🍀****🍀****🍀****
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
****🍀****🍀****🍀
*What a freaking love story📖*By ©UmmySaudat✍
®*Saudat Adam Isah*wattpad_ummysaudatt
10~
Ranan wata Juma'a da safe,
a can cikin Guardroom din daya wadatu da tsararrun masu laifi ne na tafi ganin Najib,
yana can gefe jingine da bango wani sukuku dashi a yayinda ya sauke idanunsa qasa,lumshe,
du ko da cewan ba wai barci yakeyi ba,ya tsunduma ne a cikin birnin zuciyarsa,inda babu wacca yake ji yake gani sama da kyakkyawan halittan zahra,da yadda wutan so da qaunarta ke cigaba da ruruwa a cikin ko wacca daqiqa,wani gefen na ransa ke tayashi jimamin daga ina ze bullo ma lamarinta,yaushe har ze samu sauqin wannan musibar,
dan tun yana iyaa Namijin qoqari dan ganin ya yakice babinta har qarshe ya zubda makaman yaqinsa,ya gama haqiqancema kansa cewan ta riga data zauna kuma ruwa da iska batada ranan fita,
sosai zuciyar tasa ta kafe masa ta tsare da azalzala,ita a lalle i lalla babu abinda take muradi bayan zahra,
a yanxun rashin ganinta ne yake neman ya halaka shi,
hkn yasa har ya ringa daukarma kansa alwashin bala'in daya tanadar ma mufidah gagarumi ne,jin kaman qiran sunansa ne ya sanyashi dawowa daga kogin tunanin daya dulma,
ya bude lumsassun idanunsa cikin sauqi ya saukesu setin gun dayaji sauti na isowa,yana ganin sojan dake gabansa ne ya sanya shi auna wata tsinanniyar tsaki yaja a hade da kallon banzan daya watsa masa ya kauda kansa gefe kaman be san da ajiyar Allah gabansa ba,"so na ur father na yin b d owner of AMP,
o boy,no wonder,so,dat wan b d reason y u too deiyyy haughty shebi?,
buh d tin wei still de baffle me nayin b how come u take enter dis place for d first place na....",(pidgin english)
mutumin ya 'dan tsagaita yana cigaba da bin Najib da kallonsa fal qurillah da niyyan jin wani qarin bayanin daga gun shi,
(aha,niko ca nace lalle ashe zaka shirya kwana anan din kam)
ganin baze samu abinda yake nema bane ya sanyashi 'dorawa da kausashshen muryansa,
"abeg carry ur self comot jare....,
u don get d freedom",da haka ne najib ya miqe ya bar cikin gun banda kumbure kumbure babu abinda yake,
dan memakon yai murna da fitarsa ma se yake jin zuciyarsa dagule,daga jin wannan yasan Mahaifinsa ne ya shigo abun,a sa'ilin da zuciyarsa ta cika fam da haushin Mahmoud
(wanda ya kasance Abokinsa ne tun a zamanin childhood,da ya zarce ya zama Amini,ya qure har ya zama kamar dan uwa,bugu da qari kuma Miji a gun qanwarsa wacca suke uwa daya uba daya wato Fareeda),
tunda tsaf yasan shine ya fada ma Alhaji halin da yake ciki,
kuma tsaf yasan da wannan Alhaji'n ze qara a kan na baya,har ya ji dadin sukansa a duk sa'ilin daya samu dama,
yaja tsaki a dede lkcnda ya sauke idonsa kan Mahmoud din dake tsaye wajen MP guardroom din,
"mazaaa,
...ko kasan abinda ya faru a jiya jiyannan kuwa...,
bayanan fa a qasar ma gaba ki daya,
buh via phone to phone talk,
then he makes d impossible fucking possible,
nd u finally....",
Mahmoud din daya aza yayi abin gwaninta ya fada bakinsa washe,
kallon haushi Najib ya bisa dashi ya wuce ya barsa nan,yayinda shi mahmoud din yai 'yar qaramar murmushi ya take masa baya,cikin motan Mahmoud din suka shige suka lula titi,
banda sautin waqar Ed Sheeran me taken 'Shape Of You' da sassanyan sanyin da Ac ke fitarwa babu Vibe din daya karade ko ina,
se kuma tulin zantukan da mahmoud ke korama Najib,wanda yai kunnen uwar shegu dashi dan kawo i yanxun kam shi kadai yasan lamuran dake damunshi,
de da cewan muhallin Najib a street din Matan Fada yake,yasa ya zama dole ne ta gaban makarantan SOT zasu gifta,
hkn har yasa a dede gun da suka biyo ta gun,Najib ya nemi alfarma wa mahmoud kan ya tsaida motan,
batare da gardama bane ya paka motansa gefe yana kuma bin expression din dake sanye kan fuskan aminin nasa da kallo,kaman yadda aka saba 'din,ilahirin hnklnsa ya tarkata ya miqa a kan duk wani dalibin dake kai kawo bakin gate din,
unfortunately,har aka shafe lkc me tsawo be samu daman yin tozali da abinda yaketa faman cigiya ba ,
shi mahmoud kam tun yana 'dokin ganin abinda aminin nasa ke son yi har ya gama qosawa,banda magiya babu abinda ya cigaba dayi da mita yana azalzalansa da tmbyyi babu kai babu gindi,
"bani minti 5",shine kurum abinda najib ya cigaba da nanata masa,har minti 5 din ya ru'banya ya shafe tsawon awanni 2,
qarshe najib cikin yanayi me kama da tashin hnkl ya koma ya jingina da seat din motan,hannunsa dafe da qirjinsan da tuni ya somai masa bugun harbi kaman ze dare,
"kaja mu tafi kawai",ya fada da tsuran damuwa bayyane cikin sautinsa,
a lkcn da ya ha'de idanunsa ya lumshe da qarfi,kawai jin kansa yake kaman yai ta faman rafka ihun kuka yana 'wayyo Allah na',qilan ya iya samun sauqin radadin da ya gaji da mamaye qahon kafofin zuciyarsa,
shikam mahmoud mamaki ne ya masa dabaibayi a cikin kallon halin da aminin nasa ke ciki,se kuma jikinsa yai sanyi ya qiya tada motan,
a cikin sa'a guda ne najib ya soma jin bugun zuciyarsa na tsananta,dan tabbatar da abinda hasashensa ke basa ne ya bashi daman bude idonsa,
a de de lkcnda ya saukesu kan babbar 'diya a gun Mukhtar na Allah (Zahra)
ALHAMDULILLAH,
shine abinda ya ringa hawa kaina dan ganin yadda tsuran farinciki ya gaji da bayyana kansa a ciki da wajen najib,
a lkcn daa ace zaka dubi zuciyarsa,hk zakaita qirga lamuran da zuciyar tasa keta faman ayyanawa dangane da ita,ya gama qissimawa kansa kan ze iya yin uban komai ma dan ganin ya kai ga mallakan wannan qasaitacciyar halitta,a wannan karon kuma dangantakan arziqi yakeson ya qulla tsakaninsu,
shi mahmoud daya fuskanci abun,
se hkn ya ringa sashi 'ba'b'baka uban dariya kaman ba gobe,
har seda su zahra suka tari keke napep suka tafi ne kamin najib ya soma dawowa hayyacinsa,
aka ci sa'a har ya samu daman maida hnklnsa gun mahmoud din da har yanxun be gaji da dariyan ba,hkn yasa shi 'bata rai da fadin,
"kai dallah ka bari,
it's not funny mana",
mahmoud na qoqarin tsagaita dariyan zumbur ya dago daga seat din motan dayake jingine,yace,
"no dude,u're funny...,
buh banda naka abun ai wannan daga ninta ba biyema iskancinka zatai ba,bare har ta samu daman maye maka gurbin ita wancar din da abu ya kwabe tsakaninku",Najib ya gyara zamansa yana kallon fuskan mahmoud dakyau,
"baka sani ba Mahmoud...,
lemme tell u,
u see dat bae!,
she is super rare,
she is a freaking beauty,
guy she exist's as d absolute defination of elegance,
believe me,ban taba jin mace a raina kaman yadda nake jinta ba,kuma sonta nake a matsayin matar aure,nd am damn serious about dat,
Man maganan gsky wlh aurenta nake son nayi",
ya qare zancen babu wata alaman wasa a saman fuskansa,
se a sannan mahmoud ya maida abun da gaske amman mamaki uwa ze kashesa yake kuma jinjina abun,dan mutum 'dan duniya irin najib da maganan aure ai kam kasan abu bana wasa ba,"Dude like serious fa,
...re u for real",
najib ya girgiza masa kai yana kuma tabbatar masa,
dede lkcn da wayan mahmoud ta hau rurin kida,"ALHAJI",
sunan daya fito saman screen din wayan da manyan baqaqe,
qasurgumin girman da Alhaji ke dashi idon mahmoud ne ya dingi bayyana zahirinsa dumu dumu,
ya gama dedeta nutsuwansa kamin ya daga,ya rusunar da kai kaman gaban Alhaji'n yake yana miqa masa gaisuwa a cikeda ladabi,
ko meye ake fadi daga dayan bangaren de banji,naji mahmoud ya kalli najib da fadin,
"eh muna tare ranka shi dade",
ya cigaba da sauraren abinda ake fadi,daga bisani naji yace,
"to,ranka shi dade",
ya qare zancen ya danna handsfree yana miqama najib din dayai wani kicin kicin da fuska,"hello...
"Son,
"Najibullah....",
aka jera fada daga daya bangaren,
yayinda najib din ke bin wayan da wani kalan kallo mawuyacin misali,a dede lkcn ji yake kaman ya katse kiran,
hakanan se ya qiya,yaja numfashi ya sauke da fadin,
"barka da rana Alhaji","Madallah,
yaya kake!","a qoshe da lfy Dad",Najib ya amsa,
a dede ga'bar da Alhaji yai murmushinsa me sauti wanda yafi masa kuka ciwo,yana fadin,
"Masha Allah,
da kyau Son,
buh it does'nt seem so",a sannan ya numfasa,ya 'dora,
"ka fadamin!,
....what d hell 's happening to you huh?,
wani abun kunyan nakeji bakin Brigadial Magaji,sounding as horrible as u attempting to rape his daughter,
ina so insan dalilin dayasa a kullum babban burinka be wuce ka wofantar da rayuwanka,
ko matsayina na uban daya kawoka duniyar ma,abin takaici abin baqinciki ya zama ni din ne ban isa da kai ba,ka dubi mutum kamanni me girma da kima idon jama'a se ya kasance a kullum alwashinka be wuce ka tozartani...",
"tit",najib ya katse kiran a taqaice cikin hucin haushi,
ya tsinkayi muryan mahmoud a cikin fadin,"kaide kam babu wanda ya kaika matsala wlh,kuma Allah ya ganar dakai,Ya nunamin ranan da zaka soma gudun fushin ubanka mahaifi",
Najib ya tari bakinsa,
"malam ja mota ka kaini gida dalla",
du da yadda maganar tai kama da me tsauri amman raunin dake dauke da sautinsa ya dunkufar da wannan,hkn ya bama mahmoud qwarin guiwan seta kansa sosai yana fuskantansa,
"Najib mi magana ta gsky da fahimta mana,tunda kai din me ilimi ne,karan kaina na isa in bada shedan wannan,
kasan karatun haqqin iyaye,kuma kasan albarkar dake a cikin kyautata masu,hk zalika musibar dake tattare da quntatawa a garesu,lamarin dake cimin tuwo a qwarya,har nake rasa dalilin take saninka...",
ya dan numfasa a cikin kallon Najib din dayai wani zuru hannunsa tallabe da kumatu kallonsa yake qyam kaman wani me daukan darasi,a karon farko daya 'baro masa irin wannan zancen ba tareda ya taka masa birki da bambamin bala'i ba,
hkn ya kuma qara masa qaimi,
a sannan ya shimfida murmushi kan sautinsa ya 'dora da fadin,
"Masha Allah,
tunda daman gashi har ka soma zancen aure,
nasan Allah ya riga daya kawomu lkcn,
Dude it's hightime u go talk things out with him,
karan kanka kasan ni masoyinka ne,Najib u re more like a brother,a kullum ni me maka fatan Alkhairi ne,
da Allah ka qoqarta ka tsaya kaima kanka karatun ta natsu,dan tsaf abinda ka shuka shi din kake girba,jiya ba yau ba Najib,ka tsaya kai tunanin abinda gaba zata haifar maka"...
a sanyaye najib ya daga kai yana kallonsa murus,
Mahmoud ya ka'da masa kai ya damqo kafadansa a hnkl yana 'dan jijjigawa,
Najib din da yai wani tsam dashi,dan ga dukkan alamu de for d first time in record kam,zantukan mahmoud sun ratsa shi,bece um ba bare um um har mahmoud din yaja motan ya qara gaba dasu...
Masha Allah,
Here we come,
pls ku samo min soda pop mana,am damn exhausted throughout ma way crafting dis wollah,
buh never mind me jare...next episode coming as earliar as tomorrow by evening insha Allah,buh ma conditions apply,
~atleast inaso in samu sama da 10 votes nd comments,
then after dat we keep on rocking d free world kawai,love y'all,
SunnySmilesUMMYSAUDAT
ESTÁS LEYENDO
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
RomanceStrictly inspired by TrueLove, extraordinary LoveStory,revolving around Islamic Values,Family goals,Friendship,Destiny nd a lot more, Showcasing dis in a super baffling way, #ZuciyarMutumBirninsa, sabon salon labari,wanda ya ke tafe da asalin qasait...