.... 'Kazafiii... 29
©Ummu Abdoul
Kai tsaye gidan Sheikh suka nufa babu haufi balle tsoro. Sun iske Nasir a gidan wanda shi ma bai dad'e da isa ba.
Kallonsu Sheikh ya tsaya yi, har saida su Shireen da Rufaida ( Yar wajen Mahmud) suka hau jikinshi suna jan gemunsa. Rungumesu yayi yana shi musu albarka kafin ya d'ago kai yana mai daure fuska ya dubi Mahmud
"Daga ina kuke Mahmud? Wato ban isa in hana ka hanu ba kenan?"
"Ka gafarce ni Abba ba haka nake nufi ba, ina so a sulhunta matsalar ne."
"Abba na yarda muje muyi DNA test din." Nasir ya katse Mahmud.
Bai musa ba ya amince musu su tafi suje suyi. Hannu Da Yawa Clinic suka je, wannan karon ma Dr Rufaida suka iske tare da Dr Yuseef da Dr Muttaka suna tattaunawa akan wani tiyata da sukayi. Batare da b'ata lokaci ba ta turasu wajen mai yin gwajin Haj Fatima.
Cigaban da aka samu yasa bai d'auki lokaci ba gwajin ya nuna. Kamar yanda Mahmud ya ke tsammani hakan ne. Yara dai na Nasir ne. Sujjada yayi yana gode ma Allah.
"Dan uwa nagode fa." Fadin Nasir yana murmushi.
"Mtswww a yau ba, ai duk mai daukar zancen fasiki yana mai tattare da NADAMA." Yana kaiwa nan ya kara gaba ya barshi tsaye da takarda a hannu.... 'Kazafiii 30
A mota kafin isowar Nasir lambar wayar Hannu Da Yawa Chamber ya kira, inda Barrister Jibril ya d'auka, ya fad'a masa zasu shigar da karar asibitin Healthy life ne, yana son lawyan da zai tsaya musu. Nan take yace su zo suyi abin cikin tsari akwai Barr Aysha Kura a 'kasa zata tsaya musu.
Bai ce ma Nasir komai ba ko da ya iso, sun fara tafiya Nasir ya rok'e shi da su je asibitin Healthy life. Batare da gardama ba suka d'au hanya.
Suna shirin shiga ofishin likitan suka jiyo murya cikin d'aga murya
"Mannira kin cuce ni wallahi, na miki aikin nan bayan kin biyani kika yaudare ni nayi zina dake, da ban duba kaina duk wata ta ya zansan ina dauke da cutar sida, Allah ya isa." Ya k'arasa muryarsa na rawa.
Bud'e ofishin da Nasir yayi yasa suka kallo 'kofar gaba d'aya.
Hanjin cikin likitan suka kad'a,cikin rashin nutsuwa yake magana
"Na tuba ku yafe min, wallahi hakk'inku bai barni ba ga shi ta sa min kanjamau na shafa ma mata na, ku yafe min."
Mannira kuwa tsoro ya hanata motsi, shak'o Dr da Nasir yayi yasa Mahmud saurin janyeshi suka bar ofishin. Fad'i yake "Su ga hukuncinsu nan daga Allah, saura mai yarda da maganarsu"
Banza yayi dashi. Ko da suka isa gida suka fad'a ma su Sheikh da Sumayya abinda ya faru kasancewar da yaran kawai aka tafi gwajin DNA din. Sosai Sheikh yayi musu wa'_azi akan daukar magana ba tare da bincike ba. Ya basu misalai da ayar dake cikib Suratul Hujrat da wasu hadisai da yayi magana akan hakan. Aka rabu ana farinciki
Ko da suka koma gida ba k'aramin daru aka sha ba kafin ya samu ya shawo kan Sumayyarshi.... 'Kazafiii...
KARSHE
Zamani ya shud'e inda darare suka juye zuwa makwanni, watanni suka zama shekaru..
Sheikh ne kwance yana fama da ciwon kai, sannu kake ji ta ko'ina kamar mai babban jinya.
Budurwar da ta shigo tana waya ne ta dauki hankalinsu, fad'i take "Ke fa rufyn nan shegen son girma ne da ke, wata nawa kika ban,ki zo ga ni wajen Sheikh Abba." Gaida iyayenta da me zaune tayi kafin ta karasa wajen Sheikh.
"Dr Shireen takwarar indo na." Ya fadi yana mika mata hannu suyi sallama.
"Allah ja zamaninka, Uba Nagari" Ta fad'i tana rik'e hannunsa da kyau.
Hira sukeyi sosai har iyayen maza suka shigo. Nayi mamakin ganin Rooney ya shigo tare da yayansa Bilal, bayan dan hira Mahmud yace "Ku shirya yau ne fa ranar ziyara, zamu gidan yari da asibiti."
"Dady Ubaidullah motarka zan shiga, kuma Rufaida bata iso ba." Fad'in Shireen don shak'uwar da ke tsakaninta da Rooney.
"Mijina ba direban ko d'ayanku bane" fad'in Suwaiba cikin wasa.
"Rabu da ita kinji dota, zamu jiraku, kishi antynki take" Cewar Suwaida, tana goya jaririnta yayinda Bilal ke gyara mata zanin.
Hamdala Sheikh keyi, in ba Allah ba wa zai baka ya shirya maka, yaransa suna zaune lafiya a gidajen aurensu.*************
Kud'in da Sahal ya mik'a ma wani d'an gidan yarin ya jawo hankalin ganduroban. "Kai wa yace ana musu kyauta?"
"Wannan uwarsa ya kashe yake nan yana jira a sa masa ranar da za'a kashe shi ne" Nan suka waigo suga wannan
"Manniru!!!" Suka fad'i a kusan tare.
Kunya yasa ya tsere,su ma jiki a sanyaye suka fito suka je asibitin garin Bauchi. Sun zazzagaya d'aki-d'aki.
Wari ya ziyarce su daga d'akin da suke shirin shiga. Hakan suka daure suka shiga. Wata baiwar Allah ce tayi bayan gida jikinta duk ya baci.
Sumayya uwar tausayi ta karasa kusa tana mata sannu.
Mannira ta d'ago ta dubeta,ko kusa bata mance mai wannan fuskar ba,a sanyaye tace
"Sumayya! Kece kuwa, Don Allah ki yafe min kar in mutu da hakkinku."
Sai lokacin suka ganeta,duk ta rame tamkar wata kwarangal haka ta koma. Kai duniya ba komai bace!
"Mun yafe miki Mannira" fad'in Sumayy tana mai barin wajen cikin sauri sakamakon wani sabon bayan gida da Mannira ta saki (da nima warin yasa na gagara typing...lol)Anan zance muguntar mai mugunta zaivkashe shi..
Naso yafi haka yawa,don na tsallake wajaje da dama kamar rayuwar Zulai bayan barin Sheikh, haduwar Mannira da Dr,kwayoyin da Dr Rufaida tace Sumayya tana sha ya akayi Manniru ya kashe Zulai..Da wasu da dama.Duk wanda na 6ata mawa ya/ta yafe min.
Ummu Abdoul ke muku fatan Alkhairi
Mu haɗe a makarantar Malam Lami mu ji irin karatun sa. Love you all
YOU ARE READING
'KAZAFI
General FictionSau da yawa hotunan mu kan shiga kafofin sadarwa, tare da lbr mabambanta haɗe da hotunan wanda hakan kan iya zama Qaharu.