Chapter 124

1.3K 70 0
                                    

*UNIQUE WRITERS ASSOCIATION*



*MATAR SARKI*

*WRITEN BY*
*AYUSH ILIASU*
*HAWWA SALEH*

*Watpad@AyushaIliasu*


1⃣2⃣4⃣

*Mun sadaukar d wannan fejin ga daukacin masoyanmu d masoyan wannan littafi,Allah y bar zumunci y biya muku bukata,y barmu daku har gdn Aljanna Ameen y rbb.Ana tare irin sosai dinnan*


Zaune yake cikin office din sa ya duk'ufa yana rubutu cikin wani file saida y dau kusan minti Biyar bai dago ba yana rubuce rubucensa,sai can Dr balaraben y dago y k'arewa farha kallon yace tin yaushe kika daina jin motsin cikin? itama da tinda y fara rubutun ta sunkuyar d kanta tana sake sake cikn xuciyarta sai lkcn t dago tace dashi tinda y shiga wata n biyar ne,jinjina kai yai ya jango wata farar takarda yai rubutu aciki yace ynx xakuje aimiki scanning, to farhan tace dashi,wayar land line dake gefen sa y janyo ya kara a kunnensa,byn d ya tbbtr an amsa wayar ne naji yana cewa ki turomin salma,dg haka y ajiye wayar yaci gaba d rubutun sa, bbu dadewa salma ta shigo office din,saida t gaishe d Dr balarabe cikin girmamawa sannan t gaida farha,takardar dayai rubutn y miqawa salma yace mata kije da ita aimata scanning yanxu,rissinwa salma tayi t karbi takardar tace to Dr,jiki bbu kwari farha t miqe tabi byn salma,sunje bakin kofa xasu fita Dr yace salma kuyi sauri fa karki dade,idan kuntarar d wasu kice d sulaiman yai muku injini ko dake bari na masa waya kawai,Ok kawai salma tace dashi suka fice dg office din.

Baafi mintuna 25 ba suka dawo office din Salma t miqa masa sakamakon y karba yai mata gdy sannan t tafi,tsaf y duba sakamakon gani farha tai yanayinsa y canja take taji gabanta y fadi rass,innalillahi wa inna................ta shiga ambata cikin xucitarta,saida y gama jimami y dago y fuskanci farha gami d gyaran murya yace sakamako y tabbar d cikin nan y kwanta,wata zabura farha tayi da sai da Dr y tsorata,take y shiga kwantar mata d hnkli d cewa tayi hkri insh Allah xasuyi iya k'okarinsu wjn ganin cikin y tashi,itadai farha d tinda Dr y fara mgn tai shiru kmr wdd ruwa y cinye sai da y miqo mata wata takarda yace d ita wadannan magungunan zaa siya insh Allah kina sha komai xaixama normal, karbar takardar tayi jiki b kwari tai masa gdy ta fita,sosae Dr y tausayawa farhan musamman d yaga tashiga damuwa.

Tinda t dawo dg asibiitin t shiga daki bbu abinda takeyi sai aikin kuka ita kenan a hka rywrta xata kare dg wannan sai wannan ynx t fidda rai baxata taba samun farin ciki d kwncyar hnkli a rywrta ba.

         A haka ta wuni har saida sarki y dawo sannan taje asibiti yasa sarki xuwa dubata kfn y tafi masallaci sallahr magriba,baxai iya jira har sai yaxo yimatsma saida safe ba dan yau b a dakinta yakeba,lkcn d ya shiga dakin kwance y ganta saman gado hawaye na bin kuncinta d alama ma batasan ya shigo ba,cikin halin tausayawa y k'arasa inda take y d'agota y rungume,jinta d tai a jikin maimartaba yasata sakin sabon kuka,maimartaba bai hanataba saida tai mai isarta sannan y tmbyta ydd sukai d Dr ,cikin shashsheqar kuka t shaida masa abinda yace da ita,take wani gumi y karyowa sarki yana ambaton innalillahi wa ........Allah humma ajirna fi musibatina wa aklifna khyran minha,tin dg hk maimartaba y kasa cewa komai sbd tsabar kidimewa d yayi,itama farha bata km mgn ba saida sarki yaji ana kiran sallahr magriba ya miqe xaifita,har yaje bakin kofa sannan farhan tace ga takardar magungunan d xaa siya din,karba kawai sarki yai yasa a aljihunsa y fita,dakyar itama farhan taja jikinta tayo alwala ta gabatar d sallahr magriba,haka taita addua har akai sallahr isha'i sannan ta umarci rakiya ta Kawo mata abinci d tea,dan bata cikasa halima aikiba nauyinta takeji,dakyar t danci abincin tasha tea din d yawa sannan ta shiga wanka.

Can ma maimartaba saida y dau lkci yana addua akan matsalar farhan saida akai sallahr isha'i y dawo gida. Tinda rakiya t kawowa farha abincin takoma takewa halima tsegumi taga idon uwar dakin su ya kumbura d alama kuka tayi,jinjina kai halima tayi afili tace Allah yasa b wata matsalar mugayen mutanen nan suka km jefa baiwar Allahn nan ba rakiya t amsa d amin.

*Bayan  wata uku*

Babu wani mgni d farha bata shaba dan ganin cikin nn ya tashi hk ma maimartaba bbu wani kokari d baiyi ba akan cikin amma abin y faskara,har saukar alqur'ani yasa akai mata km aka rubuce matashi tasha amma shiru.

Wata rana sarki yai bak'o abokinsa y kawo masa xiyara dg garin kaduna,tare sukai makaranta dashi, aikine y kaishi kadunan,suna zaune suna hira a dakin d sarki yake saukar baki, abokin y lura hankalin sarkin baya kan hirar d sukeyi, shiru yai shima yana naxarin sarkin y tbbtr yana cikin damuwa,kafadarsa y dafa yace meke damunka abokina n lura tin dazu hankalinka baya kan hirar d mukeyi? Murmushi mai martaba yai sannan y xayyanawa abokinsa duk abin d ake ciki ya Dora d cewa wllh Tijjani babu wani kokari d ba muyiba amma abin yaci tira,shiru tijjani yai yana nazarin kalaman sarki can ya nisa yace amma baka ganin hakan baya rasa nasaba d asiri kuwa? Ido mai martaba y zaro yace haba tijjani wani irin asiri km kake magana,mirmishin tijjani yai yace eh to nidai nafi danganta matsalar d asiri Sanin kankane gida kmr naka n sarauta yana cike d kalubale iri iri kama dg kan abokan zama d sauransu,jinjina kai sarki yayi yana gaskata mgnr abokin nasa yace amma kuma lafiya suke zaune fa d abokan zamanta,dariya mai kama d yaqe tijjani yai yace haba abokina kana matsayin sarki y dace ace kawuce wannan gabar ta fuskantar duk wani Abu d zai faru a gidan nan,kada kayi mamaki akan duk abinda zakaga y faru a gidan nan,sosae sarki y jinjina  kai tabbas yasan gsky abokinsa y fada km yasan hakane kawai yana gudun zargine shiyasa tin farko baiyi tinanin hakan ba.

Nan take maimartaba suka ringa tattaunawa t ydd zaa shawo kan matsalar,bakaramin ddi sarki yajiba d wannan xiyara d tijjani y Kawo masa b yau. Acan kuwa gidansu farha momy nata shirye shiryen haihuwar farha ganin ciki y shiga wata n 8,wayarta t dauka t kira farhan byn sun gaisa take tmbyrta y nauyin jiki,kuka farhan ta fashe dashi lkci guda hankalin momy y tashi,tmbyr farhan takeyi lpy amma farha t gagara amsata,kashe wayar momy tayi tana adduar d duk tazo bakinta,tinani t shiga yi wannan wace irin ryw farha take yi dan t tabbar kukanta baya rasa nasaba d wata matsalar d ta shiga,sai da farha tai kuka mai isarta sannan ta yanke shawarar shaida wa momyn abin d ake ciki game d cikin sbd duk a tinanin ta matsalar baxata dau lkci kmr hkba cikin xaitashi ,dan farha t kasance yarinya mai tsananin xurfun ciki Dan ko a gd kfn aurensu sai takure momyn ke Sanin damuwarta duk kuwa da jansu  d momyn keyi a jiki tana muna musu itace komansu,kama dg damuwarsu xuwa jin ddinsu amma hkan bai canja dabiar farhan b ta xurifin ciki.

Wayar ta t janyo t kira momyn ckn sanyin murya ta xayyanawa momyn abin d ake ciki,SBD tsabar takaici momyn ta rufeta d fada tana cewa d ita amma farha bansan rashin hankalinki d xurfin cikin ki yakai haka ba,wannan matsalar ai ba abar boyewa bace,sbd rashin hnkalin ki bakya ganin irin gidan d kike zaune komai xai iya faruwa dake amma har ynx ba kiyi hnkli ba to wllh tallahi ki nutsu kisan meke miki ciwo,momyn n kaiwa nan ta katse wayar cikin kunar rai d jin haushin wnn banxar dabiar ta farha.


Byn momyn ta dan nutsu ne ta shirya d kanta sai gidan yaya,byn sun gaisa d mahaifiyar tata take xayyana mata duk abinda ke faruwa tare d cewa haka fa wancan matsalar d ta shiga taki fad'a min ko yan uwanta sai da fyrouxa t haihu taxo sannan n fuskanci tana d damuwa sai nice n tinkare ta na tmbyta sannan take fada min,sosae YAYA t jinjina lamarin gami d cewa xatasa malam y taimaka mata (wani makocin yaya ne da yake taimakawa mutane idan matsala makamanciyar haka t taso musu),take momy taji ddin wata nutsuwa taxo mata dan tasan mahaifiyar tata xatai iya kokarinta akan matsalar,haka suka ringa hira d tattauna alamura d matsalolin ryw.

Bangaren mai martaba ma yasa a bincika masa alamarin kuma cikin ikon Allah anyi dace t hanyar tabbatar masa d cewa lallai asiri akaiwa farhan aka kwantar d cikin km wnda yai a cikin gidansa yake,mamaki taf y cika mai martaba yai Allah wadarai d duk wnd yaiwa farhan wannan mummunan abin,haka km gudin karya ta dawa farha hankali yasa bai fada mata asiri ne ba yai shiru d bakinsa yana adduar Allah y Toni asirin duk wnda yai asirin.

Wata uku sai da suka shude farha nata mgni kama dg na bangaren mai .artaba da na bangaren yaya,had'i d addua sannan aka samu cikin ya taso, ranar d aka tabbatrwa d farha ckn y taso baqaramar murna tayi ba,haka shima sarki dasu momy sunyi murna d adduar Allah y kare gaba y km sauketa lpy.

Momy taso farha t taho gida har saita haihu amma t hkra ganin abin b mai yiyuwa bane km b tsarin masarauta bane.

    Duk wnn kitimillin d akeyi n Neman mgni su jakadiya d kubrah basu sani ba suna can suna nasu haukan,duk kuwa d lokaci lokaci Sina ganin farhan,ganin d sukai baa zancen haihuwar farhan ya km tbbtr musu d aikin su yayi dan hk hankalinsu kwance suna jin ddi.

MATAR SARKIWhere stories live. Discover now