PART 12

1.4K 160 5
                                    

✨ *KALUBALEN MU* ✨

     *AMMIN SU'AD* ✍

12

🌈 *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*

"Nafisa, na gode sosai kuma insha Allah zan rabu dashi saboda mai sonka shi yake dora kan hanyar daidai na kuma yarda dake ba zaki taba cuta ta ba"
"Shike nan na gode nima da bani lokaci da kika yi kika kuma saurare ni"
Tare suka jera har aji basu jima da zama ba Malamin ya shigo ya fara lectures. Tasan shi zai zo daukar ta don haka kafin yazo ta tafi gida ko da ya kira ta ta shaida masa tana gida bai ji dadi ba amma da yake ya goge sai ya nuna mata babu komai.
Hajiya ta matsawa ta gyara mata tata motar don ta gaji da hawa Napep. Ai kuwa ta aiko aka gyara dama ba wani gyaran kirki bane kawai dai itace bata maida hankali a gyara mata ba.  

***     ****        *****

Rabo na da Ahmad na manta ya sake linkaya cikin aiki ya manta dani sai dai kawai nayi ta jin alert na kudade suna shigo min daga gunshi, tuni dama ya kammala bani kudina ni kuma na bawa Yaya Muhammad babban dan dakin mu nace ya saya min hannun jari dasu tunda dai ni nawa mijin ya hani ni business.
Ban wani cika damuwa da  rashin sa ba tunda na samawa kaina lafiya yanxun sai dan abun da baa rasa ba. Amma abinda yafi damu na shine yawan ciwon mara da nake fama dashi ina kuma ta yawan gwada magunguna da dama amma babu wani ci gaba, ga kuma baya na ma dake damu na sosai shi ma.

***      ****        *****

"Ralyna, kin guje ni kwana biyu, ni kuma ban san abinda nayi maki ba ko kadan.. Kina ta daure min fuska baki so na rabe ki why?"

"Aure nake so muyi Auwal"
"Aure kuma?"ya fada cikin firgici sai kuma ya dake.
"Aure fa nake nufi...., na gaji da wannan kazamar Rayuwar da muke yi ya kamata mu dakata hakan nan tunda muna son junan mu me zai hana mu yin aure kawai"
"Ke yanzu ni dake wa ya isa aure? Ko makaranta fa bamu gama ba har ni kaina.. To mahaifina ba ba zai barni nayi aure ba tunda ina Da mata biyu sama na da basu yi aure ba balle kuma ni namiji"
"Amma ai mun isa neman kanmu ko? Ni gaskiya in dai ba don aure muke tare ba kawai gara mu rabu"
      Shiru yayi bai taba tunanin zata yi masa haka ya rabu da ita haka kawai bai cimma burinsa ba ai da sake gara ya rabu da rayuwar sa akan ya rabu da ita shi kam. Gumi yake ji don dabara ta kwace masa, yana kallo ta dauki jakar ta ta bar gurin.

Ya dade kan gado yana tunani kafin daga bisani ya gano abun yi. Murmushin nasara yayi don wannan karon bata isa ta kufce masa ba ba kuma dogon lokaci zai dauka har ya tsaya garin kallon ruwa kwado yayi masa kafa. 

Kwana uku tsakani ya nemi ta sau biyu yana kiranta taki dagawa har washe gari ya kuma tabbata ta gani kawai ki ranshi ne taki dauka kuma taki biyowa.
   _Assalam_
    _Gimbiyar Mata_
      _Ina mai bada hakuri akan laifin da nayi maki wanda yasa kika ki daukar wayata. Don Allah kiyi min afuwa ba don ni ba sai don girman Annabi (S. A. W) kuma ina da wani kyakkyawan albishir da zan yi maki_

Ta karanta yafi a kirga wata zuciyar na son yadda da sakon wata kuma na kwabarta anya ma wani shiri yake dashi akanta ba? Ita dai tana tsoronsa sosai. Ba jimawa sai ga kiran shi ya shigo dagawa tayi don jin da wacce kuma yazo yanzu.

"Nasan nayi laifi ayi min hakuri Ralyna, a zato na zan iya rabuwa  dake amma zuciyata, gangar jiki na da kuma komai nawa sun ki yarda hakan, hankali na ya tashi bayan tafiyar ki tilas na tafi Kaduna na shawo kan Mummy da kyar ta samu Daddy suka yi magana shi yasa kwana biyu kika ji ni shiru. Amma yanzu Alhamdulillah, nan da sati uku manya na zasu zo da fatan zaki amshe su ko? Abinda zai hana su zuwa ma don yanzu Daddy zai yi tafiya ne can America amma da ya dawo zaki gansu"
  "Allah yasa dai ba tsara ni kake yi ba"
"Wane ni?...... Ya kamata ki gane bana daga cikin masu karya"
"Haka ne.... Yanzu yaushe zamu hadu?"
"Gobe a bakin gate na school dinku"
"OK bye baby"
"Bye My love".
    Ta kashe wayar tare da shiga toilet don yin wanka.

Tunanin ta wa zata fadawa wannan labari, Alhaji ko kuwa  Hajiya? Kai sai dai shi don bata mance artabun ta da Hajiya akan Ibrahim.
   A dakin shi ta same shi yana shan iska, kila dawowar shi kenan daga shagon da Hajiya ta bude masa kenan yana saida kayan sanyi wanda a karshe ita zai kawowa cinkin ita kuma ta yaga masa wani abu a ciki sau da dama takan jiyo musun su in zata hana shi wani abu tace sai yayi mata tausa a parlour ba tare da jin kunyar idonta ko na masu aiki ba zai hau yi mata, don shi kam ya zama rakumi da akala.
  Gefen shi ta zauna yace
  "Raliya, an taso daga makarantar"
"Eh" ta bashi sannan taci gaba "Alhaji dama magana nazo muyi da kai" "Baki ya shiga washewa yana fadin ina jinki yata. Bata boye masa komai game da zancen da suka yi da Auwal ba. Shiru yayi kafin yace
  "Amma kin samu Hajiyan tukun?"
Kai ta girgiza alamar A'a
"To ki same ta kuyi magana sosai duk abinda tace ai shike nan tunda ita ce mai wahalar"
  Dama ta san zaa rina wai an saci zanin mahaukaciya. Kuma kuwa zaton ta ya tabbata don haka bata sake komawa ta kanshi ba ta tashi ta tafi tana adduar shiriyar Allah ga wannan mahaifin nata.

Inda yace su hadu nan taje ta same shi, a motar shi suka tafi yau kam har da Hamida suke tare. Suna tafiya aka kira shi wayar ya dauka yana kwatancen daidai inda suke yana fadin ya kusa karasawa. A kan hanya ya tsaya ya saya masu lemuka, shi ya dau baki ya sha ita kuma Hamida ta sha Fanta. Ganin harda gwaninta Maltina yasa ta daukar daya ta sha.

Suna ta hira jefi jefi abinsu tare da Hamida wanda ba sosai suke gane kan gadon zancen ba sosai.

Kamar cikin mafarki taji ana kokarin kusantar ta, a gigice ta farka gaba daya. Bata san sa'ilin da ta hankade shi ba tare da fadin
   "A'uzubillahi minnas shaidanur rajim!!!".
   Kayanta ta fara laluba cike da wani irin bakin ciki da kuma da ta sanin abinda suka bata ta sha. Kuka ne ya kwace mata
"Auwal, Zinar ta zama dole ne! Da sai ka bi kowacce hanya don ganin ka aikata masha'a dani? Ka cuce ni ka kuma cuci soyayyar mu..."
Tana kokarin ficewa a dakin ya finciko ta tare da fadin
  "Dole ne na cika muradi na akan ki Rakiya dole ne wannan ki je na tabbata da kafafuwan ki zaki dawo"

A parlour ta samu Hamida da wasu maza suna ta busa shisha. Da sauri ta tari gabanta
  "Bestie,lafiya kuwa?". Hankade ta kawai tayi, ta fice a gidan gaba daya.

Tana isa gida dakin ta ta wuce straight sai gado, kuka tayi har ta gaji bata taba tsammanin hakan daga gurin  Hamida ba sai gashi yau ta yaudare ta ta kuma cuce ta. Wayar ta ce ta sanar mata da shigowar sako don haka ta shiga ta duba.
Auwal ne yayi mata magana ta WhatsApp ya turo mata videos guda biyu. Ta bude dayar magana ce kamar haka
    _Da zaki yiwa kanki gata to da kin dawo gare ni, kin taimaki kanki gurin bani abinda nake so, in kuma ba haka ba to ki shirya yaduwar video din dake kasa_
   Da sauri ta yi loading video din. Video yayi mata a lokacin da ya gama raba ta da kayan jikinta gaba daya ya kuma baje ta kan gado a hankali tana jiyo saitin dariya Hamida.
Kanta ne ya kulle gaba daya kenan da niyya suka yi mata wannan abun? Babu ko shakka cikin wannan lemon suka zuba mata wani abu wanda ya gusar da hankalin ta gaba daya ya kuma saka ta barci mai nauhin gaske. 
_Allahumma ajirni fi musibati waklifni khairan minha_ shi kadai take iya maimaitawa.
Wani message din ne ya sake shigowa wayar ta makamancin wannan daga Auwal.

_me kika yanke dawowa gare ni ko kuwa yaduwar tsiraicin ki?_

To fa wanne Raliya y zata saba komawa ko kuma yaduwar video?

_*AMMIN SU'AD*_ ✍✍


*SHATUU* ❤

KALUBALEN MU! Where stories live. Discover now