... 'Kazafiii...26
©Ummu Abdoul
Kuncin rayuwar da Sumayya ta shiga ba'a magana, bata da wanda zai bata hakuri sai tagwayen k'anninta mata. Kullum cikin kukanta take kai ma Allah 'ko'kon baranta.
******************
Cigaban labari....Yau ma kamar kullum addua take bayan ta idar da sallar walha, sallamar da taji ne yasa ta sallamewa tare da shafa addu'ar.
"Hamma Mahmud kai ne a gidan? Marhaban bika" Ta fad'i tana mai murmushi. Har cikin ranta tayi murna da zuwanshi don ko ba komi zai bata shawara mai amfani.
"Sumayya zuwa nayi in tafi dake"
"Ina?" Ta fad'i tana mai zazzare idanu
"Ba wani dogon bayani nake so ki shiga ki kwaso kayanki da zai miki kwana biyu, da na su Shireen, yanzun nan d'ifa zamu wuce, kinga yau suke yin hutu."
Cikin hanzari tayi kamar yanda yace, daga gidan basu tsaya ko ina ba sai makarantar su shireen, ta dauke su suka kama hanyar 'Difa.
Duk da garin ba bak'onta bane amma wani farinciki ya ziyarce ta yayinda ta sha'ki iskar garin.
Dangin su Nasir sun kar6e su cikin girmamawa, sun ci sun sha kamin Mahmud ya nemi komawa. Ta rako shi bakin mota sannan ya kalleta yace
"Babu wanda zaiyi tunanin kina nan, kuma ba wanda zan fad'a mawa ga inda na kaiki, in yana son ganinki sai yayi abinda musulunci yace kayi in har fasik'i yazo maka da labari"
"To hamma amma Abba fa"
"Abba baya son sa bakinshi ne kawai, amma farin cikinsa ne gaskiya tayi halinta. Ki cigaba da addua kawai"....'kazafiii... 27
©Ummu Abdoul
Karfe goma sha biyu (12:00) ya masa a makarantarsu Shireen, ba karamin firgita yayi ba da malaminsu yace tun k'arfe goma (10:00) aka zo aka tafi dasu.
Cikin hanzari ya isa gida nan firgicinsa ya karu inda ya iske babu sumayya ba yaran. Ga alamu de na ta kwashe wasu daga cikin kayansu.
Daukan waya yayi ya kira ta, nan fa ya tuna ya kwace dukkan wayoyinta. "Toh ina zata, me zance ma Abba" ya fadi yana dafe kai.
"Tabbas bazata wuce Azare ba, ko kuma wajen saurayinta ba" abinda zukatanshi ke raya mishi kenan.
Waya ya fara ya na tambayan kanninta ko ta fad'a musu inda zata, duk suka nuna basu da masaniya akai.
Komi yai ta zuwa masa tun farkon komawansu hannun sheikh, rikon da marigayiya tayi musu, rasuwanta, yanda Mahmud ke yawan fad'in cewa "bamu da abinda zamu biya Abba don da yanzu muna k'auye".
"Oh ni Nasir son zuciya da kishin banza ya sa na kasa rik'e masa 'ya, innalillahi wa inna ilaihir rajiun".
Haka yai ta tunani, rashin madafa ya ga gara ya kira Mahmud su san inda zasu fara.
"Dan uwa Sumayya ta gudu da yara" ya fad'i sanda Mahmud ya d'aga wayar.
"Bata gudu ba, ni na d'aukesu na kaisu inda suke da daraja, ina ba yaranka bane su".
"Ina ka kaimin iyali na?"
"Ana aure da zargi ne, in zaka ce ina nakai maka matarka kace, yara ba naka bane"
"Mahmud zan kai karanka Kotu fa, ka dawo min da iyali na"
"Man tuk'i nake ka jira na dawo". Yana kaiwa ban ya kashe wayar.
Huci yakeyi kamar mayunwacin zaki, "mai Mahmud ke nufi, yafi ni son Sumayya ko mi, yafini sanin abinda ya dace ne da ze daukan min iyali, bari ya iso zai ma fito dasu".... 'Kazafiii... 28
©Ummu Abdoul
Zaune suke gaban Sheikh kowannensu rai a bace.
Nasir da Mahmud 'yan uwan da ba'a taba jin kansu, tare suke kashewa su binne. D'aya baya k'yashin faranta ma d'an uwansa ko da hakan na nufin 6ata ma kansa ne.
"Kun zo kun tsare ni lafiya kuwa? Me ya had'a ku ko kun sha kayan maye ne da daren nan?" Sheikh ya fad'i cikin fad'a.
"Abba sacemin iyali yayi"
"Sata kuma Nasiru, wasu iyali kuma?" Sheikh ya tambaya cike da mamaki.
"Matata da yara na." Nasir yayi furicib kamar zaiyi kuka.
"Abba na kaisu inda aka san darajarsu ne, bazan bashi 'kanwata ba sai yayi abunda ya dace, ko yau ya shirya zan d'auko masa su Shireen suje ayi DNA daga nan sai a san wani mataki za'a dauka"
"Kai Mahmud ba na ce kar wanda ya sa bakinsa a zancen sumayya ba?"
Mahmud ya sadda kansa
"Abba ka gafarce ni"
"Toh ka tashi ka maido masa da iyalinsa"
"Toh Abba, Allah 'kara d'aukaka". Yana fadin haka yayi sallama ya fita.
Kunya ya hana Nasir motsi, tunani yake me yasa Abba yanke wannan hukunci, ko dai haushinsa yakeji shima?
Saida Sheikh ya masa magana ya tashi ya tafi jiki ba kwari.
Tun daga ranar Mahmud ya b'ace, ya shirya musu zuwa Otta Farms a jihar Ondo. Yaje har 'Difa ya dauko su Sumayya sannan suka tafi.
Hankalin Nasir ya tashi rashin ganin Mahmud da su Sumayya. Duk inda ake tunanin suna can anje basa nan.
Zasu dawo yau, gobe, sati daya, sati biyu har wata babu su babu alamunsu. Ranar da suka cika kwana talatin da daya suka shigo garin Bauchi.Check my new story makarantar Malam Lami. It's a short story of not more than 20k words Insha'Allah. Don't forget to read, vote, comment, share to ur faf, frnds of frnds, frnds of frnds of frnds.
Am giving you a double update now, saura kar ku yi commenting duka ehe 😎
YOU ARE READING
'KAZAFI
General FictionSau da yawa hotunan mu kan shiga kafofin sadarwa, tare da lbr mabambanta haɗe da hotunan wanda hakan kan iya zama Qaharu.