16~So da Shaquwa

2.6K 145 4
                                    

A/N

nd here comes d latest chap,
kinda crappy,dull nd d worst of all UNEDITED,
kumin uzuri ku karanta shi da zuciya daya,
just bear with me,nd i promise,gonna make amends in d coming episodes,
a yanzun lamura sun sha kaina like hell ne shys,

happy reading,
nd again never forget to pamper me with those loving votes nd comments of urs

🍀****🍀****🍀****
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
****🍀****🍀****🍀
*Strictly inspired by TrueLove📖*

By ©UmmySaudat✍
®*Saudat Adam Isah*

wattpad_ummysaudatt

16_

2months After,
as life goes in,
a sannu a hnkl rayuwar yake tafe,
da hk har kwanaki sittin suka faru suka shude,
cikin yardar ubangiji yasa lamuran Najib suka miqa ga bin tafarkin tsira,kuma 'dari bisa 'dari aka ida samun nasara har suka samu ma'aunin daidaituwa,
nd all d thanks goes to Malam Iliyasu Me iyali,
a cikin wa'annan lokutan da suka gabata ne da taimakon Allah aka duqufa,aka dingi sauke ALQURANI har sau babu iyaka,duka da sunan Najib,
aka rubuce masa shi tas ya ringa kwankwadama cikinsa,aka maida kai tuquru da nema masa Ludufa,Gafara da Rahamar Ubangiji,shima ya jajirce a nasa bangaren,
Alhamdulillah,
Fa'inna Ma'al Usriyy Yusrah (Q94,V5),
(To,lalle ne tare da tsananin nan akwai wani sauki),

da taimakon Allah,a sannu aka warware tafkin Musibun dake a lullube da tabaron Najib,
duka suka zama labari,
al'amuransa suka rikide in a good way fa,
ababen da yake so ada halin yanzun suka juye suka zama abokan gabansa,
sega Najib ya yanke duk wata mu'amular dake a tsakaninsa da Mutanen banza,kai har ma da ababen banzan de duka,a yanzun ya zama babu abinda yaqi jini sama da ya gani ko yaji warinsa irin nau'ika da dangin abinda ya shafi maye,giya ko barasa,
bugu da qari ya idda yin bankwana da duk wata harkar da zata kusantosa ga zina,a yanzu hk sam,gabaki daya bainan Mata basanan gabansa,
point of correction amma fa idan aka cire masa qwara daya tal cikinsu aka ware,
Ya natsu ya gyara ibadunsa tsakani da Allah,a kullum sujjadarsa ta qarshe a tafe yake da yima mahaifiyarsa addu'ar neman jinqai da Rahamar ubangiji a hade da nema ma kansa gafaran Mahalicci,
a yanzu hk ma tuni aka hau aikin gina masallatai da duk wata dangin data shafi sadaqatul jariya,
ya kafa qungiyoyin taimakon gajiyayyu duka da sunan akai ladan kabarin mahaifiyarsa,
yayinda Mu'amula ta ginu tai qarfi qwarai tsakaninsa da Mahaifinsa,
kuma a gefe guda ga immaculate lovelife dinsa nan,
dan a kwana a tashi,
se ga danqon soyayyar da ta idda kankama tai qarfi a tsakanin zukatan Mutane biyu,
a gun Najib da Zahra asalin soyayya ake babu kama qafar yaro,
shaquwa daso kaman su hadiyi junansu,kaman a tare aka halittosu,
a kusan kullum kullu yaumin a tafe yake zaryan zuwa gidansu,a ko da yaushe masoyan na manne da taimakon waya,
lfy lfy,hnkl kwance lamura ke tfyrma ko wannensu,
a yanzun babu wani fargaba ko 'dar a qasan ran zahra,
sosai gabaki dayanta ta gama sakankancewa da Najib,
dan cikin ikon Allah shi Najib be bar mata ko dalili qwara guda tal daze hassasa rashin samun gamsuwa da ingancinsa ba,Addinance har da Mu'amulance,
kyawawan Dabi'unsa,
kalan tsaftatacciyar so,kulawa da kyautatawan da yake kwatanta mata ya wuce gaban misali,
hkn yasa se ta nemi wannan sashin dake son ya shafa masa baqin fenti ta rasa,a inda ta gama kyautata ma kanta zaton dake tafe da cewan ita da Najib are meant to be,he's her destiny,
alal haqiqa,rabuwanta da jabeer nada dalili,kuma tasan wannan dalilin alkhairi ne,
ya bude mata qofar daya sadata da Najib dinta,
shine nan wanda Allah ya zaba mata,Mijinta kuma uban 'ya'yanta wanda ya kunna mata tsuran farincikin da bata taba zato ko tsammanin dakwai irinsa a doron zamanimmu ba,

Weekend,
Ranan Asabar,
da Misalin 2:44pm,

na hange ta can,
a kimtse tsaf cikin shigar datai na wata hadaddiyar purple super java,wanda akabi da kyawawan floral patterns masu kalan silver,
an danqara asalin dinkin fitet gown din daya tafi dakyau ya lafe ya kwanta da dirarren jikinta de yadda ya kamata,a mutunce kuma a cakude da gayun de duka,kanta a yane da mayafi silver na chanel,
wani irin kallo na kafe ina binta dashi fal na qurilla,
ba ni kadai ba,dan harta Sahibin nata,kullum a cikin yi mata irin wannan kallon yake,kuma yake tai ma kansa kwadayin ganin ranan da Ubangiji ze cika masa qudurinsa na more mallakar wannan cikakkiyar qira,wadda take nan qere da 'yar taqaitacciyar halittar da Allah (SWT) yai ma Zahra,
kyakkyawan mulmulallen farin fuskanta,banda asalin kyau da annuri babu abinda ya bada himma yana fitarwa,
batun labarin zuciya a tmby fuska ne nan ya tabbata,
kwanciyar hnkl,jindadi da farincikin dake nan kwance a qasan zuciyanta ne ke tsaka da fallasa kansa dumu dumu a saman fuskanta,har baida iyakan lissafi,bafa anan abin ya ida yada zango ba,yanayinta ne gabaki daya ke neman ya sauya min,
a yanzun so full of life,carefree,loving,hopeless romantic,ambitious,aspiring duka de gasunan har basuda iyakan lissafi,
nd obviously,all d credits goes to fadowan Najib Ahmad Mekudi Meturare cikin duniyanta,
yana tafe ne da qasurgumin sauyi da kuma isassun lamura kyawawa,wa'anda ta fuskanta gameda kanta,wanda a tsawon shekaru ashirin din datai fadin duniya ita bata taba sanin dakwai su ba,

ZUCIYAR MUTUM BIRNINSAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن