BABI NA TALATIN DA BIYAR.

1.7K 85 0
                                    

Sakkwato Birnin Shehu.

A guje ta shigo d'akin tana wani irin fasa kuka. Fad'awa tayi ajikin mama dake zaune kan gado tana linke tufafin Baba.

"Subhanallah. Manal me ya faru? Ina Aliyun ko ba tare kuke ba?"

K'ara fashewa tayi da kuka kana ta mik'e tsaye tana huci.
"Mama. Yaali yaci amanata, ya manta alk'awarinmu. Mama Aliyu bai san girman alk'awari ba."
Kuka take yi sosai har Aliyun ya d'aga labulen d'akin ya shigo, fuskarsa babu walwala da ka ganshi kasan yana cikin damuwa.
"Aliyu me Manal take fad'a me ya faru?"

Zaunawa yayi akan kujera ya matse hannayensa yana mai zurawa Manal da ta durkushe a k'asa tana ci gaba da rusa kuka.
"Mama. Tun a lagos,  tun Manal tana k'ank'anuwarta tun bata mallaki hankalin kanta ba,  mu kayiwa juna alk'awarin aure komai rintsi. Mama na kasa cika wannan ak'awain. Ki duba girma irin na Samira a garemu,  ki duba girma irin na mahaifinta a garemu. Yayi mana abinda duk fadin kasar nan bamu da kamarsa. Ya suturta mu. Mama bama hakanan ba,  yanzu haka maganar da nake yi anan Samira na asibiti. Ina tsoron ta rasa ranta a hannuna. Naje mata da maganar auren Manal da zanyi,  amsar da ta bani ta matuk'ar daga min hankali. Mama cewa fa tayi. " Haba Aliyu, ka d'an jira lokaci na ya k'are mana. Ina ji ajikina bani da kwanaki masu yawa a doron k'asa." Ganin haka yasa nayi mata barazanar zan aure Manal koda kuwa zata dauke duk wani alherinta da tayi min. Nan take ta yanke jiki ta fad'i. Tana asibiti."

"Innalillahi wa'innaalaihirraji'un. Tana asibiti fa? Ai wallahi ba za ayi haka babu yadda za ayi mu aminta kayiwa Samira kishiya. Banga abinda ta rageka dashi ba. Kayi kokarin cetota kada hakkinta ya kamaka. Ke kuka Manal haukar banza  kike babu yadda za ayi Aliyu ya aureki da ciki ajikinki."

"Ciki Mama?"
Aliyu ya zaro ido yana tambayar mama.

"Eh ciki kuwa na haihuwa. Tun zuwanta gidan nan da sati biyu na hango ciki a jikinta. Kuma gata nan sai ka tambayeta dama jira nake kazo na sanar maka kar azo ayi abin kunya."

Da sauri Manal ta mik'e tana shafa cikinta. Kana kuma ta juyar da kallonta akan Ali da ya tsareta da ido,  kana ta kalli Mama.

"Ni ciki? Ciki fa? Wallahi k'arya ne bani da komai. Ali dan Allah ka aureni ka san bani da kowa duk fad'in duniyar nan."

"Ni zanyi miki k'aryar? Sai ki fada mana tun zuwanki gidan nan kinyi jini? Kalli yadda tayi fari ta k'ara cika."
Da sauri ta girgiza kai tana cewa.
"Banyi ba. Ba kuma shi ke nufin ina sa ciki ba. Kawai idan ba zaku taimakamun ba ba sai kun mini sharri ba."

"Ke!"
Ali ya dakatar da ita cikin tsawa.

"Karki zo ki fada mana nonsense, ki zo yanzu mu tafi asibiti ai su zasu sheda mana. Ba zaki zo kisa ayi mana k'azafi a unguwar nan ba,  idan ma cikin ne sai dai a zubar dashi idan kina son zama a gidan nan."

Da sauri ta fice daga d'akin ta nufi d'akin da aka sauketa.
"Ciki? Anam kai ne. Wallahi cikin kane,  ba za a zubar min da ciki ba."
Kamar mahaukaciya take shafar cikin kana ta had'a kayanta cikin bakko. Ba da bata lokaci ba ta fice daga gidan da gudun bala'i.
Ali na nan zaune yana jiran fitowar shiru. Koda yaje d'akin ya duba babu kowa sai guntuwar wasik'ar da ta ajje.

_Ka manta da ka sanni. Cikin da ke jikina na mijina ne. Ba shege bane kamar ni,  yaa da dangin akasin ni,  na san ba zai walak'anta ba. Dan haka ba za a zubar min da ciki ba. Ka zauna da Samira ita kad'ai ta dace da kai. Sai wata rana."

"Manal!"
Ya kwala mata kira kana ya fito waje inda motarsa yake. Babu ita babu alamunta. Yana kokarin tashin mota ne aka kirasa daga asibiti Samira ta farfado dan haka dole ya juya akalar motarsa daga zuwa neman Manal zuwa duba lafiyar matarsa.

Sai da ta kai bakin titi kana ta tsagaita da gudun. Keke napep ta hau zuwa tashar mota.

Tana zuwa ta siye ticket d'in motar Abuja. Tana da tabbacin acan zata samu Anam ba tare da ta had'u da Hajiya Ladi da iyalanta ba.

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now