BABI NA ASHIRIN DA UKKU

1.4K 69 0
                                    


*#QUEEN2MERMUE*

*BABI NA ASHIRIN DA UKKU*

Maryama Ibrahim Salis, mace ce mai matuk'ar tausayi da sauk'in kai, tana da saurin yarda bata saurin fushi, a kwaita da tawakkali da rik'on addini dukda ta kasance tsatson 'yan boko.
Tun lokacin da tayi aure Tahir babban yayanta yake kula da sha'anin kasuwancinsu da mahaifinsu ya bar musu acan Abuja da Kano.
Haka ta rik'e Ladi da 'ya'yanta da zuciya d'aya tana jinsu tamkar 'yan uwanta.
Ladi a gidan ta tare gaba d'aya sanadiyar mai dafa abincinsu da ta rasu hakan yasa Maryama ta nemi da Ladi ta dawo nan kasantuwar sosai da sosai Ladi ta iya girki.
Shekaru goma suka ja, sarai Maryama ta fahimci k'aunar da Ladi take yiwa Anam dan tana k'aunar mahaifinsa ne, alokacin taso nisanta Ladi dasu, inda tayi mata alk'awarin duk wani abu najin daɗin rayuwa. Sai dai lokaci ya k'ure mata, nan Nura ya nuna babu inda Ladi zataje.
"Haba Maryama, duk shekarun da aka fito hallayarki bata canja ba sai yanzu da kika fi kowa buk'atar Ladi a kusa dake? Ga tsohon ciki, ga Anam da kinsa a yanzu yafi k'aunar zama da Ladi akan ke dan ita bata takura masa kamar yanda kikeyi..."
Cikin ɓacin rai akan kalaminsa na k'arshe Maryama ta ɗaga masa hannu a karo na farko a iya zamansu na aure.
"Yafi k'aunarta? Haka zakace? Ina takura sa? Takurar da nake masa akan addininsa ne, wallahi koda zaku k'ini gaba ɗayanku bazan gaji da takura masa akan addini da tarbiyarsa ba. Bana buk'arta zamansa da Ladi ina so ya koma gidan Yaya har Allah ya saukeni, sam! Ban lamunta a lalata tarbiyar Anam ba wanda yayi sanadiyar hakan kuwa gagarumin yak'i ya haddasa tsakaninmu, dan wallahi bazan yafe ba."
Tana kaiwa nan ta fice daga ɗakinsa.
Wasa-wasa al'amarin yayi tsamari tsakaninsu.
Maryama tana kan bakarta, inda ta ɗauke Anam dake k'okarin kammala jarabawarsa ta Neco ta mai dashi gidan Abba Tahir.
Anam yarone mai matuk'ar hak'uri, sai dai wani lokacin kamar mahaukaci yake idan aka taɓa shi,yana da saurin aminta da mutum, kuma idan yana sonka duk abinda ka tsara ka faɗa masa zai yarda da kai.
Ta hakan ne Ladi take k'okarin cusa masa tsanar mahaifiyarsa da nuna masa itace mai k'aunarsa Maryam kuwa mai takurawace a wajensa.

"Aqeel, ka saurareni da kyau, zan maidaka gidan Yaya bana son rashin ji dan Allah, kagan kuma bana so kana kwaikwayon su Malik, ka rik'e addini da mutuncinka a duk inda kasamu kanka, banace wai kadaina k'aunarsu ba amma ka kiyaye tarbiyar da na baka."
Jikinsa yayi sanyi kwarai, yasan Umma mai k'aunarshi ce,tabbas yasha kama su Malik suna shan sigari, kuma ya fahimci ba'anan kaɗai suka tsaya ba, sai dai shi mai k'aunarsu ne, yana jinsu kamar jinin jikinshi.
"Umma, zan kiyaye amma pls da nayi sati biyu zan dawo nan ko?"
Murmushi Maryama tayi, ta dafa kafaɗarsa tace.
"Eh zaka dawo, nima zan dinga zuwa ina ganinka, ka kula da k'anwarka Minal ka gaishe da su Mama."
Daga haka driver ya tashi motar tana ɗaga masa hannu har suka wuce.

"Maryama. Wai yaushe raini ya fara shiga tsakanin mu ne? Ban isa na shimfiɗa doka acikin gidana ba har sai kin k'etara? To wallahi bari kiji, akan wannan matsalar komai naiya faruwa tsakaninmu."
Alhj Nura ke zuba ruwan masifa a ɗakin, cikin bak'ar zuciya mai kwanji da takasance a k'irjinsa.
"Komai zai faru? Ina da rai da lafiya sai na ajiye 'Yan shaye-shaye a gida? Ban isa nayi musu magana sabida basu bani girman mahaifiya ba? To indai ni na ɗauki Ladi aiki daga yau na sallameta, zan iya ci gaba da biyanta albashi cinta da shanta zan ɗauke mata amma ta koma wani gidan ba anan ba. Wallahi bazan lamunta ba, bazan yafewa duk wanda yayi k'ok'arin taɓa tarbiyar Aqeel ba, gata haukane? Ko kuma arziki fitinace?"
Cikin k'araji da dagiya take fitar da waɗannan kalaman daga can k'asan k'irjinta, zuciyarta na mata zafi raɗaɗi da kuma zugi, hallitar dake acikin cikinta yana k'ok'arin neman mafaka daga tsawa da wutar da ke k'ok'arin tashi a zuciyarta.
"Maryama? Ashe haka kike? Son kai naki har yakai kiyiwa 'Ya'yan Ladi k'azafi? Mace shekaru goma ta wahala da famada ɗanki? Menene batayi miki ba? Menene bata yiwa Aqeel ba? Ko ke da kike ik'irarin kin haifesa baki fita wahala dashi ba."
Ya tako har gabanta,
"Kin canja wallahi, ki nemi Ladi gafara kada hakkinta ya kamaki."
Yana kaiwa nan ya fice a ɗakin ya banko k'ofa da k'arfi.
"Innalillahi wa'inna aelaihirrajiun."
Abinda take nanatawa kenan har ta sulale akan guiwowinta.
Haihuwar Akil da ta fidda tsammani daga ci gaban rayuwa? Jini ake samata jini yana ɓallewa? Numfashi ya ɗauke jijiyoyi suka shafe? Bayan rainon ciki na wata tara, taci gaba da rainonsa har tsawon shekaru shida? Rana ɗaya an goge wancan tarihin a kwakwalwarsa an zuba masa na shekaru goma kacal?
Hawaye zazzafa suke kwarara akan kyakkyawar fuskarta, zuciyarta na zafi da tafasa har saida tayi dana sanin tunkararsa.

Ladi kam 'Yanci ya k'ara samuwa, dama boka ya shaida mata abinda ya faru dan haka kai tsaye a yau ta shirya kwalliya 'yar ubansu. Abincin Alhj Nura ta ɗauko, maimakon ta ajiye akan table kamar yadda ta saba, Maryam takan zo ta ɗauki abincin ta haura sama dashi, yau kai tsaye ta haura a saman.

"Assalamu alaikum"
Tayi sallama cikin mak'ale murya kamar wata shak'akk'ar ganga.
Cikin mamaki ya ɗago kansa daga kallon talabijin ɗin ya zuba akan Ladi da take shigowa.
"Alhaji barka da kwana."
Bai amsata ba, cikin ɗaure fuska yace.
"Me ya kawoki anan?"
Tiren ta ajiye a gabansa ta durk'usa tana kame-kame.
"Ehm dama, Hajiyace tace inzo an kawo maka abincin..."
"Maryam ɗin?"
Ya faɗa cikin ɓata fuska sosai tare da mik'ewa tsaye.
"Eh, ita"
"Tashi ki fita!" ya faɗa cikin tsawa kana ya ɗauki tiren shuri nan take filas ya fashe tus!
Cikin k'araji ya banka k'ofar ɗakin ya shiga.
"Ina take?"
Ya kai dubansa akan gado inda yaganta naɗe cikin bargo. Hakan ya rage zafin wutar da ya shigo da ita, yafi dak'ik'a goma a bakin k'ofar kana ya saita fushinsa ya iso a wajenta.
"Maryama?"
Ya kira sunanta cikin raunanniyar murya.
Da kyar ta iya buɗe idanunsa akanta.
"Bakida lafiya ne? Na kira likita?"
Murmushi ta jefesa dashi kana tayi k'ok'arin gincirawa akan filo.
Tana mai girgiza masa kai ta rik'o hannunsa.
"Haba Maryama, bakida lafiya shine baki gayamun ba? Har da turamin Ladi a ɗaki ta kaimun abincin?"
Ko kaɗan ba tayi mamakin kalaminsa na k'arshe ba, haka kuma bata musa ba illai hannunsa da ta k'ara matsewa.
"Daddyn Aqeel, ba kai bane ka barni ni ɗaya a ɗaki ba? Awowi suka gabata ba tare da mun haɗa kwayar idanuwa ba, ai dole nayi ciwo tunda na tabbatar da fushi kake dani mai tsanani."
Ta tsagaita yayinda ta goge hawayenda suke k'ok'arin makantar da ita daga ganin tasa k'wayar idaniyar.
Rumgumeta yayi sosai, yana jin yanda tsananin k'aunarta da begenta ke hanasa sukuni.
"Maryama bana iya fushi dake, bansan me yasa ba kwana biyun nan nake kasa adalci a kalamanki, dan Allah ki yafeni ke ba abarsa kuka bace a wajena."
Cikin sanyi zuciya tayi murmushi mai haɗe da kaico! Kana tace.
"Nice mai neman gafara, amma kayi min afuwa Akeel ya kammala jarabawarsa kana ya dawo."
"Babu komai Maririn Yaya."
Ya faɗa cikin sigar zolaya tare da lak'uce mata hanci."

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now