan haka ta wurgar dani akan jikin da ze zama abincin tsutsa wlhy daban sha wahalar neman taba, danasan akan wani qyalqyal banza na duniya ta cillar dani wlhy daban sha wuya wurin bijirewa mahaifina da kullum yake tare dani akan dadi ko wuya, ko aure be qarayiba sabida bakin cikin data saka masa,danasan cewan ku dangin tane daban zauna daku ba wlhy, i've heard enough yaa Al'ameen zan tafi kuma karkace zaka hanani dan bazan hanu ba, dukkanku hainku daya dangin su mamana, sankai kaima haka kaso kai raping nawa, momy ne da T zee kawai ba haka ba,kuma ka sanar mata bazata sake ganina ba har abada!!!!!!" tana kaiwa nan taja akwatinta qiii tayi waje a fusace cikin kuka da qunan zuciya, shikuwa tsayawa yayi sororo yana kallonta ya kasa koda motsi, can taje kai tsaye ta miqa a warwarayenta masu guda shida na zinari aka bata kudinsu, ta kama hayar gida madaidaici wanda kwananta biyu a hotel kafin ta samu gidan ma,komai akwai ciki har kayan kallo, one bed room ne da parlor,se ktchn da dining kalar ginin turawa dai, ta siyo food stuffs ta dire sauran kudadenta a bank, duk wannan yawon datakeyi yaa bg na bibiyarta batare data sani ba sam, sabida yarasa dalilin damuwarshi akan yarinyar gashi ya kasa sanar su momy duk kalan neman da suka mata kuwa,ya sani lallai favorite aunty dinshi ta rafka babban kuskure mara faduwa ma akan wani body shape take ajiye yarta datayi nakuda da kanta sekace aikin asiri, yanaji yana gani amma sam ya kasa fada,gashi maryama jiki ya qara rikice mata,ta hango tsanar ta qarara acikin idan yarta daya tilo a duniya.
*Bayan wata d'aya*
Deeyah ta kammala lectures nata, tana tafiya domin hawa bus dazata sadata da unguwar su ta hadu da yaa shuraim, sam ita batama kula dashi ba amma shi kallo daya ya shaidata,yakuma san meya faru da daddy fari akan nemanta da akayi kusan 4 yrs aka rasa yana can kwance tamkar matacce ma,se kwana kinnan nema akace ya soma tashi yana yawa tawa amma ko aiki baya zuwa, da sauri ya tsayarda me taxi d'in ya fito,kamar daga sama taji muryan dabaza ta tab'a mantawa da ita ba kira sunan ta, cak ta tsaya sannan ta juyo a hankali b'angaren dataji amon muryan, tsayawa kallon juna sukayi na y'an daqiqu kan daga bisani ya tako a hankali yazo daf da ita yace "Haleemah kina duniya dama kikabar daddy fari acikin wannan yanayin na rashin lafiya kusan shekaru uku kenan? " Zabura tayi ta dafe qirji tace "Rashin lafiya kuma yaa shuraim ? Nashiga ukuna, me kuma ya sameshi?" kallonta yayi cikin madubin idan dake manne a idanshi yace " Ina zakije?" cikin mutuwar jiki tace "agidana zankoma na tashi daga school ne" nuna mata taxi yayi yace "Muje" ba musu tabi bayanshi ta gayawa me taxi d'in inda zasu ya kaisu, acikin gidan ta bashi ruwa yasha sannan tace
"Yaa shuraim kace daddy fari bashida lafiya" amaimakon ya bata amsa seyace da ita
"Mesa kikazo nan garin baki sake waiwayar gida ba baki kuma kira kowa ba,kinsan halin da wannan shirmen naki ya jefa daddyn ki kuwa? Toki sani yanacan kwance tun dayazo hutun qarshen shekara yaji babu labarinki,sanar dani haukan daya kaiki zaman kanki a london?" kuka ta saka masa
"Haba mana yaa shuraim ni kenan tunda na taso a rayuwa ta ban taba sanin dadin uwa ko dangi ba, bantaba samun kaina acikin dauwamammen farin cikiba,kowa nawa baya bani kulawa....daganan ta kwashe tarihin rayuwarta tun daga A har Z ta sanar masa komai ta qara da cewan
" Yaa shuraim mesa daddy yasan shi kadai ya ragemun danake gani inji dad'i se kuma yace ko hutu bazanje in ganku ba kuda nake yan uwana,ka taba ganin inda mace akace tayi rayuwarta ita kadai a wani country daba nata ba, kanna hadu da mommy na zata a gidan marayu ya dakkoni sabida a iya sanina ko shege yanada dangi uwa da uba kuwa" Sosai yarinyar ta bashi tausayi, dama yana tausayinta sosai bama tausayi ba santa yake tun tana yar qaramar ta, kawai dai ya kasa sanar mata ne kuma shima yasha fama da ciwon rashin ta,duk sanda yazo london haka ze riqa zagayen gari gari sabida kawai ya ganta, yayi jinyar rashinta sosai yau duk jarumtarsa sanda ya mata kuka agabanta kuma, itama a wannan lokacin tsohon abin nan datakeji game dashi ada ya dawo mata sabo fil aranta babu wanda yasan dan uwansa na sansa aciki, dakyar yayi murya yace
"Kiyi hakuri,zancen zama ke kadai kuma hadda laifinki duk yanda naso in sakaki ajikina guduna kike Deeyah, wasu lokutan sena miki magana kimun banza rashin maganarki ya taimaka sosai wurin kadai cinki, nasoki tamkar raina ze fita babu yanda ban nuna miki ba kikamun banza dole na aure margayiya farida ina tsoron kicimun mutunci" zabura tayi dajin kalamnshi,tun zuwanta london ta fahimci tana qaunar yayan nata, dak'yar ta saisaita kanta ta rage tunanishi
"Yaa shuraim badai wai Aynty fary ta rasu ba,naji kace margayiya?" zaman dirshan ya sakko yayi a carpet "Ba farida ba har yayanki munir Allah ya masa rasuwa tun bayan barinki Niger da watanni hudu yayi accident, sannan kuma farida gurin haihuwa ta rasu,wani irin kuka ne yazo mana ta zauna kuwa tayi one hour tana kukan rashin munir shida suka fi shaquwa koda yake ba wani masa surutu takeba ashe rabuwar kenan? Tasha kuka dakyar shuraim ya rarrasheta sannan ta kalleshi tamai ta'aziyya tace "Ina fatar ka qara aure?" kanshi ya sadda akasa yace "Bazan iya qara aure ba Deeyah, ke nake jira ke nake fatan sake aure, ina tabbatar miki da cewar duk wannan zagayen danakewa wannan contry danke nakeyi ba garin dabana zagawa nemanki, ki taimaka ki dawo garemu kuma ki yafi ummanki" kallonshi tayi amma batace komai ba seda ya sake cewa "Kinji?" sannan ta rausayar da kanta tace "Zan koma gida dole amma gaskia yanzu ina gaf dayin final exams nawa so se nan da 4 months,zancen gaskia kuma banida kudin jirgin zuwa Niger" murmushi yayi yace "Wannan yafi komai sauqi deeyah, yanzu dai barin kira daddy baki ya sanarwa daddynki na samoki a laondon kuma kina cikin koshin lapiya karatu kuma saura wata 4 kawai ki dawo" murmushin dai kawai ta masa ya daukii waya danya kira daddyn nashi....
*Bayan sati biyar*
Su maryama sun gama yanke shawarar zuwa Niger dukkansu nxt month har Bg da humaina,zasu jira ta kammala dxams sanan suje suyiwa iyayen su bayani aje abaiwa Musa hakuri, yaa Bg ya gama damuwa gaba ki daya hankalinshi nagun Deeyah kullum yana tsare da ita kuma ya kula se wannan satin ya dena ganin shuraim a gidanta,wanda yana lura duk sanda suke waje ta dinga wage baki kenan tana fara'a....a bangaren Deeyah kuwa da shuraim shaquwa ce me tsanani ta shiga tsakaninsu kuma tana yin waya da daddyn ta sosai yanzu har ya soma warwarewa sedai jiki ba kwari kam, Soyayya ce daga Allah tayi alqawarin inshaa Allah batada miji se shuraim sannan kuma bazata qara waiwayar mahaifiyarta ba gida zata koma gun daddy kawai dama yanzu saura mata 6 weeks exams.......
Yaa Bg ne yazo yayi knocking a gidanta bayan yaga shigarta gidan da befi mintuna goma ba, zuwa tayi ta bude batare datakoji waye ba, kallon kallo suka tsaya yi sannan tace "Ya akayi kasan nan gidan?"
"kwana ne kawai banayi anan amma nafiki sanin nan gidan kullum ina tsare dake,baqon dake zuwa miki kwanakin baya waye shi?" kallon mamaki ta masa sanna tace
"Shine wanda zan aura kuma maqotanmu ne a Niger koma nace family friends namu ne" wani abu yaji ya daki qirjinsa dajin wannan haukan ya sake kallonta yace
"Aure kuma yaushe aka qulla wannan?" dauke kanta tayi gefe daya tace
"Tunkan nazo london" jikinshi ne yayi sanyi yace da kyar "Dama zuwa nayi muyi sallama, zamuje Niger dukkanmu kuma ki sani Aunty maryam batada lafiya har yanzu ya kamata kisan cewar uwa uwa ce,kin gane ba?" murmushi tayi
"Allah ya bata lafiya" iya abinda tace kenan taja bakinta ta tsuke,tama rasa mesa takejin ba dadi ance batada lapiya....
Mom Nu'aiym
YOU ARE READING
BABU WAIWAYE
General FictionBugun zuciyar tane ya qaru, ganin shigowar Al'ameen gidan, ktchen take qoqarin shigewa sanda ya qaraso gabanta ya murtuqe fuska hade da ce bayan ya qura mata manyan idansa "Ina sanin meye asalinki? Wacece ke? Wannan aikin dakike beyi kamada jikinki...