BABI NA ASHIRIN DA HUD'U

1.3K 62 0
                                    

Daga lokacin kuma, Maryama bata k'ara samun lafiya ba, a daddafe dai Anam ya kammala exams ɗinsa ya dawo a cikin sati na biyu cif.

         ***
Da murnarsa ya shigo gidan, Meenal tana rik'e da hannunsa tana aikinta na bashi labari.
"Yaya, zamu ga Ya Maryam ne? Jiya ma naji Daddy yace zai zo dubata, amma zamu koma gidanmu ko?"
Minal take tambayarsa lokacin da suke haurawa akan bene.
Baiyi k'okarin bata amsa ba ganin wata mata mai farar riga ta fito daga ɗakin Ya Maryam. (kamar yadda 'yan gidan Abba Tahir suke kiranta.)
Da sauri ya k'arasa bakin k'ofar, lokaci guda zuciyarsa tana bugawa na irin nishin da yake ji daga ɗakin.
Kafin ya k'arasa ciki Ladi ta fito ɗauke da tasa da ruwa a ciki.
"A'ah! Anam my son saukar yaushe?"
Dan dakatawa yayi yana murmushi dukda iya kacinsa leɓunansa, ga yadda zuciyarsa take raƴa masa Ummansa ce ba lafiya.
"Yanzu muka zo, ya Maryam zamu duba kuma zamu koma."
Inji Minal da taci gaba da mak'ale hannunta acikin nasa.
"Bari inga Umma da jiki."
Yana k'ok'arin raɓa gefenta.
"A'ah, ina zakaje? Umma haihuwa za tayi, ka bari har ta sauka lafiya a kimtsata yanzu namiji baƴa shiga."
"Tohm Mummy, kice mata nadawo."
Cikin sanyin jiki ya taka akan k'afafunsa.
A falo yaci karo da Mahaifinsa a cikin halin rashin nutsuwa.
Da sauri yaje gareshi, sai alokacin ya rage alhinin da ya bayyana a fuskarsa.
"D'an baba, kaine tare da Ameena."
"Eh, Daddy ashe Mummy ba tada lafiya?"
"Wallahi jikin ne ya tashi nima yanzu Ladi kemun waya dan naga ta samu sauk'i jiya shine na fita a yau."
Ya ajje Minal da ta ɗale bayansa akan kujera kana yaci gaba.
"Inaga asibiti zamu wuce, ungu je ka fidda mota."
Ya mik'a masa makullin motar kana ya haura sama.

****
Kusan mintuna talatin da shiga tiyatar. Ko wannensu zaka iya gano k'arfin bugawar zuciyarsa tun akan fuskarsa.
Anam ya gagara juri halin da yaga mahaifiyarsa sai hawaye yakeyi, Ladi itace mai lallashinsa.
A firgice Abba Tahir ya iso asibitin sai Matarsa wadda suke kira da Mum Minal.
"Ina take ne? Ba'a fito ba har yanzu?"
Cikin k'araji da tashin hankali yake maganar,kafin ya bada amsa likitan da yake ciki ya fito.

"Am sorry! An rasa yaron sai dai uwar, itama shes in C.C, amma ta nemi ta gana da mutum ukku, Danta da mijinta da yayanta. Sai ku gaggauta dan mintuna biyar muka baku, kafin mu koma kan aiki."
Cikin jimami da tashin hankali su shiga ɗakin da take kwance.
Yaron da aka fitar a cikinta har ya ruɓe yana zube a cikin tasa.
Da azama suka k'araso wajen yayinda Anam ya fashe da kuƙa ganin yanda Ummansa ta koma.

Cikin murmushin k'arfin hali ta kama hannun Anam.
Ta ɗago idanunta da kyar ta zube su akan Tahir.
"Ya..ya,

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now