Uku

1.3K 167 8
                                    

.....'Kazafi... ©Ummu Abdoul 
         (4)
ASALIN LABARI

... 1987 GUMAU

"Alhamdulillah.. Allah ya nuna mana ranar da muke d'okin zuwansa. Nayi farincikin samun uba, megida kuma suriki irin Alhaji. Bacin sani a hanyar samu da yayi ya dauki 'yarsa ya bani. Allah Ya bani ikon sauke hakkinki Aysha."Fadin wani matashi kenan, daga ganinsa baze wuce shekara 27 zuwa 28 ba,  da ka gani ba tambaya ango ne a daren angoncinsa.

Abdurrahman kenan, d'an asalin garin Gumau ne na jihar Bauchi. Mahaifiyarshi 'yar tilden Fulani ce, aure ya kawo ta Gumau duk da dai kusan auren zumunci  zamu ce. Domin kakar Abdurrahman da ta haifi babanshi 'yar  Toro ce, ta nan ne suka had'a zumunci.

Abdurrahman ya kasance babban d'a ga mahaifiyarshi kuma tilon d'anta namiji. Sai kannenshi mata, yana da yayyi 'yan uba maza da mata don Allah ya azurta Malam Muhammad da yara.

K'a'idan gidansu yaro da yayi shekara hudu (4) za'a tura shi almajiranci bazai zo gida ba se yayi shekara tara (9), inda zai zo don ayi masa kaciya, matan kuma na watan Maulidin da suke cika shekara sha biyu (12) yake aurar dasu.

Hakan ya kasance da Abdurrahman. Ya cika shekara (4) Malam Muhammad ya tura shi kasar Katagum cikin garin Azare.

Makarantar Malam Yusufa a tsakiyan anguwa yake, nan kusa dasu akwai gidan Alh Hamza.

Tun Abdurrahman bai saba ba har yazo ya saba, wani dace da yayi amaryan Alh Hamza se ta kaunace shi, abincinshi na musamman ne a hannunta.
****************
"Anty gobe zan je Gumau."Abdurrahman kenan yake fad'i ma uwar d'akinsa da murnansa.

"Kai amma baka kyauta min ba, sai yau zaka fada min."

"Wallahi Anty yanzu Malam ya fad'a min. Kiyi hakuri"

"Toh kadawo anjima zan baka sak'o. Ga abincinka de a kitchen dauka kaci"

Ko da ya dawo da maraice ta hada masa sha tara na arziki, suturu ya kaima yan uwanshi mata da mahaifinshi. Sai kuma wata embilob (envelope) da ta mika masa ya kai ma mahaifinsa. Yai ta musu adduan samun dacewa duniya da lakhira da kuma zuria dayyiba kasancewar basu taba haihuwa ba.

'KAZAFI Where stories live. Discover now