NI DA ANAM

1.2K 72 0
                                    

*NI DA ANAM* 
_(Matsalar rayuwa)_

💞🌟💞  

💞🌟💞

✍🏼 _Rubutawa:_

       
*QUEEN MERMUE*

_Tare da:_
         🤴🏻
*KING BOY ISAH*

BABI NA DAYA (15)

*
📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

*Abuja*

Da isar su Abujan a gajiye suka isa gidan yayin da ko a jirgi Minal baccin ta tayi haka a motar sai da suka iso ya tashe ta,
"Ki tashi fa mun karaso"
Bude idanun ta cike da shagwaba ta kara makale hannun sa tana mika,
"Uhm! Baby ka dauke mana, wallahi na gaji gashi kuma kafa na yayi ciwo nifa yunwa ma nake ji dauki ya hanani naci abinci"
Surutun da take zubawa kenan har ya karasa da ita acikin falon gidan ya sauke ta, bai tsaya bi takanta ba ya wuce sama ya barta anan falon kasa tana ta zuba.
Mamaki Minal da shegen surutun ta yake ita bata damu ka tanka mata ba hasalima ko labari tafi so ta bayar da abata.
Minal yarinya ce kyakkyawa fara tas tsayin ta dai-dai gwargwado, bata da wani cikar sura tafi kyau a kira ta da siririya, tsabar kyaun fuska kamar ita ta zana kan ta, doguwar fuska ce mai dauke da dan karamin bakin ta sai hakora talatin da biyu a ciki jerarru farare tas, hancin ta mai dan tudu ne ya taso ta karshen sa hakan ya kara fidda idanuwan ta masu matsakaicin girma dauke da zarazaran gira, ba tada goshi mai girma haka kan ta dauke yake da dumbujejen gashi mai mugun tsawo duk da bashi da cika da yawa amma akwai tsawo kam. Ta gefen halaye kuma yar rigima ce ga son mutane amma akwai zuba karya dama ance duk wanda ya cika surutu to da wuya baka same shi da yawan zuba karya ba, muguwar sauna ce ga tsabar son jiki hakan ya hadu da gata da hutu sai ya haddasa mata rashin son aiki ko kadan, mace ce da misali ace kina gidan sama tana falon kasa tana iya kwala miki kira har sai kin sauko tace ki miko mata remote a kujerar da ke kusa da ita.
Indai gefen gayu da bugun mota ne ba'a barta a baya ba, saka sutura kamar yar fashon, akwai kashin kudi dan cin dadi dayawo a gari ana tsala gudu akan titi kamar yar tseren mota. Akwai son soyayyar baki a zauna a kashe dare ana charting amma yarinya ce da bata kaunar a taba jikin ta bale akai da aikata akai-akai da ita, in banda wannan da tuni ta gama zama tantiriyar kwarai saidai son jikin ta ya ceceta.

Tun tana karama ake kiran ta da Matar Anam hakan yasa ta kamo da son shi har tasowar shi, Mahaifiyar Anam itace take kiran Minal da surika tun tana jaririya shiyasa Mahaifiyar Minal ta yi alkawarin bashi ita muddin yace yana so, yanzu kuma wannan dalilin bai hana ta yarda aka bashi Minal ba a ganin su idan yasan dadin mata zai daina duk wata muguwar dabi'a duk da har yanzu basu aminta da yana aikata abinda Mahaifin su ya tabbatar musu da shi ba.
Wanka ya shiga ya fito ya shirya cikin farar  jallabiya mai guntun hannu ya sakko kasa dan tafiya Masallacin da yake kusa da gidan.
Tana nan inda ya barta  kwance rabin jikin ta akan kujera rabi a kasa.
A hankali ya iso wajen ta yara bubbuga kafafun ta.
"Minal!"
Murmushi ta sakar masa lokacin da take kokarin bude idanuwan ta,
"ki tashi kiyi wanka kiyi sallar magrib an kusa yin isha."
"tohm, na tashi ashe ma anyi salla ni mafarki ma nakeyi wallahi inda ma ace dogon bacci ne da zaifi dadi..."
Har ta karasa sama tana bada labarin mafarkin da tayi.
Bai dawo gidan ba sai da akayi isha, karfe tara ya shigo falon tana zaune sai raba idanu take yi ta takure a gefen kujera takai volume karshe harda yan matan hawayen ta. Tana hango shi ta rugo aguje ta rungumesa tana hawaye,
"Ya wallahi tsoro nake ji kuma yunwa nake ji dan Allah kada ka fita. Yana kokarin janye ta tana kara makalkale masa yayin da yake jin tsigar jikin sa tana tashi, abinda baya so ya fara bijiro masa da kyar ya ajiyeta akan kujera yana cewa.
"ah Minal sake ni mana abinci fa na je na siyo mana, kinyi salla ko?"
Daga kan tayi tare da tallafo ledar da ya ajiye a kasa,
"jeki kitchen ki dakko mana Filet,"
Ai fa jan aiki kenan! Tunzure baki tayi tace,
"tsoro fa nake ji wannan gidan akwilai duhuwa kuma ace mutum daya aciki ai aljanun sun sami aboki ni kam wallahi bazan iya tafiya ba,"
Murmushi yayi ya mike tsaye dama yasan koba tsoro abu mai wuya ne ta iya tafiyar.
Dauke da filet biyu da kofuna biyu ya dawo dayake shi ba gwani bane wajen cin abinci da cokali ba.

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now