NI DA ANAM

1.6K 71 0
                                    

*NI DA ANAM* 
_(Matsalar rayuwa)_

💞🌟💞  

💞🌟💞

✍🏼 _Rubutawa:_

       
*QUEEN MERMUE*

*BABI NA ASHIRIN D'AYA*
21

Dariya yayi  har sai da hak'oransa suka bayyana.
Cikin takunsa na rashin kuzari ya ɓacewa ganinta.

Misalin karfe ukku na yamma ya dawo a gidan.
Bai samu Minal ba, sai Manal dake kicin tana neman abin da zata ci.

A falon ya zauna yana neman layin Minal.
Bugu ɗaya ta ɗauka tana mai gaishe dashi.
"Kina ina ne?"
"Ina gidan Uncle, anjima kaɗan zan dawo."
Leɓensa na k'asa ya haɗe da na sama kafin yace.
"Kizo yanzu kasuwa zamuje dan ni bansan abinda ake buk'ata ba."
"Haba Baby, ina yarinyar nan ne? Ka tafi da ita mana, wallahi nikam bazan iya zuwa kasuwa a cikin ranar nan ba."
Dif! Ta kashe wayar.
Mamaki yake irin hali na Minal, sam bata san meye zaman aure ba, yana mamaki ina soyayyar da take masa acan baya ta tafi?
Tsaki yayi a bayyane tare da ɗora hannayensa ya tallafe kansa.

"Sannu da zuwa."
Ta faɗa lokacin da ta fito ɗauke da faranti da daffafiyar indomie.
A hankali ya ɗago idanunsa ya sauke akanta. Wando three q ne a jikin ta sai riga mai guntun hannu, ta fito a siffar Igbo ɗin ta, wata nutsuwa yaji tana saukar masa nan take ciwon kan da Minal taso bashi ya ɓace.
"Sannu, ki shirya zamu je kasuwa yanzu."
Murmushi tayi mai sauti kana ta zauna a tsakiyar falon tana mai tank'washe k'afafuwanta.
"Jirani na cinye abincin nan."
"Akwai sauran abincin?"
Ya tambayeta tare da tsareta da idanu.
"A'a, shi kaɗai ne wannan idan zakaci ka sauko k'asa muci."
Ta faɗa tana mai karkata hankalinta akan t.v.
Da gatse tayi masa maganar, ba tayi aune ba taci karo da hannunsa acikin farantin.
Dariya yayi mata ganin yanda ta saki baki tana kallonsa.
Kaf ya cinye taliyar harda siɗe hannu ya tashi.

Koda ya fito a cikin shirin shadda bai ganta a falon ba, hakan yasa ya nufi ɗakin ta.
Atamfarta ta ɗauko ta ɗauki yagulallen hijabin da take salla dashi ta saka.
Tsura mata idanu yayi yanda kayan suka fatattake.
Taɓe baki yayi tare da cewa.
"A hakan? Ina kayan da aka siya miki?"
"Nifa waɗannan kaɗai ne dani, waɗanda ta siyamun babu kayan arziki a ciki."
Wadirob ta buɗe ta shiga nuna masa kayan.
Baice da ita komai ba ya koma sama.
D'akin Minal ya shiga ya buɗe kayan ta, wata doguwar jallabiya bak'a ya ɗauko sai mayafi bak'i.

"Ki saka wannan idan muka je zan saya miki wasu."
Amsa tayi ta shige toilet.
Da kyar da bone rigar ta wuce mata, dan Manal tafi Minal girma da kauri nesa ba kusa ba.

***-***

A gaban malam Mainasara, Momi Ladi ce zaune a gefen sa tana zayyana masa abinda ya kawota, yayinda Sarina dake mak'ale a gefenta, ta zubawa Malam idanu kamar yace, 'ass' ta ruga.
"Nifa malam, bana son kisa acikin harkata, ko babu komai idan nayi sanadiyar kashe Akilu, uwarsa Maryama bazata yafemun ba.
Amma ni so nakeyi kwata-kwata ubansa ya manta dashi, kaga duk wannan k'azafin da sharri da nayi masa baisa ya kore sa ba ko yace ya yafesa har lahira ba. A gefe kuma ga Sareena dake k'aunar ya kwanta da ita ko sau ɗaya ne, to ni abin da nafi so ya aureta in yaso sai ta haihu dashi kaga dai har wa yau komai ya dawo hannuna."
Ta k'arashe dogon bayanin tare da jinjina kai.
Malam Mainasara ya nisa sosai kafin yace.
"Hajiya Ladi kenan! Tun farko ke kikayi gan-ganci, banga dalilin da zaisa kiyi masa k'azafin luwaɗi ba, kinyi abu kamar ba Ladin da nasani ba.
Yanzu fa k'azafi ko k'aramin laifi ya daina tasiri tsakanin 'ya'ya da mahaifanyansu, kuma tun farko sai da na gargaɗeki akan kada kiyi k'ok'arin shiga tsakanin Akilu da Nura ba tare da na baki umurnin hakan ba, amma ki kayi fatali da maganata ki kaje wajen boka na gangare.
Gashi nan kinyi hasarar mak'uɗan kuɗi a banza."
Ya maida kallonsa akan Sarina kana ya nunata da yatsa.
"Wannan, ita kaɗaice dubarar da ta rage miki a yanzu, abu biyu ne sukayi miki saura. Kodai a karya asirin da Na gangare yayi tsakanin Ak'ilu da matarshi, ke kuma 'Yarki ta maye gurbin matar, amma bazata taɓa zama matarshi ba. A zahirin Gaskiya abu ne mai matuk'ar wahala asiri yayi tasiri a jikin alhj Nura, amma mai sauk'i ne a wajen Ak'ilun. Zan iya aikin da zai nisanta tsakanin su ba tare da sun tsani juna ba sai dai basu buk'atar ganin juna har abada."
K'asar da take a gabansa ya jirkita, kana ya zuba k'ananan duwatsun da suke a gefen sa.
Ya ɗauki tsawon dak'ik'a goma yana karanta wasu dalimisai kana yasa hannunsa ɗaya ya rufe idanunsa tamkar wanda aka haskewa fuska da Cocila.
A karo na ukku yana bugawa saidai har yanzun yakan rufe idanunsa cikin takura.
Cikin jinjina kai yayi duba akan Ladi yace.
"Ladi, muddin kika zaɓi Ak'ilu yayi tarayya da 'yarki, tofa babu nasara a wannan aikin. Abu na biyun kuwa, aikin da zanyi tsakaninsa da mahaifinsa zai yi matuk'ar tasiri, saidai!..."
Ya ɗaga yatsarsa ta hagu a saitin fuskar Ladi kana yaci gaba da cewa.
"...akwai haske a tsakanin bak'in duhuwar da zan tura a zukatansu, ban gano ainahin menene hasken ba, saidai dole mu ta'allak'ashi tsakanin Ak'ilu da Matarsa ta farko,  abu ɗaya da zakiyi k'ok'ari akai shine.
Kafin Ak'ilu ya nisanta kansa da mahaifinsa ya zama cilas ki wargaza auren dake tsakaninsa da Matarsa ta farko."
Ladi tayi zugum tana kallonsa da bayanansa masu surk'ulle.
Lallai babu shakka zata iyayin komai dan ganin Anam ya nisanta da mahaifinsa da duk wani da zai iya sada tsakanin su, saidai ba k'aramin abu bane raba auren da bata k'ulla ba.
"Nasan abinda yake zuciyarki."
Inji Malam yayinda yake gyara cazbaharsa mai kama da kan k'aɗangaru.
Cikin damuwa Ladi tace.
"Malam ka riga da ka sani, jibi su Malik zasu dawo k'asar nan, kuma duk wata wahala su nake yiwa, ina son komai ya tafi acikin gaggawa amma raba aurenne bansan ta ina zan fara ba."
Malama ya bushe da dariyarsa mai matuk'ar ban tsoro da sanya ciwon ciki wanda tuni Sarina ta doɗe hancinta da fuskarta da ya cika da miyaun goro.
"Ladi hoo! Wannan ai mai sauk'ine, barin in zagaya makewayi na dawo miki da cikakkiyar mafita."
Cikin nutsuwa ya faɗi hakan, kana ya ɗauki allon da ke jingine a bango mai cike da rubutu, shi ba na canawa ba shi ba na arabi ba.
Da sauri Sarina ta rik'e hannun Ladi tace.
"haba dai! Nifa kinsan ina sha'awar Hamma wallahi, shine kuma zaki wani zaɓi dukiya akaina."
"Kinci uwarki."
Inji Ladi cikin masifa.
"me Anam ya mallaka da sauran mazan basu da shi? Ko kuma duk waɗanɗa suka k'wak'uleki baki samu mai yimiki dai-dai ba? Bansan inda kika gaji wannan shegiyar jarabar ba, mtsss!"

Ta k'arashe da dogon tsaki, Sarina kuwa ta cika kamar ta fashe.
Kafin ta maidawa uwarta martani Malam ya fito yana gyaran murya.

"Ungo nan,"
Ya mik'awa Ladi wata bak'ar leda.
"buɗesu akan k'afafuwanki, wannan na mai maik'on, Zaki bawa yaron.

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now