Takwas

1K 132 30
                                    

.... 'Kazafii... 17
   ©Ummu Abdoul.

     Tun daga daren zata girka, tayi kwalliya su zauna suci, amma bayan gaisuwa ba abinda ke had'asu. Shima da yake ba gwanin magana ba sai ya shareta, gaisuwan ma ya daina amsawa cikin sakin fuska.
     Yau da gobe se Allah, Nasir ya wayi gari da matsanancin son Sumayya, kishinta a ranshi ya karu hakan yasa yadaina zuwa gidan sheikh don duk sadda yaje sai an fada masa zancen da zai k'ara masa tabo a zuciyarsa.
     Tunda ya daona zuwa gida yake dawowa da wuri wani sa'in ma tare da matarsa yake cin abincin rana duk da rashin hiran da sukeyi yana jin dadin haka. A haka so da kaunar junansu ke ninkuwa a zukatansu.. ( kira ga mata masu raba kwanon cin abinci da miji, hakan na nisantar da kaunar da ke tsakaninku, cin abinci kwano daya na haifar da soyayya da kauna tsakanin masu ci, haka ku koya ma yaranku cin abinci a tare).
    Yau kamar kullum ya dawo da azahar, hayaniyar da yaji yasa yasan da bak'i a gidan. Da sallamarsa ya shiga nan ya iske Sumayya na dariya, farincikin da yagani bayyane a fuskanta in baiyi kuskure ba rabon da ya gani tun kafin fitowar bidiyon nan.
     Yafi minti goma tsaye yana kallonta, sonta na kara ratsa dukkan sassan jikinsa. Kamar ance ta d'ago sai ta ganshi tsaye, tashi tayi cikin sassarfa ta karasa inda yake, sumbatarsa tayi a kumatu sannan ta amshi ledan hannunsa tana me cewa 
   "Marhabanbika yaa Rafeeq"
   Murmushi kawai yayi yana mai rungumo ta ta gefen shi, sun ba duk wani ahalin falon sha'awa, sai murmushi suke jefansu dashi.
    "Twins ne yau a gidan, (big, bigger) toh ina su (biggest)"
       "Sannu da zuwa, ina yini Hamma Nasir" Suka fadi a tare, suna masu farincikin ganin Hamma na kula da yayarsu.
      Wani sabon hira aka fara, ya tsokani wannan ya tsokani wancan. Sai bayan magriba ya maida su gida. Duk yanda Sumayya taso aje da ita yaqi.
      Son Sumayya ninkuwa yake a zuciyar Hammanta, ko da yaushe gizo take masa, ko yana wajen aiki. Baisan ya akayi ya fara ba amma baya awa daya zuwa biyu bai kirata ba. Bakinsa yayi nauyi wajen fad'a mata kalaman soyayya amma kula kam in aka barta zata iyacewa mijinta yafi na kowa iya kula.

... 'Kazafii... 18
     ©Ummu Abdoul
Sak'o ne ya shigo wayarta, kamar bazata daga ba don kallon da takeyi ya dauke rabin hankalinta.
   "Mssww yanzu haka Mtn ne" Ta fadi tana mai daukan wayarta.
   " I feel so lucky and loved when ever I think of u. In you I found every single happiness of my life. I will forever love and cherish you. Missing you so dearly"
    Ta k'ara duba lamban sak'on ta ga dai tabbas 'HAMMA'AM' din ne rubuce. Ta karanta yafi a kirga sannan ta aje wayar, wani b'ari na zuciyarta na umartanta data maida masa da ko kalmar godiya ne amma saita basar. Sai ma ta tashi ta shiga kicin don daura musu abincin rana.
      A bangaren Nasir kuwa zaune yake yana jiran ko zata amsa, kamfanin Mtn kamar sun san yana jiran sak'o sao turo masa da sakwanni sukeyi wanda duk ya shigo sai ya rok'i Allah yasa Sumayya ce.
     "Angon sumayya tunanin me kakeyi har na shigo baka ji sallama ba?" Fadin Mahmud yana mai hura masa iska a fuska.
    "Kai dai bro ayi sha'ani kawai, ban san sanda na fara son sumayya ba, duk kulawan da nake bata sam bata gani, dazu nayi mata (text) bata ko amsa ba kuma tagani" Ya karasa zancensa cikin yanayi mai nuni da damuwa.
      "Toh kai ta lallabata dai, (don't ever force her). Ni dama na zo ne in fad'a maka Salma (sunan matarsa) na da ciki, kusan wata uku(3)."
     "Allah ya inganta Ya raba su lafiya, ni ko ta ina zan fara ma"
     "Ta inda kowa ke farawa, shiyasa ban son d'ago zancenku baka jin shawara, aka auri karuwa dai kuma aka zauna da ita inaga wacce babu tabbas a iskancinta, shin ka taba sauke mata hakkinta kuwa?"
    "Wallahi d'an uwa zantuttukan su zulai ke hana min komi, da na tuna sai raina ya baci"
     "Wallahi Nasiru Allah sai ya tambaye ka, ita din katako ce, ni barni ma kaga tafiyata tunda zaluntar yar mutane kakeyi, Abba bai cancanci haka daga garemu ba dai" Yana kaiwa nan ya mike ya fita.
      Tun daga ranar sakonni daban daban yake tura mata mai nuna tsantsan kauna, bata taba nuna ta gani ba don a cewanta kar ya sake mata abinda yayi kwanaki.
     Yau tun da ya dawo yake nane da ita, duk inda tayi yana biye, tare sukai girkin dare wanda shi ya zab'a musu, pancake ne da cabbage source. 
     Bayan sun gama ci ya kwashi kwanikan ya kai kitchen ta biyo shi ya nuna sam shi zai wanke. Bayan sun gama suka zauna kallon labarun duniya sai ya shiga mammatse mata kafa wai yaga sun kumbura. Ganin zai takurata ta tashi tayi hanyar daki.
    "Sai da safe" Ta fadi 
      "Allah bamu alkhairi, zan dauki littafin nan please." Ya fada mata yana mai cigaba da kallo.
     Bayan ya gama ya tashi yayi shirin barci sannan ya bita dakin.
    *******************
   "Allah miki albarka Sweety, nagode nagode da kika rike tarbiyyanki. Ki mun izini in kai shaidanki gida."Abinda Hamma ke fadi kenan yana kuka. Kuka sumayya take sosai domin a daren komi ya dawo mata sabo, ta gode ma Allah da bata kasance cikin mata masu sai da mutuncinsu kafin aure ba. 
      Da safe shi ya musu komi na kari, ya gyara gidan kamar yanda ta saba. Wajen sha biyu ya gama komi ya kai mata wani ruwan tai wanka.
      Da rana ma shi yayi musu girkin, ya roke ta gafaran abinda ya mata kwanaki yafi a k'irga, iyayenta sun sha addua sannan ita kanta tasha albarka.
       Bayan sallan isha'i ya umarce ta da ta shirya su fita, basu tsaya ko ina ba sai kofar gidansu. Kallon sa tayi cikin sigan addu'a, murmushinsa mai tsada ya sakar mata tare da d'aga mata gira.
     Cikin sanyin jiki ta bishi har cikin gidan

... 'Kazafii... 19
©Ummu Abdoul
Tayi mamakin ganin kowannensu hatta Hamma Mahmud da matarsa Salma, wajen  babanta ta nufa, ta haye kujeran da yake zaune na mutum biyu ( 2 seater) kwanto masa tayi sai kace kyanwa tasa wani sabon kuka, yana shafata yace    
    "Haba zaujatu Yaasir ummu ammar ke fa kika fara shahada a musulunci, oya (be strong) kamar takwararki, inshaAllahu kinci jarabawanki"
    "Ahayye ai dama na fad'i aurennan baze kai ko ina ba, mai hali kuma." Zulai ta fad'i yayinda take shigowa.
    Babu wanda ya kula ta, ta zauna dogon kujera da yaranta a gefe. Sumayya de na dunk'ule ko fuskanta ta ki bari a gani sai ajiyar zuciya take.
     Bayan bude taro da addua da Mahmud yayi, Sheikh ya kalli Nasir yace
    "Alh ka tara mu nan muyi abinda ya kawo mu, photocopy din l indo na najin barci, ko summyn Nas." Ya karasa cikin sigan tsokana, aiko gaba d'aya se da aka dara.
      "Abba game da KAZAFIN da akai ma matata kuma kanwata ne, aka nemi b'ata ma Abba na suna shine nake neman izininka in shigar da k'ara"
     "Kana da shaidar da zaka bayyana ma kotu ne da zaka shigar da k'ara?" Sheikh ya tambaya yana mai kara zama.
      Zani ngado ya fitar ya ce "Abba  ga sheda ta, na dad'e ina 'kaurace ma Sumayya don gudun abin da zan iske, kalaman Zulai,Manniru sun hana ni aiwata komi har sai yanzu da Allah ya tashi wanke sumayya, Abba ni na fara saninta diya mace, ka gafarce ni Abba  ban so nayi rashin kunya ba".
     "Hahhhhh ai da ba'asan asalin angulu ba se ace daga ijib(wai Egypt zata ce) ya fad'o, yo budurwai nawa ke fitar da jini yanzu da jini ze zame maka sheda" Zulai ta fad'i tana mai zazzare idanu, da ka ganta kasan tabbas a tsorace take.
     "Ai tun daga likita ai se yai mana bayani ko Zulai" Sheikh ya karasa zancensa yana kallon Mahmud.
    "Eh toh Abba tabbas hakan ne, yanayin abincin da ake ci yanzu da yake cike da (chemicals) da shekarun da mata kan dauka kafin suyi aure da kuma jinin al'ada, duk wannan kan sa mace ta rasa yanar budurci ko kuma ya kasance mai rauni hakan zai sa bazata fitar da jini ba. Amma duk da haka hanyar zata kasance a matse,akwai budurcin da yake ba na asali ba, walau tasha wasu abubuwa ko aiki a asibiti ko tayi tsarki da wani abun, tabbas zata matse amma hanyar ba zai taba matsewa ba, (hattara dai )
    Na sumayya ko Allah zai iya taimakonta da Quwwansa da Qudiransa don ya wanke ta yasa tayi ambaliyan jini ma. Muna godiya muna kara gode masa" 
      "Kun ma raina ma kanku wayau, hala fim (film) kuke shooting"  Zulai ta fad'i tana mai juya idanu.
      "Abba in de Hamma ze shiga kotu akan rashin gaskiya Bismillah ni inada da shedu" fad'in Muhammad 
    "Wildun my boy (weldone my boy) fad'in Zulai tana dariya.
      "Yanda ya fadi nasa shedan anan kuma dole ku kawo na ku nan, ni kuma zanyi anfani da usul in yanke hukunci"
      Sumayya kallon Muhammad take cike da mamakinsa, "Wato har yanzu bai yarda da ita ba toh se yaushe"

'KAZAFI Where stories live. Discover now