NI DA ANAM

2.5K 74 0
                                    

*NIDA ANAM*
_(Matsalar Rayuwa)_



*Babi na 17*

Dogon numfashi taja tare da sauke ajiyar zuciya. Hadala yayi ganin ta buɗe idanuwan ta.
Kuka takeyi sosai a haka ya lallaɓa da ita zuwa bayi.
Yinin ranar banda kuka da sangarta babu abinda take zubawa, abinci ma saidai ya bata a baki.

Manal kuwa, yinin ranar tayi ta zuba ido da kunnuwa dan taji shigowar shi amma shiru babu Anam babu alamar sa.
Tunani kala-kala ya dinga ziyartar ta a lokacin daga yinin ranar babu shi.

Kusan sati ɗaya kenan Anam yana jinyar Minal har abun ya fara bashi haushi, ko ruwa zata sha sai shine zai bata, ganin zata maidashi ɗan bawan ta yasa ya daina mata komai.
"Kin fa warke dan ko ɗinki aka miki ya isa ki warke dan haka idan zaki mike kiyi aiki da zaifi miki, dan ni gobe da safe zan fara fita office."
Dariya tayi sosai kana tace. "Kai Yaya wani warkewa? Har yanzu fa ina jin ciwo a wurin."
Jawota yayi ya ɗaga pant din ta yace." yanz ki bari zan shiga nagani meyasa bai warke ba."
Zaro ido tayi tare da janyo bargo ta rufe jikin ta.
Abu kamar wasa, tsawon kwana ukkun nan duk yanda yaso ya kusance ta abun ya faskara, ita ɗin ma ta fahimci hakan duk lokacin da yaso nuna mata k'arfi sai taga ya zame gefe ya kwanta.
Ita ɗin ma daɗin hakan taji dan babu abinda bata k'auna sama ga yace zai kusance ta, sam ba tada wata sauran sha'awa ko bukatuwa.
Anam yana matuk'ar wahala akan wannan lamarin.
Yau a makare ya shirya dan zuwa Office, sai sauri yake yi gashi shine yake haɗa musu break dan ita gimbiyar bacci ne kaɗai abinda ta iya a gidan.
Yana saukowa a matattakala rik'e da jakar sa yaji Minal na kwaɗa masa kira daga can sama.
"Babyna" ya hangota tana zuwa da sauri lokacin da take saka gyalen ta.
"Baby wallahi bazaka barni anan gidan ba, tsoro nake ji, jiya kaga ɓera ya dinga bani wahala har kuka nayi, kuma gidan ya fara wari ga bayina sai warin fitsari yake."
Sai da ta iso gab dashi tace,
"Muje ko?"
"muje ina wai? A office ɗin zaki bini ko kuma ni zan wanke miki bayin?"
Turo baki tayi cikin shagwaɓa tace.
"uhmm! To ni ban iya ba ka samo min 'yar aiki mana, sai ta dinga tayani zama ko?"
Cikin bacin rai yace,
"babu fa inda zaki bini, ina nasan zan samo miki 'yar aiki a garin nan? Mtss ni zaki kara makarar dani."
Yana kaiwa nan ya banka k'ofa ya fice abun sa. Minal kuwa falo ta koma tana kuka ga wani irin tsoron gidan da take ji gashi ko'ina yayi k'ura.
Wayar ta ɗauko ta kira Abba, yana ɗagawa ta gaishe shi cikin shagwaɓa kana tace.
"Abbana ina so na fara zuwa aiki ne, nagaji da zama ni ɗaya a gida wallahi."
Abba Tahie yace,."eh to mijin ki ya kamata ki faɗawa dama akwai kujerar sakatare sai ki zaune matsayin. Amma fa ki kula kinsan yanzu da aure akan ki, kuma idan mijin ki bai aminta ba kibar maganar aikin."
"tohm Abba, Abba dan Allah kace ya nema mana 'yan aiki gidan mu yayi datti."
Abba yace,"to yayi, kuna dai lafiya ko? Babu wani abu dake faruwa?"
"a'a babu komai, muna lafiya."
"to yayi, Allah yasanya muku albarka."
"Ameen Abbana."
Daga haka sukayi Sallama.
Abba ya kira Anam yasanar dashi yanda sukayi da Minal.
"Toh Abba yayi,zan faɗawa Manager."
Abba yaji daɗin yanda Anam ya aminta cikin sauki dan haka ya ɗanyi masa nasiha da shiyi Albarka tare da jaddada masa da ya shigo Kano dan ya gaishe da Baban sa idan ya sami lokaci.

Yasan Mummy Ladi fushi take yi shiyasa yau ya shirya dan tafiya Kano.
Saida ya ajjiye Minal a gidan Uncle Jabir.
"Baby Allah ya tsare, kada kamanta da 'Yar aikin, a gaishemin da Babula na(kanen ta)."
Daga haka ya wuce.

Baya son fara zuwa gidan su yafi so yayiwa Mummy Ladi Siyayya dan yasan laifi biyu gare shi, na rashin kiran ta da kuma dukan da yayiwa Kanwar sa Sareena duk da yasan tafi son sa akan Sareena, amma dai yasan dole taji va daɗi.
Gidan sa ya wuce direct. Parking ɗin mota yayi ya fito yana mamakin sautin kiɗa da yake ji.
Falon gidan ya gani a share goge tas yasa shi tunowa da Manal. Zuciyar sa ta bala'in bugawa har sai da ya zame ya zauna akan kujera.
Mamaki yake yanda kwata-kwata ya manta da ita.
Mik'ewa yayi ya nufi ɗakin ta da yake jiyo sautin muryar ta tana rera wakar da ke tashi a falon.
Zaune take a gaban mirrow fitowar ta daga wanka kenan, babu komai a jikin ta sanadiyar tasan ita kadaice kuma ta kulle kofar falo.
Wakar take rerawa tana ɗan jijjiga jikin ta, yayin da take taje sumar kan ta da ta kara tsawo,bak'i da shek'i.
Mikewa tayi tana irin juyin Yorbawa da rawar k'asa da suke, Towel ɗin da ta goge jikin ta ɗauko da niyar ta nufin ta shanya a toilet, juyowar da za tayi tagan shi tsaye ya harɗe hannayen sa a k'irji.
Ihu ta saki da sauri ta nufi kofar bayin. Cikin zafin nama ya riko hannayenta ya haɗa ta da bango.

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now