22~A Cikin Gida

2K 102 8
                                    

🍀****🍀****🍀****
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
****🍀****🍀****🍀
*Strictly inspired by Truelove📖*

By  ©UmmySaudat✍
®*Saudat Adam Isah*

wattpad~Ummy_Saudah

22_

Kano State,Nigeria.

Zahra~
jikinta zulme da wata zumbuleliyar Hijabi shudiya ta shimfide darduma ta hau ta tsiri miqa nafilin data saba yi a wannan lkc (Salatud Duha-Walha),
qwarai ta himmatu a gun tarkato al'amuranta tsaf tana miqa su ga Mahaliccinta,a inda tafi bada qaimi kan Allah ya sauketa lfy,Ya kuma albarkaci abinda zata haifa,dana bainan Al'umman Musilmi gabaki d'aya,
ta had'a da rero karatun Suratul Maryama da Rahman ta sauke,
wanda har se a sannan ta ida warwarewa da samun sukunin laluben waya ta shiga aikin tuntub'ar layin Iyayenta,
kamar yadda yin hkn ya zame mata al'ada na wayewar ko wacce rana,hk din kamar kullum kullu yaumin,yau din be fita zakka ba,har ilaa yauma takununnan basu fasa sanya mata albarkarsu ba,uwa uba fatan alkhairi da kyautata ma d'iyar tasu Addu'ar gamawa da duniya lfy,
tattausar zuciyarta fara qal tamkar auduga,ta ijje waya tana jin yadda 'dan cikinta ya zanqale ya ringa mintsilanta da kukan qugin data waye ma kwanan zancen,har ya bi ya tilasta ma dubban gab'b'anta yunqurawa,suka bata taimakon miqe tsayinta,suturar dake jikinta ta rage yai saura daga ita se wata sakakkiyar silky gown me kalar ruwan d'orawa da zanen fulawowi jajeye,
sa'adda daddad'an qamshin girkin daya gauraye A CIKIN GIDAn ya gaji da ba'de mata hanci,
al'amarin daya tsokano mata wani irin shauqin kwadayi,
abinka da danginsu acici mala'ikun tauna,aka wani fice da hanzari jiki b'ar b'ar..
~
a sararin simiqal d'in wadatacciyar dakin daze sada ta ga ficewa b'angarennata sukai kacibus da Najib shi kuma na tunkarowa,
wata wata basui ba suka ida rufe 'yar tazarar datai saura tsakaninsu...,
tai tsam da rai,idanuwanta sukai zonzono a cikin kallon yadda ya shagaltar da hnklnsa da dubansa yana kuma yawata hannuwansa a saman tuulun cikin daya tattare kansa yai tsaye daga qasan maranta,

"Habiby",

"uhm-hum",
ya amsa mata kira a qasan maqoshi,

"ya dai,kina magana ne"
furucin da ya qara,se d'agawan dayai faran faran cikin sassarfa ya matso ya sumbaci lab'b'anta a taqaice,yana tsareta da idanuwa irin d'abi'arsa sau tari idan yanason ya karanceta,

a hnkl ta kawar da kanta a fuskansa,cikin sanyi ta d'aga y'an yatsun hannuwanta ta watsa su kan wasu y'an maballan gaban rigar 'Banyan' d'in jikinsa,shiru shiru na kamar daqiqu biyar sannan ta soma da kame kame,
"am Betterhalf wai ba wani abin bane ba fa......naga kwanakin mu biyu knn da dawowa kuma bakaa fadin komai batun har yaushe ne zaka maidani gida d'in goyon ciki",

ya nemi qwayar idanuwanta ya setasu cikinnasa yana d'age girarsa guda,
"yeah,sarkin garaje,
ai se ki bari har zuwa lkcnda nai deciding koh",

ta yamutse ta marairaice masa,
"Haba dan Allah mana,ga mutum fa a kusa da gidannan wai kuma har se ya jira an yanke...",

"Babe kada fa ki b'ata min rai mana,
kada kuma kii tsammanin dan na bi ta son rannaki kin dawo din yana nufin kin samu makafar kumai man gardama Zahra,tun ma ba kii gangancin dazesa ni sauya tunanina ma gaba daya,so enough of dat da Allah lets go eat already",
zancen daya ida sa'a guda ya dauketa cak suka dumfari fita,ya barta da cuno bakin da yake qunquni,

_a nan ne har na b'ige da ciccilla mayun idanuwa a tsakankanin gidan alfarman daya amsa sunansa,kuma ma'abocin girma da tsari na ajin qarshe,aljannar duniya ga wanda yai katarin ziyartansa_
~
Anjima can,
ya bayar da Misalin qarfe ukku saura na yammacin Allah Ta'ala,

Firgigit ta farka tai zumbur a zaune daga saman kaftareriyar gadon da take nan kwance,
fuskarta zaka gwada kalla amman hk se kai ta lissafa tarin fargaba da rudanin dake tasowa kama daga birnin zuciyarta,
al'amuran da suka sanya mata dafe tsakiyar qirjin dake ta faman harbi,tana qyarma har ta ringa kawo salati tana ijjewa,da kuma duk wata addu'ar da ta ta'ba sani rakwacam a fadin iliminta,
sashin tunanin muguwar mafarkin datai ne lkc guda suka samu gu suke ta neman sui barazana da ilahirin notikan natsuwan da suka taba d'aure qwaqwalwanta,
tsuru tsuru ta dingi baza idanuwan da suka wani qwalalo suka rine tamkar suna shirin su zube a ko wani kusurwa na dakin,
rashin ganin dalilin Najib ne abinda ya kuma hautsina mata lissafi,
tashin hnklnta me yawan gaske har ta tasarma sashin apartment din nasa da budaddiyar amon muryanta na qwalalo bitar sunansa,

ZUCIYAR MUTUM BIRNINSAWhere stories live. Discover now