🍀****🍀****🍀****
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
****🍀****🍀****🍀
*What a freaking love story📖*By ©UmmySaudat✍
®*Saudat Adam Isah*wattpad_ummysaudatt
11_
2days after,
wanda ya kama ranan wata Litinin,
da la'asariya sakaliya,
Misalin 5:05pm,
a can cikin huddled premises din BUK ne nai ta bin diddigi har na iya tsamo Najib,a tare da wani colleague dinsa,professor,wato Aisar,
dukkaninsu sun kashe kala a cikin shigar su me nuna tsuran gayu,ilimi da qasaitan dake tattare da kamalansu,suna tafe a sannu suna musanya fira har suka iso gaban gun da suka paka motocinsu,
"yauwa Prof,wai ya batun transfer dinnan naka zuwa Australia ne?",tmbyn Aisar ,
Najib ya 'dan bata fuska yana jingina kansa jikin motarsa me qirar BMW 6 Series kalan navy blue,
sannan yace,
"Guy yananan fa,
kuma banson tfynnan wlh",
Aisar yai 'yar qaramar dariya yace,
"lalle kam...,
it's freaky obvious fa,
just how much u re very obsessed with Kano city",
wani qasaitaccen murmushi ya shimfido labben Najib,
"nope,...just a special someone i badly cant just resist leaving behind","ko waye wannan de nasan baby ce,to meye ze hana ka tafiya da ita can din kawai",
daga hk sukai sallama ko wannensu ya kama Muhallinsa,
yayinda shi najib batutuwa da dama suka taru sukai masa rufduga a ka,ciki har wanda suka gama ta'dawa da Aisar,
daman cikin kwanaki ukunnan ba qaramin tough times suka saukar a garesa ba,ba qaramin tunani yaje yai ba,
nd obviously,all d credits goes to his ladylove,uwa uba har da gudunmawan amininsa Mahmoud ma,
a lokuta da dama yakan yima kansa kwadayin gyara lamuransa amman se yake ganin kaman komai ya riga daya gama ta'bewa,up to d extent din da yake tunanin kaman bazasu taba iya daidaituwa ba,
amman a yanzun yayi hands down kawai,har yakeson yai wani ho'b'basa kan qwatarma ingancin rayuwarsa 'yanci,dan sosai motsi zefi masa labewa
kuma duka wannan yake ganin se da wani wanda ze qarfafa masa qaimi,tarin abokansa bana kirkin da ya wuce Mahmoud,
shys daganan din gidansa ya nufa.
~~~kai tsaye Najib ya kutsa a cikin kaftareren living room din gidan Mahmoud Tanim Sarki,
wanda ya gaji da dangin kayan alatu,kai ilahirin gidan da kaa gani kasan ba qaramin kuka kudade sukai ba,banda sanyi da dadin Ac me cakude da daddadan qamshi babu abinda ke tashi,kai babu abinda ma yafi daukar hnkl irin qyalqyalin da chandelier din dake manne saman ceiling yake haskawa,
qanwarsa Fareeda ce a cikin gun,ta hakimce a kan daya cikin hadaddun leather cushion din gun masu kalan sea green,hannunta riqe da bowl din daya cika da oatmeal,
a yayinda ta tattare hnklnta ta miqasu kan tv plazman dake hasko wani tv series din philippines me taken Wildflower,bata fi 21yrs ba,kamar anyi kaki kamanninsu da Najib,sede ta qere shi a haske,irin fitinannen kyan nan na tsatstson fulani wanda ya samo musu asali daka bangaren mahaifiyarsu,
sanye take da wata 'yar iskar armless top da wandonta denim jeans,ya taimaka a gun qara bayyano cikakken chubby image din jikinta wanda kana ganinta kasan nera ya gaji da zama,kai har da wayewan da bokon duka babu sauqi,
ta daga kai ta kalli Najib da fara'a tana miqa gaisuwa,
memakon ya amsa mata ne ya jefo nashi,
"Ke ina mijinki?",ya fada fuska babu annuri,a karo guda ya zube nan saman sofa,
fareeda ta cabe baki tace,"ba'a sani ba",
qwalo idanu yai a cikin kallonta,
"take back what u just said"
ta noqe kafada a cikin kallonsa tana turo baki,
'dan yunqurawa yai kaman ze yo kanta,
ai a sittin ta tashi ta ruga,luckily,a nan tai karo da faffadan qirjin Mahmoud dake tahowa,ta maqale jikinsa tana marairaicewa,
"wani episode dinnaku knn",cewan Mahmoud all smiles yana kuma shigar da ita ruqonsa,"episode dinku de,
dallah ni ka saketa malam kazo mi magana",jin wannan yasa fareeda ta kuma shigewa jikin mijin tana murgada baki,
"baze sakeni ba din,
tunda ni a matsayina ta sib dinka,
ni ban isa ai addressing dina da wani sunan me dadi ba,
kai har ma nayi kadan a ambato sunan da ubana ya laqana min,sede ace wai wani KE,ai se ka...",zancen da bata qarasa ba knn ta saki Mahmoud tai ciki da saurinta,sabili da ganin yadda Najib ya tunkarota,
du ko da cewan duka wannan din a cikin gigin yaqe yake,
murmushi sukai duka shi da Mahmoud suna kalan caccafkewan da suka saba as usual,
de de nan suka zaune kan kujera a yayinda wata hadimar gidan ta bullo ta dire tray din dayai taf da tarkacen motsa baki,a fakaice Najib ya daga kai yana ganin yadda uban hadiman gidan keta kaiwa suna komowa,
'dan siririn tsaki ya auna ya dubi Mahmoud,
"mu fita waje mi magana man",ya qare zancen zumbur yana miqewa,
ESTÁS LEYENDO
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
RomanceStrictly inspired by TrueLove, extraordinary LoveStory,revolving around Islamic Values,Family goals,Friendship,Destiny nd a lot more, Showcasing dis in a super baffling way, #ZuciyarMutumBirninsa, sabon salon labari,wanda ya ke tafe da asalin qasait...