BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS

1.4K 75 0
                                    

*NI DA ANAM*
_(Matsalar Rayuwa)_

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*Wattpad*
*Queen2mermue*

*BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS*

*28*

Sosai Manal take mamakin canjin da Anam yayi, ya kasance mutum mai sauk'in kai, aikin gida ma baya barinta tayi ita kad'ai sai yace ba tada lafiya ai. Yawon bud'a ido da shak'atawa duk suna zuwa sai kace wasu masoya idan suka jera gwanin ban sha'awa.
A yanzu ta yarda da cewa damuwa da tsangwama ne suka jefa shi halin bak'in ciki a can baya har ya jefa kanshi a iftila'in shaye-shayen giya. Yanzu kuma da rayuwarsa ta samu nutsuwa sai take hango nagarta a cikinsa, ta sani dama shi mai tausayi ne.
Sai dai kuma, a ko yaushe tsoro da fargaba sukan dad'a kamata mussaman da ta fahimci akwai abinda yake so a jikinta.
Ik'irarinsa. Rashin zunubi dan ya kusanta da ita.
Kamar ma yau da yake ta k'ok'arin had'a bakinsa da nata, da k'arfi ta kwaci kanta, ture shi tayi har saida ya fad'o daga kan kujerar.

"Ka kyaleni Sir. Kana amfani da raunina bayan kasan ina cin amanar Ya Ali ne."
Hawayen da take mak'alewa suka kwaranyo dàga kwarmin idanunta.
Jawota yayi ta fad'a a jikinsa ya na mai sakata a cikin rik'onsa.

"Manal."
Ya kira sunan cikin muryarsa mai sanyi.

Ba tare da ta amsa ba yaci gaba da cewa.

" kin san da aure akanki kuwa? Ko dai kin d'auka cewa auren wasa ne?"

Murmushi tayi mai ciwo, wani irin al'amari take binnewa a k'asan zuciyarsa.

"Bana jin nauyin aurenmu kamar yadda nake jin girman k'aunar ya Ali a kaina. Shine yafi kowa sona  aduniya, shi kadai ne bai raunata maraici na ba."
Juyar da fuskarta tayi a saitin fuskarsa, kana tace.

"Ni marainiya ce, bani da kowa, ban san kowa nawa ba, wata k'ila ni shegiyace, wata k'ila karuwan Lagos suka yarda ni. Ni fa bani da alk'ibla, bansan wace k'abila da wane yare ne suka cakud'a suka haifar dani ba. Bana ji a jikina, akwai wani a duniyarnan da yake k'aunata fiye da ya Ali.
Na sani Sir kai mai tausayine, ka tausayamin ka takura kanka, ka aure ni dan ka fitar dani daga iftila'in maraici bayan kana da matarka da gatanka. kayimin komai a rayuwa."

Murmushinsa mai taushi ya sakar mata, kana ya tallafo hab'arta da hannunsa.

Ya jima yana kallonta sosai har saida ta sanya tafukan hannayenta ta rufe idanu.

"Manal, nima da kike gani maraye ne, Mamana ta rasu tun ban mallaki cikakken hankalin kai na ba."
Daga nan ya d'an labarta mata kad'an daga cikin tarihinsa da kuma dalilin da ya kai shi a Lagos.

Sosai ta taji tausayin wannan bak'ar gabar da ake k'ok'arin kunnawa tsakaninsa da mahaifinsa.

Manal tsoro take ji, tsoron take ta fad'a soyayyar da babu adalaci a cikinta.
Ta sani Anam yafi k'arfinta, ko ba a fad'a ba tasan yana da gata da darajar da suka ninka nata baninkin.
Ba zai so ta ba. Dan me zata fad'a tarkon k'aunarsa? Jikinta yake so anya tayiwa soyayyar ya Ali adalci? Ita kad'aice a duniyarta dan haka ba zata lamunci zama da kishiya ba. Taya zata yi kishi da mai asali 'yar gata irin Minal? Ta sani da matar shi ta dawo zai tattara dukkan kulawarsa akanta. Anya zata jure hakan kuwa? A'a ba zata cutar da zuciya da ruhinta ba, ya zame mata tilas ta nemi mafita kafin lokaci ya k'ule mata. Ta bayar wa kanta amsa.

Kiran da Mummy Ladi ke masa ne ya ke d'aga masa hankali.
Yasan da cewa gobe ne ranar da zata zo gidan dan haka ya nufi kitchen ya shiga neman maganukan da ta bashi.

Na garin ya d'auka yana ya tsine fuska, da kyar ya had'a shi da madara ya shanye.
Sai d'ayan da tace ya shafa a jikinsa, bud'esa yayi wani irin wari ya daki hancinsa. Babu bata lokacin ya zuba shi a kwandon shara.
Sai guda biyu na Minal da tace ya ba ta.

"Meye amfanin wad'annan kayan k'azantar kuma?"

Wani tsakin ya k'ara saki, kana ya tattara ya zuba su a shara har yana dana sanin wanda yasha.

K'ofar a bud'e take, dan haka ya tura ya shiga.
Bai ganta a d'akin ba sai motsin ruwa da tsintsiya.
A bakin gado ya zauna har saida ta fito.
Tana ganinshi ta sha toka kamar bata tab'a ganinsa ba.
Shima d'in fuska a d'aure yace da ita.

"Kin sha magani?"

"Ya k'are"

Ta bashi amsar a tak'aice.
Fita yayi ya koma d'akinsa.
Kallo ya fara yi har zuwa sha d'ayan dare.
Tun lokacin da yasha maganin ya fara jin canji a jikinsa.

Mararsa yake jin tayi masa nauyi tamkar mai jin fitsari sai dai ba fitsarin bane.
Kasala ta fara saukar masa, nan take ya fara lashe leb'enansa.
A daddafe yayi wanka ya kwanta ko zai samu salama sai dai jiki yace sam ba hakan yake buk'ata ba, yana buk'atar motsawa ne ko zai rage lodin da yake tattare dashi.

Babu mafita, illa ya biyewa gangar jikin ya rage mata zafi koda ba dukan ba.

A hankali ya tura k'ofar d'akin ya shiga.
Akan idanunta ya shigo d'akin, saidai tana mamakin dafe-dafen bango da yake yi, tamkar ba shi da lafiya.
Shiru tayi tana kallonshi da yake a cikin duhu take ita kad'ai take ganinsa.

A bakin k'ofar ya durk'ushe yafi minutes biyu kafin ya fara rarrafawa ya fita.
Da sauri ta mik'e zaune akan gadon tare da fad'in.

"Sir? Meya faru? Ba kada lafiya?"
Dirowa tayi akan gadon tazo inda yake durk'ushe.

Hannunta ya kama ta mik'ar dashi da nufin ya mik'e, amma sai hakan ya gagara.

"Sir menene dan Allah, me ya faru? Meke damunka?"
Duk ta rud'e ta tsorata matuk'a.
Ya gagara yin maganar face sakata da yayi a cikin rik'onsa.

"Ki taimaka mun da ruwan zafi."
Da sauri ta sauka k'asa ta had'a masa bak'in shayi ta dawo.

Kakarin amai yake yi sosai dan haka bai sha shayin ba.

"Sir. Dan Allah zan kira likita, kada ka mutu please, ka bani wayarka."

Sanin cewa ba shida wani takamammen likita anan Abuja balr har yayi numbersa shi yasa bai bi takanta ba ya rarrafa kan gadonta.

"Kin iya Mota?"
Da kyar ta jiyo abinda ya fad'a.
Girgiza kai tayi da cewa
"A'a."
Har  k'arfe d'aya da rabi ana abu guda, da kyar da sid'in goshi bacci ya sure shi.
Manal kam ta gagara rumtsawa sai kallon yadda fuskarsa tayi wani iron haske take yi.
Tsoro ya kamata na ganin yanda yake ajje numfashinsa tare da fisgarsa da k'arfi.
Hannayensa duka biyu a tsakanin cinyoyinsa kamar mai jin sanyi.

Addu'o'i tayi k'ok'arin fara tofa masa a duka jikinsa.

Misalin rabin awa da fara baccinsa ta koma gefe ta kwanta cike da tsoron kada wani abun ya same shi.
Kamar wani mafaraucin zaki ya mik'e zaune akan gadon, idanunsa jawur kamar na ma shayin da ya kwana a club.
Da k'arfi ya finciko Manal da ta fara gyangyad'i. Cikin rik'onsa ya fara k'ok'arin rabata da kayan jikinta.
Nan take jikinta ya fara kyarma, tsoro fal a ranta.
Cikin k'arfin hali ta girgiza shi tare da cewa.

"Sir meye hakan? Innalillahi dan Allah ka sake ni."

Inaa! Kamar tana yi da icce. Baya cikin hankalinsa, komai da yake aikata ba umurnin kwakwalwarsa bane face Zuciya da gangar jikinsa.

*Meryamuequeen*

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now