Assalamu Alaikum warahmatullah
Ga mu nan tafe da tsohuwar ajiya, na rubuta shi 2013 na yi editing 2015 yanzu ga shi na sa muku 2018. Ku karanta da ido ɗaya don lokacin da aka rubuta lokacin kanta wayis ne.Zan dinga updating sau biyu a rana, safe da dare don mu kamalla da wuri. Posts din zasu kasance kana na kamar yanda nace rubutun kanta wayis ne.
Love You all
Ummu-Abdoul💞💞💞💞💞
Wannan labarin anyi shi ne ba don wani ko wata ba, bazan kirashi 'kagagge ba don kuwa kashi ashirin cikin d'ari (20%) ya faru da gaske, kuma nayi hakan ne tare da izinin wacce abin ya faru da ita..
Godiya ta Musamman gareku makaranta domin a dalilinku ne kullum muke tsamo abin da yake illa ga Al'umma muke fadakarwa ta sigan labari. Allah ya yafe mana inda mukai kure..
2nd edition 2015..
(1)
Bakin duhun d'akin yasa na gagara gane ahlin d'akin. Sheshshekan kuka da nake ji ya k'ara tabbatar min da mutum a d'akin.
Bud'e k'ofan akayi, haske ya mamaye d'akin yayinda yara biyu suka shigo cikin d'akin sanye da kayan makaranta (uniform).
Da gudu babban ta karasa jikin matar da ke zaune akan katifan da ke dakin. Kwanciya tayi jikinta hakan yasa karamin yayi hakan shima.
"Yan albarka kuyi karatu sosai yau kunji, kun min addua kuwa?" Ta karasa zancen tana mai kallon fuskokinsu.
"Ammi nayi miki, nace Allah yasa ki dena kuka" cewan Babban Yar shekara bakwai ta fadi fuskanta na nuna alamun kuka.
Ba tare da ta jira cewansu ba tace, "Oya maza ku je makaranta, Shireen ki kula min da Sahal kinji .
**shireen sunan yan Persia ne da ke nufin (Farinciki).
(2)
Fitan yaran yasa ta tashi, bayin da ke cikin d'akin Ra Shiga tayo wanka.Doguwar Riga ta sanya, bata bata fuskanta da wani kwalliya ba, idanunta sun kod'e alamun ta sha kuka. K'uraninta ta dauko ta fara karatu cikin suratul 'Daaha.
Ba ita ta tsaya ba se da agogon d'akinta ya buga 'karfe Tara. Dai dai suratul Namli ta tashi ta kabbarta sallah.
Raka'a takwas tayi kafin ta d'aga hannu sama tana Addua. Duk yanda naso naji me take fad'i ya gagaren saboda tausasa muryanta da tayi cike da ladabi da mik'a wuya. Tunani nake meyasami baiwar Allahn nan.
"Agithniee ya Rabbi, Agithniee ya Rabbi" da take fadi ya dawo dani daga duniyar tunani na. Kuka takeyi sosai tana mai Neman d'auki wajen mai duka.
Tausayinta ya mamaye ni Amma abinda ya burge ni ya kara min kwadaituwa da son jin wacece ita shine ganin faraa a fuskanta yayin da ta iddar da addua. Murmushi tayi tace "Allah kenan, ubangiji mai Rahma, Madallah da abin dogaro kuma ubangijina Allah".
Bud'e kofan aka sakeyi a karo nabiyu. Wani matashin mutum ne ya shigo, kwarjininsa da kamewarsa ze hana duk wani mai tsaurin ido tunkararsa.
Binta yayi da ido cike da tsana da kyama. Yafi karfin minti goma tsaye ba tare da yace mata komi ba. Chan kuma ya juya ya tafi.
"Hmmmmmn Allah agajinka nake so cikin gaggawa, ka isarmin ka bayyanar da gaskiya". Abinda ta fad'i kenan baysn fitarsa.
***
"Naseer na ce maka kuje ayi gwajin kwayoyin hallitarsu (DNA). Wata uku kenan ka gaza daukan mataki kana gallaza ma baiwar Allah. Haba""Mahmud wani DNA zaa gwada, har yau ta gagara karyatawa, kuma Abba ma cewa yayi zata aikata fin hakan".
"Amma ai Allah cewa yayi in fasiki ya zo maka da zance kayi bincike.. Gaskiya daya ce daga kinta se bata, ni kaga tafiyata". Mahmud na gama fadin haka yasa kai ya fita daga shagon.
YOU ARE READING
'KAZAFI
General FictionSau da yawa hotunan mu kan shiga kafofin sadarwa, tare da lbr mabambanta haɗe da hotunan wanda hakan kan iya zama Qaharu.