...'Kazafi... ©Ummu Abdoul
(8)
Anyi auren Zulai da Abdurrahman cikin 'kan'kanin lokaci, da farko ta rike yaran da zuciya d'aya tare da yaranta. Ba tare da nuna bambanci ba Abdurrahman ya tura su makarantar kudi, mazan in sun dawo. Suke zuwa koyon kafintanci ko weilder.***********************
Lokaci ya shud'e, awanni sun zama kwanaki, yayinda kwanaki suka juye zuwa makwanni, makwanni suka zama watanni har shekaru suka zagayo.
Abdurrahman ya zama babban malamin addini inda majalisan da ya bud'e ya kara hab'b'aka, manyan mutane na zuwa daukan darasi.Zuri'an marigayiya Aysha sun taso inda Sumayya ke jami'a aji d'aya, yayinda Muhammad da Hamza ke aji hud'u a jamia, Ammar da Yasir na aji hudu a sakandari yayinda Suwaiba da Suwaida ke aji daya a secondary.
Naseer da Mahmud sun gama karatunsu, inda Mahmud ya fara aiki a babban asibitin jihar Bauchi kasancewanshi likita, Naseer shago ya bud'e babban shagon kafintanci kasancewarsa yana da ra'ayin kafa masana'antan aikin hannu.
In kai bak'o ne bazaka taba cewa ba Zulai ta haifi yaran gidan saboda rikon da tayi musu. Amma da zakai yini guda zaka fahimci wahalar da take basu.
Kullum fadan sheikh Abdurrahman bai wuce na rashin son karatun yaran zulai ba, babban namijin mai suna Manniru ya fara shaye shaye da kawar da kayan da ba nashi ba. Sheikh yayi iya yinsa don ganin ya dena abin ya faskara.
Ana cikin haka mannira ta fara tara samari, bokon ma ta dena zuwa, se taga dama. Idan sheikh yayi fadan zulai ta ce yana na yaranta sharri. Se de ya gani a tare dasu.
*********************
"Idan ance sannu a fara yi ma mannira sharri, dama. Annabi yace duk wanda yace d'an wani na abu toh ko shi ko nashi keyi, (inji karyan zulai fa) idan an taba mutum ya ce shi malami ne yasan Qurani da hadisi " Zulai ce tashigo falon,suna zaune suna kallon labaran duniya,ta dubi sheikh
"Audurrahman ka kalli bidiyon nan ka gani."
"Atoh Abba yakamata kasha kallo" Fadin Mannira tana mai girgiza kafa.
Gaba d'ayansu dake zaune basu tanka musu ba. Sheikh yayi shiru can kuma ya dubeta fuska daure "Me kenan hakan Zulaikha?" Ta ajiye cd kan tebur "Ai gani ya kori ji ko kuwa? Kai sanya idanuwansa su gane mishi." Ta fada tana kallon Manniru,da sauri Manniru ya dauka,nan da nan ya gyara saitin komai ya jona dvd kafin ya saka faifan.
Abinda idansu ya gano musu ko makiyinsu basa fatan su gani ciki."Ba yanda za'ayi tsarkakakke ya haifi mai yin zina ko ba haka kake cewaba, ina Sumayya tayi gadon zina kenan?" Zulai ta fadi tana mai (forwarding ) zuwa inda aka nuno Sumayya haihuwan uwarta da wani namiji suna aikata masha'a a halin turmi da tabarya.
Fad'uwar da Sheikh yayi ne,ya dawo dasu daga halin mutuwan zaune da suke. Nan ma Sumayya ta bi sawunshi. Zulai da yaranta sukai waje da gudunsu. Tsoronsu kada ya zamto mutuwa sukayi.
....'Kazafiii... ©Ummu Abdoul
(9)
Hankalin ahlin nan ya tashi ainun. Mazan suka kwashi Sumayya da sheikh sukai asibiti dasu. Masu hawaye nayi masu INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN nayi domin kuwa abun yazo musu tamkar saukan aradu.Mamaki ya cika ni ganin Muhammad ko gezau, asali ma ko binsu asibiti beyi ba. Dawowa yayi ya cire CD din ya kai d'akinsa ya adana. Sannan ya bi su Zulai d'akinsu.
Zawo ne kawai basuyi ba don suna tsaka da magana ya shigo. Amma da alama bai ji me suke fadi ba. Da fara'ansa ya karasa ciki ya zauna kan kujera.
"Mama Zulai Allah ne kawai ze biyaki domin kuwa kinyi jahadi."
"Hmmmm kai de mai sunan Baba, ni yanzu tsoro na ace nayi kisan kai, ina shiekhin?."
"Ko mutuwa yayi ai 'yarsa ce ta kashe shi, kin sa na tuna wakar da arna ke yi muna makaranta...
Zunubi tudu ne in ka hau naka se ka hangi na wani.""Hmmmmn wallahi ko, kasan kwanaki da Mannira ta yi wani shegen al'ada haka jini yai ta digan mata sheikh cewa yayi zubar da ciki tayi, wallahi har saki na yayi akai. Yanzu fa igiya daya ya rage mana "
"Kut.. Wallahi Mama Zulai ki lallaba, kin ga dai tashen kudi yake yanzu. Ki daiyi tunani kafin gobe sai musan abinyi, yanzu bara na koma kafin su isko ni nan."Yana kaiwa nan ya fice.
"Zulai kinga ikon Allah ko, ai na fada miki zasu yarda." cewar Mannira.
"Ungo nan!" Tayi mata dak'uwa.
"Kina ganin zai yarda damu akan 'yar uwarsa. Kinsan yafi kowa min rashin kunya"
"Amma Zulai kina ji yana baki espo, nufinshi fa ki gama da tsohon nan kamin ya sake ki, shima shegen kudi yake so." Fadin Manniru a cikin muryan sa na maye. Haka suka cigaba da tattaunawardu dai.
*******************
ASIBITI
(Accident and Emergency) aka kaisu na asibitin tarayya dake bauchi (FMC) likitoci sunyi kokari wajen kwato rayuwansu domin zukatansu suka tashi bugawa. Allah cikin ikonsa ya takaita.Kwanan Sumayya biyu ta dawo hayyacinta amma damuwa ne cike a ranta bazata taba manta hoton da ta gani a akwatin TV wai ita ce haihuwan uwarta. Ya subhanallah. (How, where and when) abinda tayi ta nanatawa kenan.
...'Kazafii.... ©UA
(10)
Satin sheikh biyu kafin aka sallame su suka koma gida, Sumayya ko sati bata cika ba aka sallame ta daga gadon asibiti amma tana ma'kale da abbanta.Ko da suka koma gida, yaci abinci yaranshi duka zagaye dashi se ya tsinci kanshi cikin farinciki. Inama inama mutuwa bata zama mai YANKAR KAUNA ba da Aisha na nan zaune kusa dashi.
Tun bayan aurensa da Aysha wacce ta kasance tsarkakka, nutsatsiya, bai taba samun digon abinda ze sa ya zargeta ba. Tana da rikon amana da kariya ga abinda ya mallaka tun ba ita kanta ba. Ta kaunace shi ta kula dashi ta tarbiyyantar da yaranshi.
Duk acikin yaran yafi son Sumayya. Kasancewa tafi sauran yaran kama da Aisha sannan kyawawan halayyarta da ri'ko da addini yasa yafi sonta.
Tana da shekara goma sha hudu (14) ta haddace kur'ani a 'kiraan hafsi da k'aloon. Ta haddace hadisai kamar su Bulugul maram, Sahihain, Umdatul ahkam da sauransu.
Ta kasance gwana a fiqhu, da Usulul fiqhu. Tayi karatuttuka da dama wanda mafi akasari ta haddace.
A iya saninsa Aisha tana kiyaye dokokin Allah, tuncdaga kan sutura har kamala. Meyasa zatai masa haka......
Hannun da yaji a fuskansa ya dawo dashi tunanin da yake. Sumayya ce ta share masa hawayen da ya gangaro masa kana ta zube guiwowinta a kasa alamun neman gafara sannan tace;
"Abba banda bakin da zan wanke kaina amma wallahi wallahi ban aikata ba, na kasa tuna yaushe hakan ya faru. A iya rayuwata hakan bai taba faruwa ba. Ka yafe min Abba na, fushinka ba karamin matsala bace a gare ni."
"Abba kayi hakuri ka yafe mata, Adda bazata taba aikata hakan ba". Cewan Ammar yana mai sheshek'a.
Shigowan Muhammad ya ankarar dasu rashinsa cikinsu. Kuma ganinsa tare da Zulai da yaranta yasa kowa ya bishi da ido.
YOU ARE READING
'KAZAFI
General FictionSau da yawa hotunan mu kan shiga kafofin sadarwa, tare da lbr mabambanta haɗe da hotunan wanda hakan kan iya zama Qaharu.