NI DA ANAM

1.4K 82 0
                                    

*NI DA ANAM* 
_(Matsalar rayuwa)_

💞🌟💞  

💞🌟💞

✍🏼 _Rubutawa:_

       
*QUEEN MERMUE*

_Tare da:_
         🤴🏻
*KING BOY ISAH*

BABI NA DAYA (12)

'             '👨🏻‍💻👩🏻‍💻'          '
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

Har acikin jirgin Kuka takeyi sai da ya tsawatar mata.
"ke Malama idan bazaki bini ba sai ki kama gaban ki zaki zo ki cikani da ihu sai kace ni nayi cikin ki"
Kalmar sa ta karshe ta kara sosa zuciyar ta sai dai babu yadda zatayi haka tayl hadiye kukan ta har suka sauka a *Kano*.
Ba tsaya a ko ina ba sai gidan sa dake GRA, wanda mallakin sa ne da Daddy ya bashi tun lokacin da yayi J.L.C, gidan yayi kura sosai a haka ya shiga tana bayan shi.
"ki gyara gidan nan kafin na dawo zanyi magana dake."
Yana kaiwa nan ya fice ya nufi zooroad gidan Abba Tahir.

Motacin da ya gani jere  a katuwar harabar gidan yasa shi fargaba musamman da ya hango Motar Alhaji Nura, kai tsaye babban falon gidan ya wuce inda yake jiyo maganar mutane na tashi, kafin ya karasa ciki ya jiyo Muryar Hajiya Ladi a bayan sa,
Cikin rudewa ta iso gareshi har tana tuntube, cikin jin dadi da kewar ta ya rungumeta yana "i miss you Mummy"
"Anam me meka zo yi anan?"
Cikin daburcewa da mamakin ganin sa anan take tambayar,
"oh Mummy bansanar dake  zan dawo ba jiya ne da dare Abba Tahir ya neme ni, yanzun nan na sakko a garin nan"
Gaban ta ya tsanan ta faduwa har sai da Anam ya fahimci hakan cikin kulawa ya kama hannun ta yace,
"Mum meke damunki?"
Nan take ta wayance da cewa,
"ah? Uhm haha ba komai ina mamakin wannan taron da Alhaji Tahir ya kira, nima yanzu yake cemun inzo anan, Allah yasa lafiya"
Ita tashi ga gaba Anam yan binta har suka isa Falon,
"Ras!" yaji gaban sa ya fadi sanadiyar ido biyu da sukayi da Mahaifinsa Nura, tausayin sa yaji ya kama sa ganin yadda mahaifin nasa ya rame sosai.
"ah! My Son ina katsaya ne kaida jirgin ku ya sauka 1?"
Karasawa yayi a wajen Abba Tahir ya zauna a kasa yana sosa keya yace,
"Am Abba na biya na sauke kaya na ne"
Cikin ladabi ya gaida Mutanen da suke a wajen,
Su shida ne a zaune Alhj Nura, da kanen sa Alhaji Jabir, Alhj Tahir kuwa Aminin Alhj Nura ne kuma surikin sa Sai kuma aminsu daya Alhj Hisham Abban Isma'il, daga gefe Hajiya Ladi ce da kuma Hajiya Bilakais Matar Tahir.
Bayan dan gaishe-gaishen da aka kara yi Alhj Tahir yayi gyaran murya yace,
"kamar yadda kuka ji nace a jira har Aqeel ya iso gabanin na gabatar da dalilina na gayyatar ku anan, ba wani abu bane face ina so ku shaida Auren D'ana *Aqeel* da kuma *Amina* ta waje na akan sadaki naira dubu hamsin gasu lakadan ba ajalan ba, yanzu sai ku tashi mu tafi Masallaci dan yin sallar azahar bayan nan kuma sa a shafa fatiha."
"Diff" kowa ya dauke numfashi duk da babu wanda yasan dalilin hakan amma abun ya basu al'ajabi.
Alhj Hisham ne yayi kokarin cewa,
"Alhamdulillahi! Abun yayimin dadi Allah ya sanya alheri sai ku tashi mu tafi kada lokacin sallah ya kule."

"Alhj Taheer auren nan bazai yiwu ba! Taya zaka cutar da yarinya ka aura mata wannan maras mutuncin? Bazan lamunta a cutawa Minal ba"
Alhj Nura ne ya fada cikin tsananin fushi da masifa,
"Ke Umma Minal kiramin ita."
Inji Tahir,
Nan take ta daga waya ta kira Aminar, ko sakkoni goma ba acika ba sai gata ta shigo kan ta a kasa
A gefen Bilkais ta zauna bata kp samu damar gaishe dasu ba Alhj Nura ya jefo ta da tambaya,
"My doughter, ki fadamun gaskiya kina son Akilu?"
Dago kan tayi Aqeel din ta saci kallo sai kuma ta kalli Mahaifiyar ta,
"Eh Daddy!"
Tana fadar haka ta fice falon da sauri yayin da Alhj Nura ya mike tsaye,
"to wallahi ba dani ba acikin wannan lamarin kuma idan aka cutawa Minal ban yafe ba,"
Ya juya ya kalli Hajj Ladi yace,
"ki taso muje!"
Yan kai wa nan ya fice yayin da Alhj Hisham da Tahir suka mike dan zuwa masallaci.
Anam kuka ya fashe da shi, Uncle Isma'il ne ya kama hannayen sa yace,
"haba Aqeel meye kuma na kuka aciki kayi hakuri komai mai wucewa ne kuma inaso ka kasance mai yiwa magabatan ka biyayya."
Da haka dai yasamu kwarin guiwa har aka daura auren imda Abba Tahir yace ya wuce gida ya huta gobe yazo ya tafi da matar sa.
Ikon Allah kadai ne ya isar dashi gida, tunani irin auren rashin gata da akayi masa yake, "a ina zan kaita? Yarinyar da ta cika rawar kai"
Tsaki yayi ya buga sitiyarin motar sa,
Yana shigowa kai tsaye falon sa ya wuce, mamaki yake ganin yanda gidan yayi haske ga karar t.v dayake jiyowa a dayan falon.
Tsaki ya saki ganin Manal kwance a kasa tana sharar bacci sai kuma idanun sa suka hango masa weding satifiket din su.
"dum!"
Yaji kamar an buga masa guduma akan kirji dan shi har ga Allah ya manta cewa auren ta ya tabbata a gare shi.
"Mata biyu?"
Ya fada yana mai zubar da files din a kasa,
"wayyyyyyyyooooo Allah na ya ilahi!"
Cikin karaji ya fada tare da durkushewa dan ji yayi idan baiyi ihu ba zai iya kurman cewa,
Manal kuwa ihun sa ya zaburar da ita cikin tsoro ta mike tare da shirin yi dambe,
Taja kafa daya baya daya gaba haka ma hannu ta ware su tana aniyar kai masa naushi.
Wani irin malolon bakin ciki yaji ya tokare shi dan haka cikin bakin ciki ya mike tsaye, dan sai yaga ta dawo masa jacob din ta babu abinda yafi jin takaici irin dogon wandon ta na mahauka ga kot dinnan da tafi karfi ta.
A jiyar zuciya tayi dan ita mafalki tayi an bata fili daga ita sai Hajiya Maryam da Lawisa ance taci uban su,wannan ihun da taji tazaci dayar su zata kawo mata hari.

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now