Shida

1K 149 22
                                    

....'Kazafi... ©Safiyyah Ummu Abdoul
          (11)
Zama yayi yana wani daure fuska, daukan waya yayi yana danne danne, take wayan shekhi yayi kara, karantawa yayi yana mai murmushi da aje wayar..

"Assalamu Alaikum wa rahmatullah." Sallamar sheikh ya dawo da masu tunani daga duniyar tunaninsu. 
Tare suka amsa sallaman suna masu natsuwa da mika Masa hankalinsu. 
  "Abinda yasa na tara mu anan ba komi bane face inyi fashin ba'ki akan mummunan abinda ya faru da ahlin gidanan sati biyu (2) da suka wuce.
     Nayi ba'kinciki sosai akan wannan bawai don na yarda ba sai don b'ata ma Sumayya suna da akayi. Tabbas ka haifi d'a baka haifi halinsa ba, amma tunda nake ban tab'a zina ba kuma na tabbata Allah da rahmanSa ze kare yara na musammman matan daga aikata zina...." Kuka ya saki mai tsuma rai domin bidiyon ya dawo masa sabo dal ne a idonsa.
     Yaransa suka karaso suna rungume shi. Kowa so yake ya share hawayen ubansu abin soyuwa agaresu. Gyaran murya yayi kana ya cigaba.
     "Zulai ina kika samo wannan video din?" Ya karasa zancen yana kallon zulai. 
   Ta hau daure fuska
      "Ai nasan ba yarda  zakayi ba, ciki nawa sumayya ta zubar da zaka lauye ni nan. Bidiyo de ya shiga duniya ehe, an de ji kunya".
    "Kar ki fara masa rashin kunya fa, don wallahi akanshi se in miki dan banzan duka." Fadin Hamza yana mai mikewa a fusace.
       "Toh rasa kunya, ita ta sa kanwar ka tayi abin kunya?" Ya kai ma Sumayya shuri tai maza ta kauce. Sannan ya cigaba "Wallahi duk wanda yace ze taba min matar uba gidannan se anyi rigima. An dad'e ana tauye hakkinmu akan sumayya."
      Nan fa rigima ta kaure tsakanin 'yan biyun da ba'a taba jin tsakaninsu ba. Sai da sheikhi ya tsawatar musu sannan sukai shiru. Farincikin Zulai baze misaltu ba, hatta su Manniru da ke d'an shakku akansa sun fahimci shi d'in nasu ne.
       "Abba ina da magana" Nasir ya katse shirun da ya biyo baya. 
     "Bismillah"
      "Abba na gurfano a gabanka ina neman auren kanwata Sumayya, Abba ka taimaka ka yarda ka sanya albarkanka a ciki insha Allah zaka kasance mai farinciki da wannan had'in "
      "Tabbas wannan ne kawai (solution) Abba, sai ayi rana daya da nawa kawai" fadin Mahmud kenan cikin farinciki. 
   Tun da aka fara rigiman nan suka rasa mafita da zasu sanya Abbansu farinciki. Mahmud ya fara kawo shawaran amma fir Nasiru yak'i yarda don wani sashi na zuciyanshi na zargin smSumayya. Fadi yake "Ta ya za'a ganta tana aikata abu muraran, don son zuciyanku kuce ba tayi ba.Video ne fa ba hoto ba."Duk yanda Mahmud yaso ya fahimtar da shi yaki yarda ya fahimta duk a cewansa ai yaga zahir

...'Kazafii... ©Ummu Abdoul
         (12)
     Kowa awajen yai mamaki kuma yai farinciki da wannan kalami na Nasir. Idan aka d'ebe Zulai da yaranta.
      "Mtsww aikin banza to aurenta ne zaisa ace bata san namiji ba?"  Kalaman Zulai kenan ta kara gaba, ba gardama yaranta da Muhammad suka bita a baya.
     Sumayya jin wani sonsa na taso mata tundaga tafin kafanta har zuwa kwanyanta. Bugun zuciyanta ya 'karu don ko a mafarki Hamma Nasir irin mijin da take gani ne. Miskili ne maras son magana, hakan bai hana mutum ganin yalwataccen fara'a kwance a fuskansa. Mutum ne shi mai kyauta, baya kyashin sadaukar da sisinsa na karshe ga mabu'kaci. Ga yawan ibada da bin dokokin Allah. Hawayen farinciki ne ya gangaro daga idonta. 
     "Nasiru ka tabbata har cikin zuciyarka ne wannan za'bin?." Kalaman mahaifinta suka dawo da ita duniyar tunani.
      "Eh Abba, albarka kawai zaka sa mana."
       "Allah muku albarka Ya baku zuri'a dayyaba."

*********************

Biki nata matsowa. Shirye shirye ake ba kama hannun yaro,Nasir ya kammala gininshi da ke unguwar Nasarawa Jahun. Gini ne wadatacce wanda ya kunshi dakuna uku duk da bandaki a cikinsu da falo wanda a gefensa akwai bandaki shima, se sashin baki da keda daki daya da bayinta a ciki. Daga gefen hagu kuma 'yar baranda ce (passage) da zai sada ka da kitchen da store. Harabar gidan kuwa furanni ne zagaye kasancewanshi mutum mai son yab'anya zagaye dashi.
    Abinda ke damun Sumayya rashin samun kalmar SO daga Hammanta, ba yabo ba fallasa za'a zauna ayi hira kamar da, daidai da rana d'aya bai taba kiranta don su shirya wani abun dangane da rayuwan da zasu yi tare ba. Kodai ze aureta ne don rufa ma mahaifinta asiri? Tunaninta kenan kullum wanda hakan ke jefa ta cikin damuwa...
      Zaune suke ita da Hamma Nasir da ya aika kiranta. Sun gaisa kenan se ga Manniru ya taho yana layi
      "Baaba na fada maka ka dena daga mana kai, abinda sauran su Jackson zaka kwasa, wane irin bomb ne bamu shuka da ita ba, zaku wani zo ku zauna nan wai zance, mtswwww."
      Dafe kansa yayi, ba don baya son bacin ran Abba ba da ba abinda ze hana shi fasa auren nan. Shi mutum ne mai tsananin kishi,duk sadda kuwa suka hadu sai ya gasa masa magana. Shekaranjiya haka ya watso masa wasu hotuna, duk nata ne da wasu mazan. Bakinciki yasa ya gagara kwashewa har Muhammad yazo ya gansu. Kalaman Muhammad ya tuna inda yace "Hamma Naseer kabi zuciyarka kar ka cutar da kanka"

...'Kazafii.. 13 ©Ummu Abdoul
   
   Shiru yayi yana kallon Muhammad, "Allah hamma (follow ur mind)" yana kaiwa nan ya fice daga d'akin.
  "Hamma'am"
Muryan Sumayya ya dawo dashi daga duniyar tunani. Hawaye ne kwance a kuncinta, tsareta yayi da jajayen idanunsa da suka rine sukai jajir don ba'kinciki.
    "Tashi ki koma ciki" abinda ya iya fadi kenan. Zuciyanshi na tausa, da za'a gwada jininshi tabbas da zaa iske ya hau. Alwala kawai yayi ya shige masallacin gidan ya fara sallah yana mika kukanshi ga Allah.
    Tashin da tayi d'aki ta shiga tana kuka mai tsuma ran mai sauraro, turo kofan da akayi yasa ta d'ago idanunta da suka kumbura suka rine zuwa kalan jaa. Yayanta ne Muhammad mai sonta a da, tunda abinnan ya faru ko kallo bata isheshi ba.
    A tarihin rayuwanta ta San ba Wanda ya so ta in aka cire abbanta sama da Muhammad. Shine abokinta itace aminiyarsa. Kaifin Basiransa da wayon sa yasa take kiransa da SSS, kuma ita ta chusa masa raayin zama hakan. 
    Duk yanda ka kai ga wayau ko dabara wajen boye laifi kallo d'aya Muhammad ze maka ya gano baka da gaskiya.
     Tashi tayi da saurinsa ta fad'a kirjinsa tana sabon kuka, bayanta yake shafara alamun lallashi. Ya juya ya tura kofan d'akin yana mai rungume da ita.
   "Bro ka yarda na aikata laifin nan har ka guje ni, ta ya ka kasa gano masu laifi wannan karan? ta ya ka ki yarda da aminiyarka wannan karon?" Duk ta had'o masa tambayoyin nan.
      Zaunar da ita yayi gefen gado kafin yace cikin d'aga murya "Saboda kin chanza daga sumayyan da na sani, saboda kin ci amanar marigayiya da ta kasance mafi Alkhairi a cikin uwaye why sumayya?"
      Wani sabon kuka ta saki, rungumarta yayi da kyau a jikinta yana mata magana da ni kaina banji ba, fuskan nan nasa a daure. Kallonsa Sumayya take kamar ranar ta fara ganinsa. Yanayinta zance kamar wacce ta hango tsira a lokacin da ta cire rai ga samu. 
     Daga idon da zanyi Zulai na hango labe a jikin taga farinciki fal a zuciyarta


'KAZAFI Where stories live. Discover now