PART 01

4.7K 319 9
                                    

✨  *KALUBALEN MU* ✨

               *AMMIN SU'AD* ✍
                  
                       *1*

Shatuuu095@wattpad

KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
_United we stand and succeed our ambition is to entertain and motivate the mind of readers_

This page is dedicated to Umman beauty, Salma Hassan Kwalam ILYSM

Bismillahir Rahmanur Rahim

Juyi nayi  kan gado na, na shafa gefe na kamar yadda na tsammata baya nan din dai. Mika nayi gami da fadin "la'ilaha illa Allah Muhammadur Rasulu Allah" na tashi. Dirowa nayi daga gadon, na karasa gaban mirrow, dan kyauro na dauka na hade gashi na atsakiya, ba wasu kaya bane jikina don haka sai rigar barci kawai, wata doguwa na dauko na zura na saka hula.
  Dakin su Nana na shiga barci suke sadidan abinsu, na gyara kwanciyar Maama kana na sauka kasa. Kitchen na nufa na dora tea, parlour na fito komai fes! Na wanke baki na da fuska ta a sink din dining. Kitchen din na koma tea din ya tafasa, na janyo wani tea flask baki mai fulawoyi golden da mugs dinsa guda daya babba sai tray da tea spoon. Na hada komai  na jera kan tray din. Side din Ahmad na nufa tun daga parlour na jiyo motsin sa da alama gymming yake. Rigar saman na cire daga ni sai short wanda ya rufe cibi na zuwa kusan guiwa ta, sai yar half vest mai hade da bra, na cire hula ta kamar yadda na ga matan turawa nayi da mazajen su wata kila nima in nayi zan iya jan hankalin sa. 
Yana press up don haka da sauri na na karasa naje na aje fuska ta daidai inda zai aje bakinsa.  Da sauri ya mike gami da hade fuska "ke kam you'll never be serious, na rasa yaushe zaki gane you're not of that type?" Ban ce masa komai sai dai jikina yayi sanyi sosai. Kan bike ya hau, na nufi gurin tea din ina hadawa ina masa hira amma "umm" ko "A'a" shine amsar kawai. Dana gama hadawa na kai masa ya amsa ya shanye kana ya ci gaba da sauri sauri sai da ya hada gumi sosai sannan ya dira. Kafin na sako rigata har ya wuce ni.
Shiga ta parlour na iske su Nana suna kallo da murmushi suka tare ni "_mummy good morning" nace "morning... Kun yi wanka da brush ko? "Eh" suka amsa min.
Sama na hau na tafi daki na wanka nayi ba wata kwalliya nayi ba. Wando nasa three quarter  sai riga harmless, an rubuta kiss da alamar lebe. Kitchen na dawo na dora mai tuni dama tun dare na fere dankali na saboda haka da mai yayi zafi na fara suya. Da na gama na soya kwai. Na hada komai kan dining, na dawo parlour "Nana, kira Abba kice na kammala breakfast" tace "to". Shima dai irin shiga ta jikinsa, muka zauna tare.
Mun fara kenan wayar sa tayi ringing ya kai hannu ya dauko "Hello.... Malam Bello..... Ok......... To..... Insha Allah........." Tun ina sauraron sa har na kyale shi na maida hankali na kan su Nana, daga loma daya bai kara ba, sai ya muke yana ci gaba da waya da Malam bello.... Kamar kullum naji ba dadi amma na dake kawai. Da muka gama na kwashe kayan, su Nana suka tafi daki cikin dan lokaci sun gama shiri sai makaranta. Turare na dauka a falo na fesa musu tare da fadin "Allah ya kiyaye my babies ayi karatu sosai "amin" suka amsa Maama tace "Mummy, Daddy fa?" Nace" yana sama aiki yake kuje kawai" har kofar parlour na raka su, ina tsaye Malam Tanimu ya wuce dasu makaranta.
Sama na hau da breakfast din,yana tsakiyar gado da system a hannun sa yana ta aiki. Na dan shagwabe "All  works and no fun makes my Ahmad boring" murmushi kawai yayi ba tare da ya ma kalle ni ba yace "I admit" nace" ga abinci na kawo maka"
"OK.. Kinga fa na manta shaf!.... You know what?"
Da murna nace "A'a"

"This week kayana zasu karaso, na kusa hada babban mall dina na Abuja, kinga daga nan sai maganar polytechnic din da nake so na gina private"
Dama indai Ahmad yayi murna to fa maganar aiki ce, duk da haka dai na rungume shi har kiss nace " I'm so much proud of you"  Bai ce komai ba na bata rai, "kai baka iya maida kyauta ba" dan tsaki yayi gami da murmushi yace "shi kiss abinci ne da zaa yi tayi persistently? Sake min anan to on my behalf" ya fada yana nuna dayan kuncin sa. Tashinayi nace "naki din"
   Abinci na zuba masa, ina ta masa hira, yana aiki yake daukar kamar guda shida ya cika bakinsa, don ya dade yana tauna, nace "ka bar aikin mana... Ka gama cin abincin" yace "so nake na gama yau kam gida zan wuni" Har da tsalle na duk da nasan bata sauya zani dai. Nace "bara na hado maka banana shake " " to" kawai yace dani.
  Sai da na kare fasaha ta na kuma tabbatar da yayi dadi sosai, na hado a wani jug mai kyau wanda kallonsa ma kawai zai iya saka mutum mance duniyar sa.
  Ina shiga na same shi yana saka kaya yana ta waya, na tsaya ina kallon sa. Ya aje wayar " Maryam, zan je kwari yanzu atampopi na sun karaso yanzu daga nan zan je gun Alhaji Salahu" jiki na a sanyaye nace "to" Bai kuma cewa komai ba ya kwashi takalmi, agogo da kuma hula a hannu, bene bibbiyu yake tsallakewa. Kafin na karasa gunshi har ya tada mota, yana shirin ficewa.
  Duk yadda naso daurewa amma sai da nayi hawaye, na kwashe kayan. Da rana ma indomie kawai na dafa na aika ma su Nana. Sai yamma suka dawo, lokacin ina kitchen na dora girkin dare. Tuwon shinkafa zan masa miyar agushi wata kila ko zai ci, muna ta hira har na kammala, miya ce kawai ban sauke ba. Na je nayi sallah na dawo na karasa girkin. Na jera komai a dining, wanka muka yo kana muka dawo. Shiru bai dawo ba har tara, nace muci abinci kawai mu kwanta. Da kaina na raka su daki na yi masu addu'a na fito na tafi.
Abincin na kwashe na kai sama, har na gaji da jira na tashi nasa kayan barci.
Kayan ciki bra ce sai pant sai kuma ta saman. Ina zaune har sha daya,  sannan naji karar bude gate dinsa. Daki na koma na sake aman turare yadda nasan ko dutse ne shi dole ransa ya tabu, wata kila Allah ya karkato min hankalinsa.  Niki niki da ledoji ya shigo har guda uku, na hasasho ya yaba da wankan amma ya gimtse, ya zube su parlour sannan ya shiga ciki. Cikin salo na rage masa kayan,  wanka yayo ya fito yaci tuwon. Sai da ya gama muka tafi don kwanciya.
Sai da muka kwanta ne nayi wa kaina makwanci a kirjinsa cikin kunne na yace "kin yi kyau sosai sai dai a gajiye nake sosai M C amma da na baki tukuici amma still....."
  A zato na wani wani abun da nake buri zai yi amma ina? Kawai romance ne wanda ke sake daga hankali na amma shi nashi ganin yayi wani appreciating ne. 
Da safe tun asuba ya fara shiri ni kuma na fara abinda na saba din wato kuka amma wannan karon yafi na kullum. Tun yana basayarwa har ya kama hannu na tare da rungume ni "again....? Baki gajiya ne da kuka sai hawayen ki ya kara ne? Duk tafiya sai kin yi wannan kuka kuma ni yana daga hankali na. Just be sincere me kike so?" Kallon shi kawai nake ina kunyar me zan fada masa, a gani na yafi kowa sanin damuwa ta, yaushe rabon shi dani? A kalla zamu yi wata fa ko ma fi amma shi hakan sam bai dame shi, in bashi da bukata ai ni ina da shi ko?..... "Ina jinki" da ya fada ya katse ni nace " zan yi missing dinka... Wani karon don Allah ka bani lokacin ka na roke ka" yace "I promise"
    Kafin shida ya fito, ta dakin su Nana ya biya yayi masu sallama, suna shirin makaranta.  A parlor ya nuna min kayan da ya shigo dasu jiya yace " ga kayan ku nan" nace "mun gode, Allah ya saka da alheri"
  Har mota na raka shi, Malam Tanimu ya jashi zuwa airport inda zai tafi Lagos. Na dawo na hada yan makaranta, zuwa bakwai har mun kammala komai, na rako su zuwa mota inda Malam Tanimu ke jiran su. Sai da suka tafi na dawo na gyara gidan.
Sama na koma na duba kayan, ni atampa ce guda biyar sai lace biyu da material uku, su Nana ma haka amma su maimakon atampa sai ya saka masu English wears, na tabbata kayan sa na jiya da suka karaso shine ya dauko mana su.
Daki na koma na kwanta kan gado tunani burjik a raina, ko yaushe Ahmad zai fuskance ni a rayuwa ta ne? Ya gane lokacin sa, kulawar sa, soyayyar sa, gami da shi nake so ba wai tarin dukiya ba. Hawaye ya kwaranyo fuska ta na tsananin tausayin kaina tare da tuno wasu lamura da suka shude cikin Rayuwar mu.................


Shatuuu♥️

KALUBALEN MU! Where stories live. Discover now