BABI NA TALATIN DA UKKU

1.5K 77 1
                                    

Kafin su karasa tuni magen ta mutu saura karen.

Ladi ta zaro wayarta dake cikin aljihu ta shige toilet. Dan sandan zai hanata Daddy yace ya barta.

Numbern boka ta latso ringim biyu ya dauka ya kyalkyala dariya.

"Hahaha! Aiki ya gama cika ne? Ki gaggauta turomin nawa kaso..."

"Malam asirinmu ya tonu. Sun dauki abincin da na zuba maganin sun bawa mage da kare kuma duk sun mutu dan Allah ka taimaka kayi aikin gaggawa ka rufe bakinsu."

"Ke ni ban fahimci abinda kike nufi ba? Ya akayi suka san kin zuba maganin? Ni dai ki aikomin da kudi yanzu"

"Kai nima ban sani ba kawai kayi aikin sai na kiraka."

Ta katse wayar sai zufa take.

Ta fito tana kurari.

"Ni za a nunawa kabilanci? Sai ku jira kuji abinda makaryatan zasu ce."

"Mtss! Ni ka bani hanya zan tafi d'akina."

"Malama ki kiyayi kanki zan fasa miki baki wlh."
Ganin ya hayayyako mata yasa ta koma ta zauna sai aikin harara da take bankawa Nur.

Bayan kamar awa suka dawo.
Gwajin farko ya tabbatar da mummunar guba da karen yaci wadda na take ta markada hanjinsa suka fara darewa suna zama kamar rubabbi. Haka ma magen duk abu daya ya nuna.
Daddy jikinsa yayi sanyi,  yana tuna da lokacinsa yayi da yanzu shine zaiyi wannan kaskantacciyar mutuwa.

Anam ma tsoron Allah ya kara kamashi. Lallai da Ladi tayi sandin mutuwar Mahaifinshi da har a lahira ba zai yafe mata ba.
"Wallahi wannan cin amana ne. Ni za a yiwa kazafi..."

Iface-iface take lokacin da aka zo fita da ita. Sai alokacin Sareena da Mulaika suka fito. Dama Salem da Malik basa kwana gidan sai hudun subahi suke dawowa.
"Mom meya faru?"

Sareena ta fada ganin yan sanda sun tisa kewar Ladi a gaba.

"Munafinci akayi min wai zan kashe Babanku. Ni din nan."

"Haba Daddy a gabanka ake ma Mummy haka? Dan Allah kace su saketa. Ke Mummy ki kira Malam ya fasa yi miki aikin."

Nan take hankalin kuwa ya juyo kanta. D.P.O ya iso gaban Sarina yace.

"Waye Malam din?"
Cike da tsoro Sarina tace.

"Shi ya bata maganin ku bari ta kirasa sai ya fasa aikin."

"Kinci ubanki da in kirasa. In kirasa in ce masa me?"

Ladi tayo kanta tana mai cike da jin haushin Sareena.

"Idan muka je polis station ai zaki kirasa."

Daga nan aka turata mota a aka wuce da ita.

"Manal!"

Wata zuciyar ta kira sunan cike da fargaba.
Da sauri ya fito daga dakin yana mai nufatar falon da ya barta.

Anan ya hango Sarina ta kuka.

"Ke ina yarinyar nan ta dazu?"
Ko kallonsa bata yi ba taci gaba da rera kukanta.

Ganin ba zata kula shi ba ya nufi dakin Mulaika cikin tashin hankali.

"Mulaika ina Matata? Na duba gidnan ban ganta ba."

Saida taja ajinta kamar yadda ta saba kana tace.

"Dazun Mumy da Sareena suka yi mata mugun duka har saida goshinta ya fashe suka koreta."

"Innalillahi... Duka? Manal din? Mummy kinci amanata kin kashe ni. Yanzu ina Manal din tayi na shiga ukku."

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now