✨ *KALUBALEN MU* ✨*AMMIN SU'AD* ✍
🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
*24*
Sai goma da mintuna naji motsin shigowar sa. Ina nan zaune a parlour na rasa me zan yi, nayi kuka har na gaji idona yayi luhu luhu saboda kukan da na sha na more abuna babu wani abu da yake nuna cewa zan zauna gidan Ahmad, na riga dana gama sirewa har sai da ya shigo ya same ni ba wata magana muka yi ba illa ya ce dani. "Kayan da ki ka gama hadawa ki janyo su corridor Mallam Tanimu zai zo ya dauka" "To" na iya cewa dashi kawai. Ya juya shi kuma ya fice gaba daya.
Ban bata lokaci ba na fiddo kayan na kuma je daki na same shi don sanar dashi na kammala komi. Rubutu yake a wata farar takarda, take zuciyata ta bani amsa takardar saki ce ma na sani. Wani hawaye ne mai zafi ya biyo kumatu na, wanda yasa ban ma iya sake yi masa bayani ba na fito.
Na jima kafin na fara jiyo muryar Mallam Tanimu yana fadin "..... Har wannan takardar Alhaji?" Ban ji me Ahmad din ya ce masa ba kasancewar shi baya magana da karfi.Ina idar da sallah ya shigo a tsaye yace dani "ki shirya kafin shida" kafin na amsa masa har fice. Kamar kar nayi wanka sai kuma na tashi nace bara nayo na karshe don in ya sake ni kila zan iya kaiwa kwana bakwai ban warke zuciyata saboda damuwa.
Ba wani jimawa nayi na fito. Atampa na saka riga da zani plain, na daura dankwali sannan na dora gyale na akai. Glass dina na zura bayan na goge wata kwalla, tun safe nake ganin jiri, wata kila in na saka glasses din zan ga daidai.
Ina nan tsaye ya shigo sai da ya qare min kallo sannan yace dani "fito mu tafi" bai jira amsa ta ba ya fice ya bar ni tsaye. Na karewa daki na kallo sannan na tafi, shike nan yanzu na bar daki na zan koma gidan dana baro ina kuka yanzu kuma ina kukan komawa cikinsa.
Ban jima ba na fito, tuni shi har ya sauka kasa. Can na ruske shi su Mallam Tanimu nata zabga masa godiya. Isowa ta yasa ya juya gare ni "Hajiya, mun gode kwarai da abinda aka mana Allah ya saka da alheri ya biya. Sai dai duk ka hukuncin da Alhaji ya dauka bai mana dadi ba amma muna fatan Allah ya sanya hakan ya zama alheri. Zamu kewar alherin ki" wani irin lugude naji zuciyata tana min, ai shikenan kashi na kuma ya bushe, amma Ahmad bai kyauta min ba, hatta da Driver sai da ya fadawa ya sake ni?.
Wasu hawaye naji suna sakko min wanda suka hana ni furta ko kalma guda. Ahmad ne yayi yunkurin Kama ni ya juya ga Mallam Tanimu yana fadin "je ka kasa a bude gate din mun fara sakin jiki" ya karasa fada yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa.
Shi ya kama hannu na muka shiga mota. Mallam Tanimu shi yake jan mu har _MALLAM AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT._ Yana kai mu ya koma. Cuku cukun yayi tayi ni dai ina gefe ina ta kallo ban kuma san me yake faruwa da rayuwata ba. Ina nan zaune ya dawo dauke da leda a hannunsa ta _chopsticks_ ruwa, lemo da glazed doughnuts. "Bismillah..." Ya fada yana zama gefe na. Kasa karba nayi illa zuba masa ido nayi, ina son sanin me yake nufi dani ne baki daya. Saki na zai yi ko kuma wani abu zai yi min ne? "Malama ki ci abincin mana, ni din kamar wani bako?" Ido na sauke kasa wanda hawaye ya biyo baya. "Na koshi" na furta a hankali. Shima bai ce komi ba, bai kuma sake fadar wani abu ba. Har lokacin tashin mu yayi. Wata tsohuwa dake share share ya kira ya damka Mata ledar yace taje taci abinta.
Karfe tara muna cikin jirgi wanda ga seat dina ga nashi side by side. Muna nan zaune jirgi ya lula damu ba tare da nasan ina muka dosa ba. Kamar awa biyu hostess yazo dauke da menu na kowa abinda yake so. Ni kam ruwa nace zan sha, shi kuma Ahmad yace a kawo masa coffee. Ina nan taje ta kawo min ruwan, abinda yasa na amsa tun jiya da safe babu komi cikina ko da ruwa ne, nasan ina jin yunwa sosai amma bani da nutsuwar cin abinci.
Tumbler uku na sha a ciki na, sannan na dan jingina da kujera ta sanyin na bin gabban jikina. Ba kuwa mu wani jima ba naji cikina yana hautsinawa, dame shi nayi ina jin yana kullewa. Ba kuwa jimawa sai na fara jin amai, da gudu na tashi na yi toilet naje nayi ta kelaya shi abuna, sai dana gama sannan na jingina da bango ina maida numfashi na. Ahmad ne wanda ban san ya biyo ni ba yake tayi min sannu tare da kamo damtse na. Duk da yanayin da muke hakan bai hana mu sake kallon juna ba na tsawon lokaci, kafin shi ya janye nashi idon yana fadin "matso a kuskure bakin"
Shigar ruwan cikin bakina yasa wani aman sake taho min, nan shima na shiga kwara shi wannan karon har sai da ya rike ni don yi nake tamkar zan amayar da sauran kayan cikin nawa. Shi ya taimaka min na dawo seat dina ya kwantar dani jikin seat din tare da rungume hannayena a kirjinsa yana shafa kaina. Ban kuma jimawa ba sai wani aman. Haka muka ta zarya toilet har abun ya janyo hankalin hostess din da suke ta kai kamon bawa mutane abinci. Ahmad ne ya yi wa daya bayani don ta kira nursing service na flight din.
Lokacin da tazo da kit dinta ina lafe jikin Ahmad jikina gaba daya ya saki saboda rashin kwarin jiki. Dudduba ni tayi tace a hado min tea a kawo saboda kamar akwai yunwa a jikina. Badadewa kuwa aka kawo min. Da taimakon Ahmad na sha duk da sai da ya sha fama kafin na karba na kurba. Ina gamawa kuwa na fara kokarin wani, wata tasa ta bani nayi aman a ciki, ta dauko wasu magungunan ta bani kafin mu sauka amma duk a banza babu wani ci gaba.
Bayan shudewar awanni jirgin _Turkish Airline_ ya sauke mu a _Istanbul Airport_, tuni dama an kira Ambulance ta babban asibiti. Da taimakon Ahmad na iya saukowa zuwa Ambulance. Su suka taimaka min na shiga, tun lokacin suka fara bani taimakon gaggauwa. Kafin kuwa mu karasa asibitin tuni barci ya soma awon gaba dani.
Farkawa nayi na ganni a bakon guri, sai lokacin na tuna da abinda ya same ni. Ashe asibiti ne, kuma ganina sanye da kayan marasa lafiya. Da kyar na yunkura na tashi zaune ina ta kalle kallen yadda tsarin nasu asibitin yake.
Kamar minti goma tsakani sai ga Ahmad ya shigo, gani na zaune yasa shi karasowa da sauri yana fadin "kin tashi?" Kai na gyada masa. Kujera ya ja ya zauna yana rike da hannayena. "Sannu kin ji" ya fada yana dan matsa hannun. "When last kika ci abinci?" Ya fada cikin wata siga hakan ya tuno min da wani lokaci can baya. Sadda kaina kasa nayi sai hawaye...
"Yaushe ne zaki saita rayuwar ki? Yaushe zaki mance abun da ya faru? Wani lokaci kika daukar ma zuciyoyin mu don ki bar su su huta? Ki sani cewa kuka damuwa duka basu yayewa mutum wani sai ma su kara. Shin kinsan yanzu haka me ke damunki? To ulcer ga BP din ki very high. So kike sai kin kashe dukka jikin ki sannan ne zaki huta. Na roke ki da Allah da kin mance komi tunda tuna shin ba zai qare mu Da komi ba. _Abin da ake gudu (Batul Mamman)_ ya riga ya faru sai dai mu kiyaye gaba kawai. Let the past be, mu kalli gaba. And for the last time na roke ki da ki yafe min laifuka na, na sani dukka wannan abubuwan suna faruwa ne sila ta...." Hawaye naji yana zuba a idona, ban bar shi ya qarasa ba na dago hannayen sa na sumbata. Shima daya hannun yasa wajen share hawayen idona. Shigowar likita tasa na sake shi duk da shi bai ma kula ba, kasancewar su hakan ba komi bane a gun su. Dudduba ni yayi yace na samu abinci naci tukun.
Yana fita Ahmad da nufin hado min abinci sai ga Nurse ta shigo dauke da tray a hannunta. Ta ajje shi, ita ta taimaka mun nayi brush sannan ta jawo min abincin gaba na don nafi dadin ci sosai. Da taimakon Ahmad na ci, dama fresh milk ne sai farfesun cray fish mai romo da kayan kamshi.
Kwana biyu aka sallamo ni, ko _Richmond Hotel_ da muka yi booking bamu karasa ba saboda lokaci muka wuce can.Tsirarun awanni ta sauke mu a _WASHINGTON DC INTERNATIONAL AIRPORT_. Mamaki ya kama ni sosai na ganin mu anan to me muka zo yi? Ko da aka gama clearing mu, taxi muka dauka dai _foggy bottom_ a harabar _Watergate Hotel_ . Da taimakon driver din duka muka fito da kayan mu na ajje nan, gaba daya sai na zama yar kallo ma tamkar ban zo gurin nan ba. Komi Ya canja an sake canja fasalin komi ya sake zama na zamani. Ina kalle kalle naji an kama hannuna na juyo na kalle shi murmushi ne dauke a fuskar sa yace "muje ko?" Binshi nayi a baya har muka isa reception. Zaunar dani yayi yaje ya amso card din dakin da yayi mana booking online. Hannu na ya kama har sama na biyu.
Sai da na shiga dakin sannan komi ya dawo kaina, Shekarun baya suka dawo kaina tarwai! Kallon shi nake kafin na tafi da sassarfa naje na rungume Shi ina son sanin maanar wannan abubuwan da yake min sosai. Bai ce dani komi ba, sai dana gaji don kaina na sake shi.
Wanka ya saka muka yi, Shi ya riga ni fitowa shi sai da na dan kimtsa bandaki sannan na fito. Har ya fara saka kaya abinsa nima nazo na shirya muka tafi tare dashi. Doguwar riga ya bani baka sai coffee gyale da na yane kaina dashi.Ban san ina zamu je ba, Muna take tafiya a kasa yana ta nuna min gurare da dama wanda ban gane ba ya sake min bayani, sosai aka sake zamanantar da komi.
Ba jimawa sai gamu a layin _Georgetown University_. Kallon shi nake tayi kawai. Kallo na shima yayi yace "yunwa nake ji" kallon shi nima nayi. Ta _Luke's Lobster_ muka biya yayi order mana Chinese rice da salad, sai strawberry shake. Da akwai alamar sabo a tattare dasu don naga sun gaisa sosai. Nima na saki jiki naci abinci don akwai yunwa sosai a tattare dani kamar naci babu haka nake ji.
Sai da muka kammala sannan muka tafi. Cikin makaranta muka shiga hakan yana ta tuno min da tsohuwar rayuwar mu. A gaban *Maryland Book Bank* muka tsaya, kamar daga sama sai ga wata baturiya ina son gasgata kaina amma ina sai da tazo daf dani sannan na gasgata idona tabbas kuwa itace ban sadda nace *Linda!!* itama da saurin ta karaso ta rungume ni tana fadin *Maryam!!* sosai naji dadin ganinta. Shekara nawa ai lokacin da tsayo sosai. Ahmad ne ya kalle ta yana fadin "Kin ganta nan gaba daya ta canja min shi yasa na kawo ta na kira ki don kawai ki sake hada mu ina son ta mance komi musake sabuwar rayuwa tamkar yau muka fara ganin juna" dariya muka yi gaba daya ta kalle ni ta kalle shi tare da kama hannayen mu ta hada tana fadin " _meet one another. Maryam.... Ahmad_" dariya muka yi saboda ta tuna mana lokaci na daban kama ni yayi ya rungume ni tsam! Tare da furta "I love you Mairo!" Dan dukan shi nayi a kirji nace "I love you too" shima cizon kunne na yayi yana fadin" ki mance komi Mairo mu sake sabuwar rayuwa tare da ke". Hannuna ya kama muka fito tare da Lindahar ta hau taxi muka tafi muma. Taxi muka hau yanzu muma har dakin mu.
Ina shiga na cire rigata na sauya kayan da na gani a dakin wanda na san zama na suke yi. Kan gado na kwanta shima ya kwanta tare dani muna hira jefi jefi sosai kuwa nake jin dadin kasancewar mu dashi. Can ya dan kwanto dani jikinsa yana fadin "kina jina ko Mairo? Na yanke wani abu duk da nasan ba lallai bane yayi maki dadi amma nasan domin mu ne baki daya.
Na yanke shawarar dauke ki gaba daya daga Kano zan maida ki can Kaduna ki zauna tare da Mummy a sabon gidan dana gina part dinki daban nata daban kawai dai ina so ne na hada ku guri guda don nima na samu saukin zirga zirga gaba daya. Kuma tunda kina da yanayin da koda yaushe kike bukatar attention wasu lokutan zan iya yin bulaguru kinga zan tafi sai ki bar su gun Mummy nan ne baki daya bamu da rashin tabbas na tarbiyar su. Amma kiyi hakuri.
Sannan abu na biyu shine yanzu a matan duniya ke daya kawai nake so yara na kuma sun ishe ni ban san nan gaba mai qaddarata zata kaya ba, ta yiyu ban ji ina son sake samun wasu yaran bayan naki wanda hakan yana iya janyowa nayi aure! Ta yiyu har abada naji ban canja ba. Ni dai kawai ba zan maki alqawarin ko daya ba kin gane?"
Shiru nayi na gaza amsa shi zancen shi na farko bai same ni ba duk da nasan yau da gobe sai Allah, zama na da uwar miji amma na biyun in ya kasance gaskiya ba zan ji dadi ba. Tashi nayi ina kallon cikin idonshi kafin na kankame shi ina kuka nace "hakan ma na gode ko yanzu kayi min hallaci kuma ban damu da auren ka ba don dama nasan duk wanda ban ketare iyar Allah dole yayi ta ganin ba daidai ba. Sai dai ka sani ina son ka kuma ina tsananin kishin ka......" Hannunsa yasa ya rufe bakina yana lallashi na a hankali yana dan bubbuga baya na har nayi shiru.*_SHATUU_* ❤
YOU ARE READING
KALUBALEN MU!
General FictionKALUBALEN MU! It's all about masturbation..... How does it feels that you have desires, sexually aroused and your parents said you must finish your A level before aure? How do you feel when lust covered u and your husband said business first? How do...