A/N
hey lovey dovies,
atlast de ga wani update din nan ya iso gareku,ba fa da 'yar qaramar wahala ba,
to be outspoken,m not too sure 'bout how i plotted d chap,
imagine,
have been erasing,typing plus editing non-stop through out a week span fa knn,
ugh,nd all d tanks goes to dis freaking hectic chap right here,
buh Alhamdulillah,Masha Allah,
tunda har Allah ya bani daman kammalashi,har ma gashi yanzu naa kawo,
Rabbi yasa duk mu amfana kuma mu fahimci asalin saqon da ake son a isar,
Insha Allah,Buds,idan kunason #NAJRAH
don't ever hesitate to VOTE, plus
COMMENT for dem....🍀****🍀****🍀****
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
****🍀****🍀****🍀
*Strictly inspired by Truelove📖*By ©UmmySaudat✍
®*Saudat Adam Isah*wattpad_ummysaudatt
18_
Kai dakata,
ni babu wani abinda zan ji daga gareka,'ya de diyata ce ko,kuma ni din ke da alhaki na za'ba mata mijin aure,managarcin mutum me kyawawan halaye da dabiun da suka saje da ra'ayina,to sam kai din baka shiga cikin jerin wa'annan mutanen ba,
tun wuri gwamma ka janye duk wani quduri naka akanta,
can ka tafi gun ire iren mata masu salon dabi'unka,ni kam bade da 'diyata ba,babu yadda za'ai na aurar da 'yata ga mashayin giya kuma ga dan iskan mutumin dayai qaurin suna irinka,na hada ka da girman Allah tun muna sheda juna daga yau dinnan kada ka sake kayi gangancin da har ze sani ganinka da ita ko alamunka a cikin gidana..."duniyarsa ke juyawa a cikeda tsananin zugin radadi ne har ya himmatu da tariyo munanan lafuzzan da kunnuwannasa suka kammala jiye masa kimanin awanni uku ciff baya,
yananan cikin motansan dake killace ta gefe can da jikin qofar gidansu zahra,inda ya zubar da kansa tun zamanin da ikon Allah ya fitar dashi daga cikin gidan,
na ganosa da'bar mutuwar zaune saman seat me mazaunin driver,babu wani qwaqqwaran motsi a tattare dashi,banda azababbun ruwan qwallan dana gani na tsaka da silalowa kyakkyawan fuskansa,wanda shine kurum abinda ya bani sheda na alaman dakwai rai a tattare dashi,wanda rabon daya shiga makamancin hali na uqubar data hassaso masa zubarsu har ya mance shekarar,
daga shi se Allah suka san tsananin alhini da tashin hnkln da suka taru sukai masa rufdugu a wannan lkc,
wanda yake jin kaman ana tsaka da watsa ma ko wacce ga'ba ta jikinsa wuta ne,kai barimma ace masifaffiyar abar da kenan qulbuce can a qarqashin tsakiyar qirjinsa,wanda yake jin kaman ya 'kwaqulo ta ya zubar uban kowa ma ya huta,
yake ma kansa addu'ar dama ace mutuwa ta iso tai awon gaba dashi,shi ze fiye masa gata dan gamuwansa da baqaqen ranakun dake tafe da barazanan rashin zahra,
"Innalillahi....",
"Allahumma ajirny fy musibaty....",
"Qala rabbish rahly sadry....",
"Wa yassirly amry....",
fal rudani ya ringa innatawa qasan zuciyarsa,
sa'ilin da a hargitse ya zaro waya ya hau kiran layinta,da hk ya shafe wadataccen lkc batareda samun nasara ta kan abinda yake nema ba,
kansa ya dauki caji,zuciyansa ya kuma bugawa da qarfi kaman me shirin faso qirjin ya fito,
"shkn a yanzun zahra ba huruminsa bace!,da gaske ne nan ya rasata a rywrsa!",
al'amuran da suka qwace ma qarfinsa ne yasa besan cikin daqiqun daya 'daga wayar dake hannunsa sama ba,
"NO,dis cant be",
ya doki steering dake gabansa da wani uban qarfi a hade da 'bare baki kaman wani bijimin zaki ya saki irin gigitaccen ihun daya sani falfalawa da gudu har ina neman na saki fitsari,wanda har seda motan yai wani wawan girgiza,
abinka da mutumin da besan da zaman wai,"yana son abu ace an hanasa ba",
lamuran suka zo masa a wani irin yanayi na wuju wuju,
ai a haukace naga ya sama motar wuta,a hade da juya steering yai wani irin mugun u~turn,ya figa da mahaukacin gudu kai kaace sabon kamu,
Allah me iko,
bahaguwar hnkl da tunanin Najib baa su suka samar masa da akalar qaqqautawa ba har se da ya samar ma kansa wurin parking dede gaban wani hamshaqin Night Club din da kana gani kasan ba qananan miyagun qwari ne ke baje kolin ziyaransu gun ba,
gabaki daya lamuran duniyan na cinsa ne ya 'ballo murfin motan ya fito kai tsaye se farfajiyan filin daze sada shi da cikin club din,
kaman yadda rudin zuciya take dibansa a game da yaqinance masa cewan zuwansa wurinnan ne kurum abinda ze mantar dashi wannan tsatstsauran lamarin dake masa barazanan zautar da ilahirin hnkl da tunaninsa,
se gashi saman wata doguwar stool din dake fuskantan Bar counter din gun,har beiyi wata wata bane yasa aka cika masa Wine cask fal da Whiskey din dayai ordering,
sede kuma mei!,'dagawan dayai ze kai bakinsa ke da wuya ne se ga kunnowan wasu batutuwa nan,
a tashi daya suka karyo suka bugi saman qwaqwalwansa,
"wai shin meye asalin fa'idar!,
wacce irin musibar ce wannan yake neman ya kuma jefa rywrsa!,
ina ribar dake a cikin zuwansa gurbataccen wurin nan!,
shin anya wannan yabi hanyar da zata 'bullar dashi kuwa,sei meye akai knn idan ya kusanto kansa ga komawa gidan jiya,meye zesa ya kuma ha'b'baka kallon rashin cancantar da ake masa,meye zesa baze natsu ya fuskanci matsalarsa ta ingantaccen siga ba,",
sannu a hnkl najib ya ringa qididdige munaqisar da shedan keson ya kuma shirga ma rywrsa,
jikinsa ya mutu murus da sauke wine cask din dake hannunsa ya hada da jikin tebur din gabansa,
"Ya Rabbig firlyy....",
ya fada sagaggun hannayensa biyu tallabe da saman goshinsa qoqam,
he never saw this coming,wlhl azeem ko da wasa bei ta hassasa tsammani da cewan qazamin rayuwar dayai baya ze dawo ya farauci tsaftatacciyar rywr daya shimfida har hk ba,
bama da wani babin yake neman ya horas da shi ba wai se da ta'bo masa mafi girman jigo na rywrsa irin zahra,
a karo guda ga zantukan mahaifinta nan na kumai masa zagayen 'dawafi a ka,
"can ka tafi gun ire iren mata masu salon dabi'unka,ni kam bade da 'diyata ba,babu yadda za'ai na aurar da 'yata ga mashayin giya kuma ga 'dan iskan mutumin dayai qaurin suna irinka",
lkc guda kansa na saukar da wani mugun harbawan da yakeji zagaye da duk wata jijiyar dake aiki a ciki da waje,wanda yake ji kaman sara ake kafta masa ciki,bugu da qari kafirin kuwwar kidan dake tashi a gun na kuma hayayyaqo masa,
sosai a'lamura sukai masa bala'in tsamari,
yai ta maza har yai jarumtan tsaida duba da qwaqwalwansa ga al'amuran dake afkuwa gun,
Wa'iyazubillah,
idanuwansa ke ta masa nuni da qarshen ba'dala,watsewa,tambadewa da shedanancin da ake tsirfantawa gun,
ya kauda kansa qasa a kunyance,yayinda wani irin rudani da takaici ya gama lullubeshi,abun kamar almara,wai makamanciyar qazamin rywr dayai baya knn!,
haqiqatan bei ga laifin Abba ba,wallahil azeem babu uban da yana ji yana gani zeso ganin 'yar daya haifa naa danganta mu'amula da fasiqin mutum me tsirfanta munanan dabi'u irin wa'annan ba,
sei de kuma mei,babban abin dake kuma baqanta masa rai halin yanzun shine rashin bashi daman ya kare imaninsa,
a inda ma yake jin 'dugon sukuni da qaimi a ransa shine idan yai tunanin irin so,yarda da amincin da zahra ta miqa masa,
"she's d one nd only being dat makes his life a better place,her love nd trust just means everything,nd never will he trade it for anything no matter what",
ya haqiqance ma qasan zuciyansa,a yayinda yake kuma daukar ma kansa alwashin bazei taba ba'da ma zahra rsa qasa a ido ba,daga yanzun har illa masha Allah babu ko daqiqan da zei iso ya shude ba tareda tayi alfahari da mallaka masa birnin zuciyarta ba,ze kuma tabbatar mata da cewan loving him is never a mistake,
bi'iznillah se sun rayu tare a qarqashin inuwan ma'aurata,
ya zame masa waajiban ya yunqura don qwatarma ingancinsa haqqi a gun mahaifinta,
kamar yanda aka samu bakunan da sukai shedar 'batanci a garesa,to hk zalika yana da haqiqanin cewan dakwai tarin wa'anda zasu bada kyakkyawan sheda ma dabiunsa...
YOU ARE READING
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
RomanceStrictly inspired by TrueLove, extraordinary LoveStory,revolving around Islamic Values,Family goals,Friendship,Destiny nd a lot more, Showcasing dis in a super baffling way, #ZuciyarMutumBirninsa, sabon salon labari,wanda ya ke tafe da asalin qasait...