...'Kazafii...14 ©Ummu Abdoul
Binsa tayi da kallo har ya fita. Ganin kuka baze fishe ta ba yasa ta tashi ta dauro Alwala ta gana da mai share hawayen bayinsa, Buwayi gagara Misali.
Biki saura sati biyu amma ba abinda ya sauya tsakaninta da Hamman ta, bazatace yana mata wulakanci ba, zasu gaisa, zaayi hira gaba d'aya gidan amma ba abinda ke had'a su.
Ana sauran sati daya bikin sheikh ya tara gaba daya iyalin gidan. Bayan an bude taro da addua yace;
"Dalilin da yasa na tara ku anan ba komi bane se in ja kunnin ki Zulai da yaranki, idan har d'aya daga cikinku yai furucin batanci akan Sumayya har wani da yazo biki yaji, ko cikin danginki ko nawa toh babu igiyar aure tsakaninmu wato abakin aurenki. Idan kuwa har ya dawo kunni na bacin saki se nasa an kulle ku, kin san de zan iya". Iyakan kad'uwa ta kad'u don shirinsu su bata na kowa rai.
"Tab d'an auren da nake lallabawa balle yanzu da yake tashen kudi, ya sake ni in je ina" abinda take fadi a ranta kenan yayinda a bayyane tsaki ta ja
"Mtswwww hakan ne ze sa ace ba kingin maza bace, kai de Nasiru ka kwasan ma kanka rijiyan kasuwa" tana gama fad'i tayi daki tawaganta suka bita.
"Abba wai me ke damun Muhammad?" Fadin Hamza bayan fitan muhammad din tare da Manniru. Shirun da sheikh yayi yasa suka chigaba da hiransu har shi yana musu nasiha akan rayuwar duniya.***
'Yan uwa daga Gamawa da Azare sun fara iso wa, kowa ka gani da murna fal a cikinsa. An gyara amarya tayi kyau kwarai, fatarta se sheki yakeyi, domin Rufaida Omar's SPA aka gayyato tazo tayi gyaran amarya.
ALKAWARIN ALLAH YA CIKA
Dubban mutane daga ko'ina a fadin kasar nan suka hallarci daurin Auren Sumayya Abdurrahman da Nasir akan sadaki mafi Albarka 50,000. An shirya walima ga maza bayan daurin Auren. Inda aka ci aka sha.
Cikin gida ma biki ake sosai, anci an batse. Yayinda kannin marigayiya suka sa Sumayya a d'aki suna bata shawarwari da zatai amfani da shi wajen siye zuciyan Nasir. Sun mata gatan da ko mahaifiyarta nada rai iyakanta zaa mata.
Ranar ita da 'yan uwanta sunyi kukan rashin uwa, mutuwar ta dawo musu sabo haka suka had'u har su Nasir suna kuka, hatta shi sheikh dauriya kawai yakeyi yana basu baki... 'Kazafii.. 15
©Ummu Abdoul
Karfe takwas na dare aka mik'a ta gidanta bayan iyaye sun mata dogon nasiha. Kawayenta da kanninta sun taya ta kwana washegari akai bud'an kai aka watse.
Sunyi nafilan da manzo SAW ya koyar sannan ya mika mata bakin leda ya fita. Babu abinda yake tunawa sai kalaman Zulai gab da zai baro gidan,ta tare shi a harabar gidan "Ahayye wai ango kenan, toh wace irin amarya gare ka don kuwa ba budurwa bace, budurbudur ce ko muna budurwa ko bazawaran budurwa.." Tana kaiwa nan ta kara gaba. Dafa kanshi yayi yana tunani.A bangaren Sumayya kuwa ko kallon ledan batayi ba, ta tashi tasa ma 'kofan d'akin makulli sannan ta chanza kaya. Tambayar kanta take ko wace irin zama zatayi da Hamma Nasiru? Dad'i ya mamaye zuciyarta yayin data tuna adduo'in da kwararo masu yana dafe da goshinta bayan sun idar da sallah.
Washegari tun karfe hudu da rabi (4:30am) ya tashe ta, shi ya jasu sallan tahajjud din,wanda ya kasance wutri ne mai raka'o'i biyar. Ya tsawaita musu sujjadar karshe inda itama ta samu damar rokon Allah ya mallaka mata zuciyar mijinta. Ta roka ma iyayenta gafara da daukacin al'umman musulmi.
Inda tayi sallan asuba nan barci yayi gaba da ita. Ba ita ta tashi ba sai karfe 9am. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Ta fadi yayinda taga lokaci.
A falo ta iskeshi har yayi wanka, zuwa tayi ta zauna a daidai kafarsa tace "Hamma ina kwana"
Dago kai yayi yana kallonta, na kusan dak'ik'a hamsin,kafin ya ce
"Lafiya lau, ga abinci can an aiko daga gida kiyi (serving) dinmu don karfe goma zan fita." Ya fadi yana mai k'ara had'e rai.
Bata ce komi ba d'akinta ta koma tayi wanka ta sauya kaya domin d'aya daga cikin nasihohin da akai mata shine "Kar ki yarda ya fita kina cikin halin k'azanta"
Minti (15) ya dauke ta tayi wanka da kayatarciyyar kwalliyanta da dole ya ba duk wanda ya kalla sha'awa.
A hankali ta bude ma'adanar abincin, masa (waina) akai musu lafiyayya da miyan taushe,ba tare da b'ata lokaci ba ta jona (cordless jug) da ruwa a ciki, cikin minti uku (3) ya tausa ta sake a karamin (water flask) ta shirya a faranti ta kai masa.
Batare da ta nemi shawaransa ba ta had'a masa shayi ta had'a nata sannan ta zuba musu wainar a kwano daya.
"Bismillah food is ready" Ta fadi tana kara gyara masa inda zai zauna a kafet din. Batare da ya ce uffan ba ya zauna, ruwan wanke hannu ta mik'a masa ya wanke kafin su fara ci, suna ci, tana d'an janshi da hira yana amsa mata a gajarce.
Haka suka kammala ta chanzo ruwan wanke hannu ta bashi ya wanke, ba tare da yace uffan ba ya sa kai. Saida ya kusa k'ofa ya juyo yace "Na tafi."
"Allah bada sa'a Ya dawo da kai cikin aminci" Tayi kokarin fadi, shi kanshi ya ji kunyar me yayi. Tunawa da zantuttukan Zulai da Manniru ke bata masa rai.....'kazafii... 16
©Ummu Abdoul
Da rana ma an aiko musu da abinci amma ita kad'ai taci don bai dawo ba sai wajen karfe (8) na dare, kamar yanda tayi da safe haka nan tayi, cikin kwano daya suka ci sakwara da miyan egushi.
Suna kammalawa ta tattara kwanukan ta wanke su, ta rufo kitchen d'in sannan taje daki ta kwanta.
Haka rayuwan ta kasance musu tare suke cin abinci. Har sukai sati uku,baya sakar mata fuska amma hakanan zata zauna tana masa hira wanda amsarshi bata wuce eh, a'a, uhum sai wani sa'in yakan mata murmushi.An tashi da matsanancin sanyi amma bakincikin da take tattare dashi ya sata yin gumi. Bata b'ata lokaci ba wajen had'a musu karin safe, hawaye ke zubo mata, wato ya yarda da KAZAFIN da akai mata kenan. Tana shirya masa abincin ta koma dakinta ta rufe. Babban abun bakinciki ne namiji ya soma neman raya sunnah dakai ya ja tsaki kuma ya barka,wannan wulakanci dame yayi kama?
Baiyi mamakin ganin haka ba don tabbas yasan bai kyauta ba. Zama yayi ya ci abincin sannan ya fita.
Da daddare ma hakan ta kasance, nan ne hankalinsa ya tashi, daki ya bita ya iske ta kwance rub da ciki tana karatun littafin "You can be the happiest woman na Dr Aaidh ibn Abdullah al-Qarni" Gefenta littafin "LA tahzan (dont b sad) ne da wasu littafan duk na Dr Aaidh ibn Abdullah al-Qarni.
Daukan littafin Don't be sad din yayi ya fara duddubawa kafin ya d'ago ta daga kwancen.
"Kiyi hakuri ki qara min lokaci komi zai zama daidai"
Bai jira amsarta ba ya tayar da ita ya rugumo ta yana rik'e da littafin dont be sad in da d'ayan hannun. Ba gardama ta bishi har suka kai karamar falon da suke cin abinci, ya zaunar da ita yana bata abincin a baki. Haka har suka cinye. Shi ya kwashe kwanuka ya kai kitchen ya wanke su ko da ya dawo ta koma daki.
Mamakinsa ya cika ta, tunanin abinda ya faru tayi. Sun gama cin abincin dare wanda duk kayan marmari ne, fruit salad ne se cocktail da tai musu ya ji madara. Ko da suka kammala basu ko iya cin jolof din cus cus din da tayi.
Tun da suka kammala ya jawo ta jikinshi, ranar duk shi yayi hiran, fargaba da tsoro ya cika ta a wani b'arin kuma murna take lokacin wanketa yayi.
Shi ya kaita d'akinshi da kanshi domin daukan jarirai yai mata, anan kuma labari ya sauya salo amma me, bata san me ya faru ba tashi yayi kamar an tsikaro shi, cikin fushi ya nuna mata hanyar kofa "Get out!"
Sum sum ta fice tana mai jin tuquqin bakinciki a ranta. Tun daga lokacin ta dauki alwashin janye jiki daga gareshi..A bangarensa da ya dawo ya iske batanan kuma, hankalinsa ya tashi, fadi yake "Ya Allah ka taimake ni, kar kasa ta tsaneni, ya Allah ka mantar dani zantutukansu Zulai Ya mai rahma mai jinkai."
YOU ARE READING
'KAZAFI
General FictionSau da yawa hotunan mu kan shiga kafofin sadarwa, tare da lbr mabambanta haɗe da hotunan wanda hakan kan iya zama Qaharu.