......'Kazafi(03)... ©Ummu Abdoul
Fitan Mahmud keda wuya ya tashi ya lek'a masu masu aiki. Shago zan kira wajen ko karamar kamfani ko masana'anta.
Aikin kafinta akeyi a wajen kama daga kujeran taya ni gulma har zuwaga manyan gadaje da kujeru kamar an shigo dashi daga daga kasashen waje. In banyi k'arya ba zan iya cewa nashi yafi k'arko da aminci.
Rashin samun tallafin manyan k'asan yasa harkan kafintanci ya dak'ushe a Nijeriya, sun gwammace su siyo na miliyoyin kud'i ko bazaiyi k'arko ba,bayan ga masana masuyin aiki da k'arfinsu tsakani da Allah a kusa dasu. Kuma mafi yawan katakon da suke amfani dashi daga Nigeria da wasu kasashen Afrika ake kai musu.
Anan nake kira ga masu kudi da shuwagabanninmu da su tallafa ma harkan kafintanci domin cigaban k'asarmu. Sannan a k'ara inganta harkan shuka bishiyoyi (tree crop production) da kuma timber production, domin sammun ingantaccen katakai. (Ko ni Baba Buhari ya ba ministern kula da bishiyoyi da katakai ai yayi ko makaranta 😜).
***"Assalamu Alaikum" fadin wasu 'yan mata yayin da suke shiga gidan.
"Waalaikumus salam wa rahmatullah"
"Twins kune da maraicen nan?" Fadin matashiyar matar tana mai fara'a.
"Wallahi ko sis, daga makaranta muke mukace mu biyo mu ganki." Fadin guda daga cikinsu.
Hira sukayi sosai wanda mafi akasarin hiran akan matsalolinta ne, su kuma suna bata hakuri tare da karanto mata muhimmancin hakurin.
Sai gab da magrib suka tafi, ta koma dakinta ta ja kofar kamar kullum.
YOU ARE READING
'KAZAFI
General FictionSau da yawa hotunan mu kan shiga kafofin sadarwa, tare da lbr mabambanta haɗe da hotunan wanda hakan kan iya zama Qaharu.