🍀****🍀****🍀****
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
****🍀****🍀****🍀
*What a freaking love story📖*By ©UmmySaudat✍
®*Saudat Adam Isah*wattpad_ummysaudatt,
7
a lkcn da motansa ke isowa gun su zahra ne ya samu daman zuge tint glass din motan,
qiri da muzu sukai da ita,
'ras',taji gabanta ya doka,
komai na jikinta ya tsaya cak sbd signals din da nerves dinta suka soma isar ma zuciyanta,
qwaqwalwanta ya dage yana kawo mata summary na each nd every memories din abinda ya wakana tsakaninta dashi,lkc guda wani abin da bata san ko meye ne ya dabaibayeta,kuma tuni ya bayyana kansa dumu dumu a saman fuskarta,
da qyar ta samu nasaran sauke idonta cikin nasa yayinda shi najib saman fuskansa ke bayyana murmushi me tafe da tarin so da qaunanta,
idanunta a rarrabe ta suri hannun khairat sukai gaba inda ko sauraron tmbyyin da khairat ke ta mata bata samu nutsuwan yi ba bare har ta samu bata amsa,
jin kanta take kamar ta arta a guje,du ko da cewan ta rasa dalilin daya hanata yin hkn,ban dama wata zuciyar dake ta faman azalzalanta,kan tai masa agajin tsayawa ta kuma yin tozali da wannan mutumin,suna tafe qafafunta na hardewa,
yayinda shi najib ya tsaida motannasa,sosai ya shiga damuwa ganin yadda abar qaunarsa ta maidashi kaman wani abin gudu,wai har ya za ai ya cire mata wannan feeling din,'guuff'
daga baya aka bigi motan najib,inda ace ba mercedes ba ce bama da tuni ta wuntsila sama,abinda ya dawo dashi kogin tunanin daya dulma knn,
yai saurin juyawa,
mamakin daya ziyarceshi me yawan gaske a lkcnda yaga gilmawan wata siffa me kama da mufidah ta gefensa,
"Mufidah",ya fada looking so out of d blue,har se daya mitsika idonsa hadi da sauke su gun da ta nufa,
gadan gadan ya ganta na dosan su zahra kaman wacce ke shirin zarewa,
sanin haukan mufidah ne yasashi gane abinda take da zumman yi,
tashin hnkl ya ziyarceshi a yayinda yaga ta tunku'da zahra ta baya,a bircike besan lkcnda ya fito daga motansa ba,
a haukace mufida ta ringa fincikar jikin zahra kamar kazan da ake figewa,tana dukanta ko ta ina cikin hucin masifa,tsananin rudani ya hana zahra tabuka uban komai,kawai cikin ranta a cushe da mamakin wannan cin zarafin dake faruwa da ita yanxun,
"har ni za'a ci ma mutunci aci amanata,wlh Allah se na illataki yanxunnan ba se an tafi ko ina ba,yadda ma baki isa yaa kalleki har yaji wani abun cikin ransa ba,wai da har zaki samu matsayin dazeta bibiyar ki hk,
dan shi najib nawa ne ni kadai,wallahil azeem dan ni kadai aka haliccesa",zantukan dake fitowa bakin Mufidah,kan kace me taruwan Bainan_Nasi,aka ringa jan ta,amman ina se ta kuma yin kukan kura ta cafko zahra,
'ni ku rabu dani nace',ta fada tana kuma qwace kanta,"tas",sautin daya bayar a lkcn da najib ya wanke fuskanta da wani kyakkyawan mari,wanda har seda ji da ganinta suka tafi hutun hucin gadi,
cikin zugin azaba tasa hannu ta tallabi kumatunta,har take qoqarin seta idonta kan gun da marin ya iso gareta,
amman ina kamin tai wannan yunqurin najib ya kuma daddagewa ya tsinka mata wani gagarumin marin,a qufule yasa qafa yai wani mugun kutu ball da ita,
"wa'iyazubillah",mutanen dake gun duk suka sha jinin jikinsu,sukai wani quri dasu ilahirin kallo ya koma kan najib,lalle yau ake drama bakin Kanopoly SOT,
najib din da banda hayaqin masifa ba abinda kansa ke fitarwa,
mufida da ke zube qasa kallon sa take a raunane tana kuka a hnkl fasashshen bakinta be bata daman bude bakin ba,kallon banza yai mata ya watsar yana maida idanunsa kan zahra,data gaza miqe tsayinta duka,wasu 'yammatu biyu da khairat suka daddafata,
kafaffun hawaye ne kawai keta mata ambaliya a fuska,fuskan da tuni yai wani jazur ya fita hayyacinsa,gaban goshintan dake fashe na tsiyayar da jini,wuyan hijabin dake jikinta a yayyage,
kallon kallo ya shiga tsakanin najib da zahrah,kallon da su kadai suka san fassaransa,
bil haqqi suke kallon juna babu wanda ya shirya qauqautawa,
"zahra",ya fada a sanyaye a lkcnda yai qoqarin daga qafafunsa na nufan gun da take,
wani irin zumbur tai cikin kidima,tasa ihu tana kuma shishshigewa jikin jama'an dake gun,
"da Allah ku taimaka ku 'boyeni,wlh ni tsoronsa nake",
ta iya fada a wahalce tana wuwwurga ido tsakanin jama'an dake gun da najib,
jin tsakankanin qirjinsa yai na neman darewa tsaban takaici,hkn yasashi juyawa gun a taqaice ya tafi cikin motansa,zafafan hawaye suka soma biyowa kuncinsa,yadda yake jin kansa a yanxun kaman yaje ya shaqe mufida ta mutu mus har lahira,hakanan tun kamin ya faro gini har ta rushe masa komai,
idanunsa tsaye gun har aka taran ma su zahra keke napep suka tafi,cikin tunanin yanxun har yaushe ze samu sauqin abinda yake ji,taya za ai ya samu daman dandana soyayyar da zuciyarsa ke muradin samu daga gunta,yanaso ya gyara abinda ya faru tsakaninsa da ita baya ga wani nan ya hada masa goma da ashirin,
idonsa naa gun mufida har yaga ta miqe a galabaice,dede lkcn yasa kai ya fita a hargitse, har gun da take ya je ya fixgo hannunta,fuu ya jata suka shiga motanta ya ja murfin ya rufe shi gam,
babu 'bata lokaci ya soma gwada abinda zuciyarsa ta ayyana masa,
wuyanta ya shaqe da qarfin da ya sa har ta soma jin qamshin barzahu,
har se da numfashi ya soma barin jikinta sannan ya saketa,
taa wani tsure,idanun sukai 'bula 'bula da ilahirin jijiyoyin jikinta,ta riqe wuyan tana tari a wahalce,cikin tashin hnkl take kallon sa da niyyan yin magana amman tarin yaqi sakinta,
"nd am not done with u yet,kika kuma yin gigin ko da kallon yarinyar nan ne,yaseen wlh se kin 'dandana ma aya zaqinta,
se na gwada miki asalin kalana,wanda baza ki ta'ba tsammanin ni din ke dashi ba,
u mark my word",
ya fada cikin hucin masifa hadi da fita ya banko murfin motan da mugun qarfi,
batare da ya tsaya kallon taron jama'an dake gun ba ya shige mota ya ja da mahaukacin gudu kaman wanda ke shirin tashi sama
~~
har se bayan magrib su zahrah suka isa gida,wani abu ta ringa ji gameda najib wanda batasan ya misalinsa yake ba,tanason tai kuka a lkcn ko dan taji sauqin abinda ke damunta amman se taga idonta ya bushe tunanin abinda ya faru ne kawai keta mata yawo aka,hk zalika zuciyarta a cunkushe take tunanin meye ya hassaso faruwan hkn,kurarin da mufida ta ringa yi da zantuka ta ringa jujjuyawa,
qarshe ta nemi kauda tunanin har ta sauke idonta kan khairat data kafeta da mayun idanu tanai mata kallon tuhuma,
"Yaya fadamin meye ya faru dazun?,
wacece wancar ?,
waye wannan?",
khairat ta jera mata tmbyy,
murtuk zahra tai ta hade rai,
"a word of advice,
wlh,tallahi,
kika kuskura kika fadama umma,even a tiny word a kaina da duk wani abun relating to this,
i promise,u will have to deal with me,and that's a warning,aikin banza,bigmouth kawai",
qare zancen tai tana jan wani shegen tsaki hadi da watsama khairat harara kamar idanun su zazzago dan tasan idan ba hkn tai mata ba din komai a kunnen umma,tabe baki khairat tai kawai ta fice a sanyaye tana qunquni,
se da zahra ta je ta gabatar da sallah'n magrib wanda da qyar take jure yin sujjada sbd ciwon dake goshinta,tai azkar hadi da karanta Suratul~Rahman sannan ta danji zuciyanta ya lafa,taje tai dressing ciwon dake goshinta,hijabin data cire dazun ta kalla tana kuma jin takaicin abinda ya faru dazun,
ga yadda take jin jikinta yayi tsami saboda gwabzan data sha a hannun mufida,
amman a dede lkcnda tunanin najib ya gifta mata se taji sanyi na ratsa qirjinta,wanda karan kanta na mamakin kanta,
da hk ta samu ta dauko wani zulmemen hijabin ta zulma hadi da rufe goshin yadda umma bazata fuskanci komai ba,ta dan gyara idontan daya wani kumburo ya canza launi da taimakon cometics,tai gathering courage,sannan ta yunqura ta shige dakin umma,kaman yadda suka saba afra da affan zaune qasan tabarma har da umma,
duka hnklnsu akan Qur'anin da umma take musu bita,ganin zahra yasa umma dan saurarawa tana mata kallon sororo,
"ina wuni",zahra ta miqa gaisuwa sum sum da ita,"zahra'u,meye nake gani hk",
memakon amsa umma ta jefo tmby tana qureta da ido da zumman gano abu,
dede lkcn khairat ta fado dakin tana ciccila idanu kaman wata munafuka,
"ummulkhairi,meye ya faru daku",umma ta jefama khairat tmby cikin damuwa dan ganin yadda 'ya'yan nata sukai wani tsuru tsuru dasu,
"am am umma ba bu komai fa",cewan khairat murya a harde,tana satan kallon zahra,
"zahra'u nace meye ya faru",
umma ta kuma jefama zahra tmby cikin tsiwa,
same answer din da khairat ta bata itama zahra,
hk Umma ta ka'da ta raya,qarshe ta rabu dasu,pls ur votes nd comments re highly needed,
zan dakata idan bukusoummysaudat,
SUNNYSMILES
YOU ARE READING
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
רומנטיקהStrictly inspired by TrueLove, extraordinary LoveStory,revolving around Islamic Values,Family goals,Friendship,Destiny nd a lot more, Showcasing dis in a super baffling way, #ZuciyarMutumBirninsa, sabon salon labari,wanda ya ke tafe da asalin qasait...