*UNIQUE WRITERS ASSOCIATION*
*MATAR SARKI*
*WRITEN BY*
*AYUSH ILIASU*
*HAWWA SALEH**Watpad@AyushaIliasu*
1⃣2⃣3⃣
Tinda y kwantar d ita bata motsaba tmkar mara rai haka take saika lura sosae xa kaga nunfashinta na kaiwa d komowa a hnkli,sarki rasa yadda zaiyi mata yai kawai y xuba mata ido cikin tausayawa.
Baa jima ba Dr y k'araso gdn sarki, a harabar gidan y tsaya y kira wayar sarki y shaida masa ya karaso, d Kansa y tashi yaje ya shigo d Dr har dakin d farha ke kwance yai masa bayanin abinda y faru,Dr ne ya shiga kwantar masa d hnkli dan y fuskanci hankalinsa a tashe yake,duba farhan ya shigayi cikin gwaninta d k'warewar aikin sa sarki sai binshi yake d ido kawai,jin hamdalal d Dr yai yasa maimartaba saurin tmbyr meya sameta? Murmishi Dr yayi gami d cewa congratulations yallabai hajiya na dauke d ciki na sati biyu,nan fa sarki y washe baki yana murna d gdy g Allah da yasa xaiga wannan ranar da swtyn shi ke dauke da cikinsa,Dr ne ya katse shi da cewa ynx xaa Samata drip ne sakamakon Aman da tayi ruwan jikinta y ragu,cikin sakin fuska sarki yace dashi kayi aikinka duk abin d y dace kawai,take Dr yasa mata ruwan gami d rubuta mata magungunan d xaa siya ya bawa maimartaba takardar hadi d cemasa dolene saita samu Hutu sosae km kada t ringa yawan motsa jikinta ko aiki har sai cikin yayi kwari,gdy sarki yai masa sannan sukai sallama Dr y tafi.
Zama maimartaba yai gefenta ya tsura mata ido yana murmishi har saida ruwan y kare y cire mata,bacci take yi bata tashi ba sai around 12 har lkcn maimartaba n zaune yana gadinta kmr xaa dauketa,lkcn d ta tashi a hnkli take bude idonta ta saukesu akan na mai martaba murmishi y Sakar mata itama t mayar masa,matsowa yai yana shafa fuskar ta a hnkli yana mata sannu, dakai kawai take amsashi,tmbyr ta yakeyi ko tana buqatar wani abu tace aa,yace to kisha ruwan tea sbd xakisha mgni Dr yazo y baki mgni, da mamaki take kallon maimartaba, dakyar ta iya bude bakinta a hnkli tace masa magani km? meya sameni? Fuskar sarki dauke d murmishi yace mata bakida lpy ai ko kin manta abin d ya sameki dazu ne? Girgixa kanta tayi alamar a'a yace to ki tayamu murna Dr yace kina dauke d ajiyata ta sati biyu,kunya farhan taji kmr t nitse saita basar tace wace irin ajiya km? Batare d yai mgn ba ya kamo hannunta y dora saman cikinta yace kinga ne yanxu ko,hannun tai saurin kwacewa t rufe fuskar ta ,dariya yai yace ina alfahri dake km ina kara gdy g Allah d yabani mata mai tsananin kunya,wannan kunyar taki sosae take kara rura wutar sonki a ckn xuciyata km ina adduar Allah yasa ki haifamin yaya musu halaye d dabi'unki,(sbd d haka kunya b karamin kima d daraja suke kawa mace a idon mijinta ba gakuma Uwa uba tana kara soyayya a xuciarsa,kada kice ke wayayyiya ce ki cire kunya ki ajiye kina ganin kauyancine a zaman aure ki ringa jin kunyar mijinki, aa b haka bane wayewa daban kunya daban,amma xakaga wasu matan tamkar yan bariki sun ajiye kunyar d akasan ya mace d ita d sunan wayewa alhalin hakan b komai bane face rashin wayewa,hkn km baya kara miki komai a gun mijnki illa raini d rashin ganin kimarki d darajarki,dan haka ahir dinmu yan Uwa mu riqe dabiar mu ta kunya d akasan ya mace d ita) haka maimartaba yaita yabon farha tana jin ddi ckn ranta tana km kara sonsa d kaunarta,saida y taimaka mata ta sake wnka badan tasoba sai dan b ydd xatai ne jikinta b kwari gashi aman d tai dazu duk y bata mata jiki,byn t fito y hada mata tea tadan sha sannan Tasha mgni sai sabon bacci d ya dauketa.
Tin daga ranar haka farha tai ta renon cikinta ckn kwanciyat hnkli saide yawan bacci d takeyi d kasala, ga maimartaba na tarairayarta datace uhumm zai tmbyeta ko lpy hkan ba karamin karawa maimartaba kima d daraja yakeba a xucia d idon farha dan bata taba tinanin masu sarauta suna kula d matan su, a tinanin ta m basuda lkcn matansu ashe b hk bane,cikin gdn km b wnd yasan tana d cikin sai mjinita d bayinta Dan ko fita cin abincin weekend d maimartaba yakeyi d iyalinsa ta dena xuwa km maimartaba bai takura d saitaje b dan yasan halin d take ciki,shima sarkin bai shaidawa matansa farhan nada cikiba,km su halima sun gargadeta d kada t sake ta bari yan gdn Susan tana d ciki sbd gudun sharrinsu musamman d sukaga jakadiya n tmbyr su wasu abubuwan akan uwar dakin nasu sunsan b abin arxiqine yasa take tmbyrsu dan sunsan halin gidan sarauta ciknsa d bayansa shiyasa km koda wasa basu taba fadawa farhan irin bin diddigin d jakadiya keyi akanta ba gudun karsu daga mata hankali saidai sundau alqawarin kare uwar dakin nasu muddin sukaga abinda xai cutar d ita.
A yau cikin farha ya shiga wata na 5 sbd haka harya fito yaimata kyau das ajikinta duk wani yanayi n laulayi farhan t daina ji dan hk yau weekend ta fita xuwa wjn cin abincin,kallon kallo aka dingayi tsakanin matan sarki d farha musamman kubrah d bataso farha tayi koda barine agidan nan ba,bangaren hjy maryam kuwa murna tayi d ganin farhan d ciki,ahaka aka waste daga gurin xuciar kubrah a cunkushe,koda t koma bangarenta ta aika aka kira mata jakadiya,byn jakadiya t xo kubrah t balbaleta d masifa yaushe tai sake d aikin su har farha t samu ciki,mamaki sosae jakadiya tayi farha d ciki km kodai gixo taiwa kubrah,cikin rawar murya jakadiya tace Allah y huci xuciarki uwar dakina,hannu kubrah t daga mata cikin fusata tace ayi gaggawar kwantar d cikin nan bazata haifeshi ba muddin ina raye,jakadiya tace angama ranki y dade amma d zubarshi akai xaifi sauki,ran kubrah ne u kuma bace t dakawa jakadiya tsawa tace kiyi ydd nace b shawarki nake nema ba umarni na baki,bansan kwakwalwarki sam bata aikiba jakadiya sai yau so kike a zubar wato t kuma daukar wani? to kwantarshi nakeso ayi ydd har mutuwarta baxata km daukar ciki ba,bata jira cewar jakadiya b tai fuuuuu t shige uwar dakin ta,sim sim sim jakadiya t miqe t fito jiki b kwari.