BABI NA K'ARSHE.

2.3K 113 2
                                    

"Daddy zanje Sokoto yanzu. Jikina yana bani zan ga Manal a yau dan Allah kada ku hanani."

Minal ce ta share hawayenta ta dangwale masa kai tare da cewa.
"Ko kunya ba ka ji? To ai Manal din tana nan asibitin Abuja ta samemu tana nemanka. Ko da muka zo aka sanar nama zuciyarka ta tsaya muka zaci ko ka rasu ne. Shine ta yanke jiki ta fad'i tana can d'akin hutu yanzu."
Da azama ya tashi zaune yana k'okarin sauka daga kan gadon.
"Muje dan Allah in ganta ko zan samu karfin jikina."
Minal tana jin ciwo a zuciyarta,  Mami ta kalleta tare sa daga mata kai. Nan take taja hannunsa. Duka aka rufa musu baya suka nufi d'akin da Manal take. Sai da suka biya dakin Mamarym nan aka sanar da ita Manal tazo kamar tayi tsalle taje haka ta dinga yi. Nan ta shaidawa Anam ta kira Amina zasu zo anjima da safe.

Bacci take abinta. Kallo d'aya zaka yi mata ka gano k'aramin ciki ajikinta. Sai dai Mami kadai ta gano cikin. Sauran duk sun zata ko dama haka take da tumbi.
Da sauri ya karasa kusanta ya kama daya hannunta da babu allurar ruwa.
"Manal?Kece?"
Ya kwala mata kira. Daddy yayi saurin tarom dansa daga kunyar da zai bashi gaban surukai yace.

"To Alhamdulillahi yanzu sai mu koma gida. Ke Zainabu ki zauna da ita har ta tashi."
"To Daddy."
"Aa Daddy a barni zan kula da ita."
Kafin wani yace wani abu. Nurse ta shigo dauke da tire. Likita na bayanta.

Yana shigowa ya mikawa su Dadi hannu ska gaisa kana yace.

"Madallah. Alhj suma ne tayi amma yanzu ko wane irin lokaci zata iya tashi. Sai kuma a kula da ita dan kada abinda yake cikinta ya samu matsala."

"Ciki?"
Duka dakin suka fada a tare.
Dariya Doctor yayi yace.
"Au ashe baku sani ba? To test da akayi mata ya nuna ciki a jikinta. Akalla kuma zai yi wata ukku da sati biyu."
"Alhamdulillah."
Murna sosai suka yi bama kamar Anam da ya rungume hannayen Minal dake gefensa. Anan Dadi da Abba da Zainabu suka fice aka bar Mami da Minal kawai.
Mami ta shaida musu zata je gida.
Bata jima da fita ba Manal ta bude idanunta.
A hankali ta sauke su akan Anam da ya tsareta da ido. Murmushi ta sakar masa kana ta juya da zummar kara rumtse idanunta.
Da sauri ya fara jijjigata yana cewa.

"Manalina dan Allah ki tashi kada ki kara rufe min idanu."
Ai nan take ta mike zaune dan a tunaninta mafarki ne take.
Kuka ta fashe dashi tana cewa.

"Da gaske ka mutu wai?"

"Aa ina nan tare dake da Babynmu ba zan barku ba."
Sosai ya rungumeta yana jin d'umin jikinta da ya dade yana nema.
Minal ta kwankwaso kofar hakan yasa Manal ta zame ta zauna a gefe.
"Sunnu Manal dan Allah ki yafe min sharrin shedan yasa na mareki."
Murmushi ta sakar mata. Ko ba komai zargin cewa Anam ya manta da ita ya kau a zuciyarta. Ta tabbata yana k'aunarta kamar yadda take acan tana ta dawainiya da son shi ba dare ba rana.

Sai sha d'ayan dare aka basu sallama. Direct gidansa na Kano ya wuce dasu. Minal batayi kuiwa ba ya kama mata suka gyara gidan tsab.
A daren ya sanar da Manal da Minal abinda Mamaryam ta sanar dashi banda kuka babu abinda Manal take. Ta k'agara gobe tayi dan ta ga wacece mahaifiyarta. Nauyin maganun da tasha ne ya sanyata dogon bacci sai karfe shida ta tashi.
Salla tayi ta fito falon.
Nan taci karo da Anam da ya dawo daga masallaci.

"Haba Manal kije ki kwanta mana suma jirgin shida na safe zasu biyo zuwa bakwai sai muje."
Girgiza kai tayi cike da tausayi tace.

"Ban fa tab'a bud'e idanu na gansu ba. Wani irin d'auki kake tunanin zanyi a irin wannan ranar? Ni dai ka barni inje."
Kamata yayi suka zauna akan kujera yace.
"Yanzu je kiyi wanka ki canja kaya. Zan shiga na had'a miki Tea sai muje."

Cike da fargaba ta koma daki tayi wanka.
Koda ta fito har ya hada mata tea tasha ya bata magani kana ya shiga dakin Minal ya sanar da ita.

"Aa nikam ku ajje ni a gida kasan tsoro zanji."

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now