Goma

954 114 19
                                    

... 'Kazafii... 23
©Ummu Abdoul
   Garin kwashe-kwashensa ya had'u da Mannira, kyawun ta ya daukar masa hankali ba shi ya samu nutsuwa ba har saida ya kaishi da  kaita gadonshi.
    Bayan ta fahimci yanda ya gwanance a harkan na'ura mai kwa-kwalwa, ne ta sako masa zancen Sumayya, ba tare da bata lokaci ba ya had'a faifan bidiyon amma zuciyarsa ta gagara amince masa da ya siyar da fuskan Sumayya a duniya.
    Sati biyu bayan yayi aikin da Mannira ta sa shi, ya had'u da Muhammad. Had'uwan farko hankalinsa ya kwanta dashi yaji ai yasami aminin da ya dad'e yana mafarkin samu.
    Cikin sati guda gaba d'aya 'yan gidansu Roneey sun san Muhammad kuma nutsuwarsa yasa Dr Zahida ta amince dashi.
     Muhammad bai tab'a kyamatarsa ba har ya samu ya gano duk abinda yake nema, abu d'aya yayi bai taba yarda sun had'u da Mannira ba.
    Ranar da ya amshi fayafayen bidiyo da hotunan da ya harhad'a na Sumayya ya zaunar da Rooney yace
    "Ubaidullah kana tunanin mutuwarka kuwa? Kana tunanin kwanciyar kabarin nan kuwa? Ina zaka kai dukiya fisabilillahi naga kana mutuwa da kyallen yadi 'yar (#70) za'a kaika toh me zakayi da kud'i?"
    "Kai amini kudi sune rayuwa."
    "A'a ni ba amininka bane, kana aikin 'yan wuta ni kuma ina iya kokarin tsare kaina daga wuta, ina amintar mu anan?
      Ni na gwammace nayi bara a duniya kai kuma kanason bara a kufai bara inda babu wanda zai jika" (Gaisuwa ga Aminu ALA, ni ba mai jin wakokinsa bace, ranar da naji BARA A KUFAI a napep nayi hawaye na k'aru a imani, ina maka da dukkanin musulmi fatan kariya daga bara a kufai)
    Shiru Rooney yayi. Hakan yasa Muhammad ya cigaba
     "Kasan hukuncin kallon films din batsa ko karatun batsa? Kamar fa zina ce da ido, kuma ranar lahira idanuwanka zasu bada shaidan abinda suka gani.
     Kai baka tsaya a kallo ba,saika yad'a ma duniya kasan kuwa duk wanda ya kalla a sanadinka kana da zunubi kwatankwacin nasa. Haka zalika wanda yayi rubutun batsa.
     Duk wannan bai ishe ka ba saika kwashi hotunan kannin mutane, 'ya'yan mutane da iyayen mutane da basu ji basu gani ba ka na watsa ma duniya da sunan batsa, anji sunyi zunubin sanyawa a media kai kuma fa, ina zaka gansu ka nemi gafara, ina zaka kai zunuban nan?
     Duk fa sai an maka hisabi dasu. Ina zaka gansu Rooney?
    Kud'in da ka tara me zakace ma Allah a kansu, jiya Bank statement dinka ya nuna $9b ina zaka kai? Ta ya zaka fara shaidan sisi da sule a gaban Allah?
     Zan tayaka neman gafaran Sumayya da Mannira ta baka kwangila duk da kun hana mata zaman aure cikin kwanciyar hankali. Na barka lafiya" yana kaiwa nan ya fice ya barshi.

.... 'Kazafiii... 24
©Ummu Abdoul
    'Dago fuskarsa yayi da ke jik'e da ruwan hawaye, na'urar da ke d'akin ya kunna, da yake gwani ne cikin mintuna ashirin ya gama had'a (virus), ya had'a ta da (site) dinsa akan mutum na shiga gaba d'aya wayar sa ko kwamfutarsa zata dauke kuma gyarata zaiyi wuya.
    Jiki babu laka ya tashi ya gangara gidansu. Bai ga nisan hanyar ba, tafiya yake zantuttukan Muhammad na masa yawo a kwakwalwa, haka har ya isa gida.
    A harabar gidan ya iske Miminsa ta rako baffansu zai fita.
    "Rooney lafiya kake tafe a k'afa, multi billionaire bachelor da tafiya a 'kafa. (You are not meant to suffer son)" Ya fad'i yana mai d'aure fuska.
    Dr Zahida kam kallonsu take cikin halin tausayawa domin tausayinsu takeyi ganin yanda suka dauki rayuwa.
     "Baffa gara na wahala yanzu da nayi ta 'kiyama, baka taba tambayar silar arziki na ba, yau Muhammad ya taimaka min, banda aminin da yafi minshi" Ya fad'i yana mai fashewa da kuka sosai.
   Fitan da baiyi ba kenan, zama sukai gaba d'aya ya maida musu abinda ya faru. Gaba d'aya iyayen sun girgiza da halin d'ansu. Nan take Baffansa yayi nadama don a cewarsa shi ya kaishi ga halaka.

*************************
   Rayuwa mai cike da 'kaunar juna ke wanzuwa tsakanin Sumayya da Nasir. Ko minti biyar (5) kayi a gidan zaka fahimci soyayyar da ke tsakaninsu.
    Wata uku bayan bayyanar gaskiyar, ciki ya bayyana a tare da Sumayya. Kula da soyayya sai abunda yayi gaba.
     Watarana suna zaune a falo, cikinta na da wata bakwai, Hamma Nasir na mata tausa, ta na rike da madarar Habib da ya zame mata abinsha akayi sallama.
    Wacce ta shigo bayan amsawar sallamar ce ta basu mamaki, Mannira ce jina jina da ita ta kod'e kamar wacce tayi jinya, tun bayan rabuwarsu basu k'ara sanyata a ido ba sai yau.
     Bayan sun gaisa ta fara rok'onsu gafara tana mai zubar da hawaye a cewarta ta tuba su yafe mata.
     Nan da nan zuciyar Sumayya ta amince da ita, ta ce "Haba Mannira akai ma Allah laifi Ya yafe balle kuma mutum? Ni godiya zan miki ma,da bakiyimin hakan ba yaushe Hamma'am zaiyi tunanin aurena? Kuma kinga ba macen da ta kaini  dacen mijin aure." Ta k'arasa tana sumbatar tsakiyar kansa.
     Gimtse fuska ya sakeyi ya tashi ya wuce d'aki batare da ce ma Mannira komi ba

... 'Kazafii... 25
© Ummu Abdoul
     Binshi d'aki tayi ta rok'eshi tana mai nuna masa muhimmancin yafiya tsakanin al'ummar musulmi don Allah nason mai yafiya.
    Saida Mannira tayi sati biyu (2) sannan ta koma da alk'awarin zata dawo bayan haihuwar Sumayya.
   Cikin ikon Allah Sumayya ta haihu lafiya inda aka sami 'ya mace, murna sosai 'yan uwa da abokan arziki sukayi. Ranar suna yarinya taci suna Aisha inda ake ce mata Shireen.
    Shireen nada shekara (3) Sumayya ta haifi Abdurrahman da suke kira da Sahal. Soyayya da gata babu wanda bata samu daga Hamma Nasir ba.

Ta kammala karatunta don kanta tace bata bu'katar aiki.
      Tun bayan haihuwar Sahal take fama da 6ari, da ciki ya kai wata (4-5) zai zube, sunje asibiti likitanta da yake dubata tun haihuwar Shireen ya tabbatar da lafiyarta.
    Kwananta goma da wani 6arin suna zaune sai ga kiran likita akan yana son ganinsu a asibiti. Ba tare da b'ata lokaci ba sika tafi. Sun iske shi zaune a ofis yana mai jiransu.
   "Ka yafemin d'an uwa bazan iya cigaba da 6oye maka ba." Likitan ya fad'i yana mai sheshek'a.
    "Talk please Doctor!" Nasir ya fad'i cikin k'aguwa
    "Wallahi zancen matarka da yaran nan ne" Yaja majina yana mai share hawaye da hankici
   "Me ya same su?" Nasir  ya fad'i cikin tsawa
     "Ka yafemin, daman zan fad'a maka cikin nan da ke fita Madam da saurayinta ke zuwa a cire"
   "What!!! Kana hauka ne?" Nasir ya fad'i yana mai cakumo wuyan rigarsa.
    "Wallahi iyakar gaskiyar kenan ga ta nan ka tambayeta ko kuje a duba mahaifanta ya kusa samun matsala ma, ko yaran can ba cikinka bane." Yana maganar fuskarsa na nuna hakikanin gaskiyarsa muraran. 
     Bai ce komi ba, yaja hannun Sumayya sai Hannu da Yawa clinic inda suka iske Gynea Rufaida. Batayi wata wata ba ta tura su inda ake hoto suka yo.
     Ko da ta duba sakamakon rai a bace tace "Kuna da hankali kuwa take shan mugayen kwayoyin nan? Idan bakwa son haihuwa ga tsarin iyali kuyi mana. Yanzu dai dole kuyi hakuri kada komi ya shiga mahaifan har sai ta gama shan magungunan nan" Ta fad'i tana rubuta musu magunguna.
   Sumayya hankalinta idan yayi dubu toh ya tashi,kuka takeyi kawai kamar wacce aka aikowa sak'on mutuwa. Nasir bai ko kallon inda take.

  Daga asibiti basu tsaya ko ina ba sai gidan Sheikh wanda yake auran, k'anwa take ga mahaifansu Nasir. Har garin D'ifa aka je aka d'aura aure, bazawara ce amma bata tab'a haihuwa ba, hakan yasa ta rungumi yaran a matsayin nata.
    Bayan sun isa, Nasir yayi ma Sheikh bayanin abinda ya faru daga farko har karshe. Bud'ar bakinsa cewa yayi "Zata aikata fin haka, ku tashi ku bani wuri." 
    Banda salati babu abunda Sumayya keyi,wai wannan wace irin rayuwa ce? Wannan ma wani sabon Kazafin ne ko kuwa dai? Ya Salam.
      Tunda suka koma gida ya umarceta da zaman d'akin bak'i. Ya gagara sakinta don wani sashi na zuciyarsa ya kasa yarda. Sheikh ya hana sauran yaran daukan mataki akan abin.

***** kuyi hkr zanyi a takaice domin zanyi tafiya ranar alhamis, zan so in kammala kafin nan.

'KAZAFI Where stories live. Discover now