NI DA ANAM

2K 82 1
                                    

*NI DA ANAM* 
_(Matsalar rayuwa)_

💞🌟💞  

💞🌟💞

✍🏼 _Rubutawa:_

       
*QUEEN MERMUE*

BABI NA GOMA SHA TAKWAS(18)

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

_​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook_​​
_Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION_
_📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​_
_Zamaniwriterassociation@gmail.com_

*ⓂⓂAsma Gwamnati, karki damu ana mugun tare🤝🏽Allah ya kara Basira.ⓂⓂ*

Kiciniyar kwace kan ta takeyi sai dai ba rik'on wasa yayi mata ba.
"Sir dan Allah..."
"baki da tarbiya ko? Ko kuma tsabar karuwancin ne yasa kike zama tsirara a gidan da ba naki ba? Indai dan wannan ne"
Ya fada tare da kai bakin sa akan nipple din ta ya dan ciza, "babu abin da zai sa naji, kin riga da kin gama sanin maza ko? To bari kiji, ni ba Aliyu bane babu wani abu a jikin ki da matata tarasa bale har nayi sha'awar shi, munafukar banza."
Idan akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce a zagi Aliyu ba.
Wani irin zafi zuciyar take mata, ji take kamar ta ingiza shi acikin wuta. Cikin taurin rai tace,
"Ni ba Karuwa bace, Ya Aliyu na kuma ba dan iska bane dan baya shaye-sahye, ko karuwanci zanyi wallahi ba zanyi da gay..."
Bata karasa ba cikin mugunta ya kara mird'e hannun ta tare da kama lebunan ta ya cije su sosai har saida ta fasa k'ara.
"gobe ki k'ara yimin rashin mutunci kiga yanda zan illataki."
"anyi maka! Mugu kawai, Allah ya isa na."
Da karfi ya turata akan gado ya haye ta, duka nauyinsa ya sakar mata tare da had'e bakin sa da nata cikin salon mugun ta har sai da yaga numfashin ta yana neman d'aukewa.
Da kyar ya iya janye jikin sa ya mik'e,
"wallahi sai na nuna miki iya mugun ta muddin kika kara kirana da mugu."
Da sauri ya fita d'akin ya barta anan tana kukan bak'in ciki.
Toilet ya fad'a ya sakarwa kan shi ruwan sanyi, tun ranar farko da ya had'a bakin sa da nata acan garin Lagos lokacin da yake a buge, tun a lokacin yake burin kara haduwa da lallausan lebenan ta.
Da kyar ya iya saita kansa ya fito daga bayin.
Cikin lemon green shadda ya shirya ya murza hula bak'a da takalma bakak'e. Sauri yake ya isa gidan jin yadda cikin sa yake neman agaji.

Sai da ya biya Daleel super market ya siye kayan shafa da sark'a mai d'an karen kyau kafin ya wuce gidan su.
A falon farko ya tarar da Sareena da Mulikat, da gudu Sareena ta zo kan shi tare da huggin din shi, Mulikat kuwa sannu da zuwa ta shiga yi masa yayin da Sareena ta wani mak'ale shi sai faman hankada ta yake.
"Hammana..."
"meye haka wai?"
Ya katse mata maganar.mamaki ta shiga yi ita da bokan Mummy yace da ya dawo da rawar jiki zai zo a gareta amma shi yake mata tsawa.
"ina Mummy?"
Ya tambayi Mulikat da ta maida hankalin akan wayar ta.
"tana d'akin Daddy."
Bai ko kalli Sareena dake faman kad'a kafa ba ya haura sama.
"aikin banza, wahalalliya."
Inji Mulikat yayin da ta mik'e tsaye, aikuwa Sareena kamar jiran ta takeyi ta fara kumfar baki.
"wallhi zan ci ubanki! Ni sa'arki ce shegiya munafika? Yar bak'in ciki."
Mulikat ta juyo gareta ai da sauri ta mike ta haye sama tana zaginta.
Yar buhu duk da itace Yayar Mulikat amma mugun tsoron ta takeyi da bazaiyi mata wuya ba ta hada mata na jaki, dan ita Mulikat bata shiga harkan su.
Yayi matuk'ar jin dad'i ganin yanda Daddy ya karbesa, sunyi hira sosai wadda bazai tuna rana ta karshe da hakan ya kasance tsakanin su ba.
Hajiya Ladi kuwa, yak'en dole ta ci gaba da yi har saida ta keb'e da shi a d'aki.
Cikin kulawa tace,
"My Son, ina amaryar? Me yasa baka zo da ita ba?"
Murmushi yayi ya shafa kan sa yace.
"Mummy ta fara fita aiki ne a companyn Abba, shi yasa bamu zo tare ba dan wannan ne satin ta na farko."
"Ohk."
Inji Mummy Ladi kana ta koma cewa,
"ya naga baka walwala irin ta angwaye? Anya kun sadu kuwa?"
Kunya yaji ta rufe shi duk da babu kunya tsakanin sa da Mummy dan haka yace.
"kai Mummy, munyi mana..."
"sau nawa? Anya yaron nan nawa bai fara k'arya ba?kasan bakada kamata a fad'in duniyar nan, gwara ka fadamun gaskiyar lamarin sai musan abin yi."
Shiru yayi na dan wani lokaci kana yace.
"hakane Mummy, ni sau d'aya ne, daga lokacin kuma idan nazo kusantar ta sai ta hanani, ni kuma sai naji bana iya forcing kai na."
Hamdala Mummy Ladi tayi, acikin zuciyar ta kuwa ashar take zugawa kamar yadda boka ga umurce tayi, muddin aikin sa yayi tasiri to sai tayi ashar sau bakwai.
Cikin tsananin damuwa tace,
"haba gaske dai. My Son abinda nake so da kai shine.
Kadaina shan giyar da kakeyi da sigarin, idan ka daina nida kai na zan fahimtar da Daddyn ka, yanzu ma da kaga yana maka fara' a sai da nace masa har asibiti sai da aka kai Minal ranar farkon ku."
"Mummy ai na daina shan sigarin, giyar ma sau d'aya tak nasha ta bayan auren, wallahi na daina."
Ko kad'an bataji dadin wannan kalamin ba, amma dai haka ta daure ta shiga yi masa nasiha, wanda rabin nasihar duk zuga ce.

"Hmm! Alhaji wallahi bansan me Anam yake son yi ba, ka kalli karamcin da mutanen nan suka yi ma duk da cewa suma d'an su ne amma suka kauda zargin da ake masa suka bashi 'yar su gashi nan yana neman jefata bala'i."
Cikin rashin fahimta Alhj Nura yake kallon ta."Me kike nufi Hajiya?"
"Alhji yaron nan fa baya bukatar mata, da yana bukatar mace taya za a kai masa amarya amma har yanzu ya kasa kusantar ta? Ni inaga da an raba auren kawai."
Cikin tsananin bacin rai Daddy yace,
"Shiya fada miki hakan?"
"to a ina zanji? Har rokona fa yayi a barshi ya bar kasar nan, so yake yaje can kasar turawa ya aure Bature, nifa ina tsoro kada ya nemi 'yar mutane ta baya."
Huci yaci gaba dayi kamar zaki, can kuma sai wani tunani yazo masa dan haka ya kalleta yace.
"ki barshi kawai, yaje duk uban da zai aure sai ya dawo, ai duniya ce tafi bagaruwa iya jima."
Yana kaiwa nan ya mike ya barta anan.
Ba haka taso ba, so tayi ya tsine masa kuma ya raba auren sa da Minal, in yaso Sareena ta aure shi ta haifi namiji koda ba nashi bane sai su hallakar da Anam, shikenan sun mallaki dukiyar.

"wallahi Anam idan ka cutar da Minal ta muguwar hanya ban yafe maka ba, idan ka tursasa ta zan tsine maka."

Wannan maganar da Daddy ya gaya masa ita take yawo a kwakwalwar shi, ya rasa me yake nufi dan haka ya kira Mummy cikin zafin rai da irin maganganun da Daddy ya gaya masa kafin ya baro gidan.
"Mummy! Kinji abinda yace ai, me nayi masa kuma me yake nufi da wadannan kalaman nasa?"
Hajiya ladi tayi murmushi acikin ran ta, a fili kuwa sai tace.
"Anam Daddyn ka inaga baida lafiya, wai fa na sanar dashi abinda Minal take maka na hanaka hakkin ka, nace zan kira mahaifiyar ta ayi mata magana shine ya hauni da bala'i wai bai yafe ba idan ka k'ara kusantar ta."
Hadiye wasu irin yawu yayi kafin ya tsinke wayar.

Da k'arfi ya banka k'ofar falon yayin da take tsaye tana tara cot din ta a gaban fanka, da alama so take ta bushe daga wanke ta da tayi.
Daki ya shige, kusan mintuna biyar ya k'ara fitowa, still twna zaune a gaban fankar.
"mtsss!" yaja tsaki a fili lokacin da ya nufi teburin cin abinci.
Zaro ido tayi ganin ya bude abincin da ta ajiyewa kan ta taci.
"kut!" ya hadiye wayu ganin tuwon dawa da miyar kuka da man shanu tasha yajin daddawa da naman rago.
da sauri ta iso wajen tana cewa.
" sorry Sir, its for my Dinner and ban girka da kai ba."
Bai kulata ba ya wanke hannun sa ya fara ci, ita kuwa zuba masa idanu tayi tana ture baki.
Kunnen sa na dama sai kadawa yake, rabon sa da yaci abinci mai dadin wannan tun kan ya tafi Abuja. cikin salon jan magana yace.
"hv u eaten?"
Girgiza kai tayi,
"where did u gt it?"
Ji tayi kamar ta kunduma masa zagi amma sai tace,
"kud'i nagani da dakin ka shine naje gidan can na tambayi kasuwa sai yarinyar gidan ta rakani muka sawo kayan abinci."
"kice sata kika fara?"
K'ara turo baki tayi tace,
"wane sata kuma? Nifa abinci na siya."
Ganin zai cinye duka yasa tace,
"zaka cinye fa?"
Bai kai ga bata amsa ba aka bud'e k'ofar falon.
Jamila ce yar Makotan su da suka dan saba na kwana biyu.
"Lah kuyi hakuri ni bansan mijin ki ya dawo ba,"
Inji Jamila tana k'okarin juyawa.
Manal tabi Jamila tana cewa.
"ki shigo mana ai ba komai."
Jamila kam tuni ta rufe kofar ta fita, Manal ta juyo sai tayi turus ganin irin hararar da yake mata.
"uban waye mijin ki?"
Ja da baya tayi kana cikin rawar murya tace,
"ai fa...ai ta zata kai ne Yaya Aliyu."

🧐 ga ten readmore din nan Zulaihat😂

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now