26~Laifin Dad'i......

2.2K 111 10
                                    

Finale date~Monday,25th February 2019,

🍀****🍀****🍀****
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
****🍀****🍀****🍀
*Strictly inspired by Truelove📖*

By  ©UmmySaudat✍
®*Saudat Adam Isah*

wattpad~Ummy_Saudah

26_

da hk duniyar take juyawa,kuma al'amura da dama suke afkuwa har ma su shud'e su zama labari,a cikin ranakun da suka faru suka wuce na shafukan kundin qaddarar Najib ya had'a har da wanda ya karb'i sammaci daga State high court ana tuhumarsa da laifin kisan kan Mufidah Magaji Mabel,
dukkuwa da yadda y'an uwa da abokanan arziqi sukai ta k'undunbalan ganin abin be kai labari ba,se ikon Allah ya kayar dasu qasa warwas,yayinda shi Najib d'in be nuna ko d'ar ba,sabida me?,yasan bashshi da wani dalilin da ze sa ya d'aga hnkl kan laifin daya tabbatar ba shine yai ba,ina! bei ci nanin ba nanin bazata ci sa ba,
se ya jingine al'amuransa ya fawwalasu ga Allah huwal Aleemul Hakeem,
da shike Allah ba azzalumin Sarki bane,'wa mallahu yureedu zulmal lil alameen',
se ya kasance a zaman farko da akai kotu zuwa na biyu aka tara qwaaraaran shedun da suka wanke Najib fes a cikin ruwan sanyi,ba fa da taimakon wani ba,taimakon Allah da kuma taimakon CCTV camera na gidannasa ne aka bi diddigin al'amuran da suka wakana a ranar sha takwas ga watan yulin shekarar da ake ciki,wanda ya kama daga tataccen rashin mutuncin da Mufidah da qawayenta biyu,Ramatu da Azeemah suka surfa ma Zahra,har ya zuwa bayyanar Najib da fitan da yai riqe da zahra,dawowansa gidan daga bisani har da qaramar yaqin da sukai dashi da Mufidah,gashinan qiri qiri na'urar bata bar komai ba har lkcn da ta sakar ma kanta harsashin bindiga ya fasa mata kai har lahira,
rashin qwararan shedu a gefen masu qara yasa akai watsi da complaint d'in na Brigadial Magaji Mabel,yayinda kuma ake tsammanin mutumin ze zagaya yabi duk wani hanyan da zebi don ganin ya huce baqincikin mutuwar y'ar tasa tilo se kuma fa labari ya juye ya sha ban ban,duka bada gudummowan ko wanne mahaluqin ba ne ba se na bawan Allahn da ake ma laqabi da Alhaji Ahmad Mekudi(meturare),Mahaifin Najib ya kasance irin k'waarin mutanennan ne masu baiwan iya sarrafa zance da kuma madaukakiyar girma da kwarjini a idon jama'a,akasari da wannan baiwar da ubangiji ya huwace masa ne yake zame masa makami gun saye zukatan jama'a,
mutumin da ya dawo daga baya har a bakinsa kake jin kalmar "MA FATA FATA",
toh babu mamaki ko watak'il da wannan ne yai amfani gurin narkar da zuciyar ta Brigadial Magaji Mabel,
ai daga hk ne akalar rayuwar Najib ta miqa simiqal ba tare da wani tangarda ba,ata ko wanne b'angare bashshi da wani ragowan matsala,
Najib ya zama babban mutum na qin qarawa,sosai Allah ya daukaka girmansa har a idanuwan jama'a,kamar yadda ya zamana yanzu hk kaso 75 bisa d'ari na operations d'in rukunan manya manyan kamfanonin AMP wanda ya kasance family business din da mahaifinsa ya kafa,duka a qarqashin iko da gudanarwarsa yake,
baya ga hk Najib ya kuma hab'b'aka gidauniyar daya kafa tun shekara da shekaru idan me karatu me manta ba,domin tallafama al'umma marassa qarfi,da kuma wata gidauniyar tasa ta yaqi da shan miyagun qwayoyi a tsakanin matasa maza da mata,da hana zaman banza,
Najib yaa kasance garkuwa ya kuma zama abin koyi ya yi shahura kan ayyukan alkhairinsa kuma abin koyi ga duk wani matashin dake tasowa a fadin qasar Nigeria dan har se daya samar ma dubban matasa aikin yi qarqashin inuwar mabanbantan rassunan kamfanonin AMP,
a kwana kwanannan ya kuma kafa wata babbar cibiyar dake daukar nauyin jigilar kaiwa da kawowar al'umman musulmi marasa hali sauke faralin aikin Hajji,niyyarsa duk shekara……
a bangaren rayuwar data shafesa da iyalinsa kuma,
babu ata fagen da zaka tab'o su wai kace ka jiyo kansu,ba kuma wani abinne ya kasance masu garkuwa ba illa shaquwa da amintacciyar soyayyar da ubangiji ya halitto a tsakanin zukatansu,gaba gaba yake kuma yi yai nisa har ya fice ya kuma zarce tunanin duk wani mutum,
yasa ko a kasantuwar ranar da zahra ta tsinkayi labarin da ya tabbatar mata da gaskiyar lamarin wai Najib dinnan de,mijinnata,abin alfaharinta shi ne nan ashe mutumin daya keta mata haddi ta hanyar fyade,amma fa a shud'ewar lokutan da rayuwarsa bata waye ba,yake kuma a cikin duhun da bega hasken da yake gani a halin yanzun ba,
bata san abin daya makantar da ita ba,bata ga laifinsa ba,bata tab'a ganin baqinsa ba,ta rasa meye yasa,
har ma take ganin shin wai ma ina ribar ne!,ina ribar da zata ci ne idan tai masa qyashin yafiyarta,alhakinta a kansa baze cutar mata dashi ba kua?,wannan baze shafeta ba kua...,haqqun, cutar Najib cutar ta ne nan,lfyn Najib lfynta ne,ko a wani hali ya tsinci kansa me kyau ko akasi dole ne su shafe ta...soyayyar da take masa ne nan yasa,yaa riga daya gama d'aukanta kacokam,a inda ta taki sa'a se be kaita wurin daze barota ba...,
a gefe guda kuma yayinda Zahra take tunanin ita iyaa ilimi da kwalin karatunta na National Diploma(ND) sun isheta zaman duniya da mai da yaji,tashi guda se Najib ya shayar da ita mamakin da bata tab'a zato ko tsammani daga garesa ba,rana tsaka ya damqa mata admission letter nta na BUK Course din Pharmaceuticals,dukkuwa da cewan course din ya sha ban ban da wanda tai baya take kuma da burin ta lalubo aiki dashi wato SLT,se bata nuna masa ba,taje tai karatunta halftime,shekaru biyar rigis Allah ya nufeta da kammalawa,wanda acikin halin da ake ciki yanzu hk tuni Najib ya bud'e mata wani tamfatsetsen pharmaceutical industry,wanda za'a riqa had'a nau'ikan drugs ana distributing ma cosmopolitan da kuma wani Clinic gefe guda duka da sunanta,wanda ko qaddamar da bude su d'in ba ai ba tukuna a cewarsa wai se bayan Allah ya sauketa lafiya...

ZUCIYAR MUTUM BIRNINSATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang