PART 15

1.5K 170 8
                                    

✨ *KALUBALEN MU* ✨

           *AMMIN SU'AD* ✍

🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

                   *15*

Kuyi hakuri na samu issues da numbering ne am a bit confused, last page supposed to be 14 so take this as 15. Thank you so much darlings for always being there for Shatuuuu

Ta jima a wurin zaune tunanin ta bai wuce ta yaya zata fara baiwa Hajiya hakuri akan laifin da tayi mata? Kuka itama ta sha daga bisani ta mike ta yi kundunbala.
A hankali take iya tura kofar kamar mai tsoron kofar. Hajiyar ta hanga can karshen gado ta kifa kanta a kan pillow sai dan sautin kuka da take iya jiyowa. Wani abu ne mai daci ya tokare mata baki da makogaro gabanta kuma ya fadi sosai. Ita ba jahila bace bata mance hadisin da Annabi (SAW) yace "..... _fushin Allah, hakika yana daga fushin iyaye_....... Ita kam yaya zata yi? Bata taba ganin kukan Hajiyar ba tun tashin ta sai yau kuma duk a dalilinta. Ta kuma tabbata tana fushi da ita wanda hakan ke nuni da Allah ma yana fushi da ita.
Gaban gadon ta karasa tare da dafa tace" Hajiya, nasan na aikata ba daidai amma don Allah ki yafe min kada kiyi fushi da ni na hada laifi biyu a gurin Allah...." Katse ta tayi da fadin"Har dai baki fita a daki yara a to zan maki baki". Take kuwa ta mike ta bar daki ranta na suya. Dakinta ta nufa tayi mai Isar ta sannan ta hakura. Salloli ta tashi tayi tana neman gafarar ubangiji ta gami da tsinewa Hamida da ta kaita ta kuma baro.
   Da safe jiki a sanyaye ta tashi tayi shirin makaranta, banda submitting project da ba zata je school ba yau amma tana son ayi mata approving chapter din da take. A falo ta iske Hajiya da Alhaji suna karyawa tare ta gaida su, Alhaji ne kawai ya iya amsawa yayin da Hajiya tayi iska da ita.  Gefe ta samu ta zauna don karyawa. Tana karbar tea ta kunna data dinta burin ta taga karfe nawa supervisor dinta zai zo. Fisge wayar taji anyi, ta daga ido taga ashe Hajiya ce. Bata ce mata komai don neman sulhu take yi da ita.  Da ta gama da kyar ta iya hada kalmomin "Hajiya, mota ta babu mai" "Bani mukullin" ta fada tana miko mata hannu. Babu musu kuwa ta mika mata. "Ai tunda nayi maki gata kike wulakanta ni to zan amshe duk abinda na baki in yaso sai ki gane waye uban ki" "haba Hajiya..."Alhaji ya fada. "Saka baki kaima ka miko min naka makullin" "duk bata kai haka ba" ya fada yana maida hankalinsa ga abinda yake yi.
  Gajiya tayi da tsayuwa tace"na tafin ku" babu wanda ya amsa mata cikin iyayen nata, ita Hajiya fushi shi kuma jin bata amsa mata yasa shi datse bakinsa yana tsoron amsawa cibi ya zama kari.
   Da kafarta ta taka har titi, zuciyar ta na wata irin tafasa banda Hajiya uwa ce da tace waye ya saka ta cikin yanayin da take? Tun tuni ta nuna mata aure take so amma taki sauraron ta. Hawaye ta goge sanda ta duba Jakarta taga babu komai, Allah yayi mata taimako akwai ATM card dinta a purse da ta shiga uku yau. Duk wanda ta tare tace ya taimaka mata ya ajje ta banki, in ta ciro kudi ta biya su sai su ki. Wasu ma in ta nuna masu katin sai suyi dariya suce bige ne...
Daga bayanta taji horn don haka ta juya don ganin waye?. Baban ta ne, take taji sanyi har ranta don tasan tsayuwar ta ta kare.
  "Me ya hada ki da Baraka?" Ya tambaya daga ciki ba tare da ya bude ba. Shiru tayi tana kokwanton anya bai sani ba ko kuwa so yake ta fada masa da bakinta? A'a ranar da malam yazo ai shi ya fita, saboda ba lallai in ya sani ba.
  "Babu komai" ta fada a takaice. "To ki dai bata hakuri kin san fushin ta ko?..... Ni yanzu zan wuce Suleja kanin ki Habibu babu lafiya" "Allah ya bashi lafiya" ta fada tare da rabuwa dashi don babu alamar zai rage mata hanya bare ta sa ran zai kaita ne. A ranta haushin sa ne fal! Wata kila da ya rike kansa da Hajiya bata yi ta walagigi da rayuwar su ba,don ikirarin tana da kudi.
   Ta sha tsayuwa kafin ta samu don haka a latti tazo makaranta. Allah ya taimake ta komai yazo mata da sauki yan kuskuren da zata gyara kadan ne.

Duk yadda ta dau lamarin Hajiya abun ya wuce tunanin ta sosai ta fice a harkarta tayi kukan tayi rokon amma duk a banza, ita kanta duk ta fige ta lalace kamar ba _Raliya diyar Hajiya Baraka_ ba. Tunani ne fal ranta kan wa zata samu don ya sasanta su ita dai kaf dangin Hajiya babu wanda take ganin kansa da gashi sakamakon biyayyar da suke mata saboda yan canjin hannunta kuma tana tsoron fallasuwar asirinta don bata yaya amanar su take ba. Kawayen ta ma dai duk tafiyar daya ce, ba wani tarbiya ce dasu ba.Take kuma tayi murmushi don tuno wani abu.
  Wanka ta shiga tayo, ba wata kwalliya dama ta jima bata yi ba.    Doguwar riga kawai ta zura, tana fatan Allah yasa hakan ta ya cimma ruwa. Purse dinta ta dauka wanda dari biyu ce kawai kuma itace last cash dinta.
Titi ta fito ta samu Napep tayi masa kwatancen inda zata je, babu zato yace ta hau a dari. Murna itace har da godiya. Mamaki yau itace haka wai tana neman ragi?.
  Da sanayya shi yasa Maigadin ya barta ta shiga. A reception ta samu yan record, su ta tambaya ko Dr Kulu tana nan? Eh suka bata amsa. Tare da bata umarnin ta jira yanzu tana wani operation ne. Gefe can ta zauna bakinta dauke da istigfari wanda ya zamar mata jiki. A yanzu bata damu ta auru ba burinta daya ace yau jikinta ya bata Allah ya gafarta mata sannan ta daidaita da mahaifiyar ta.  Tana nan zaune har tsawon awa biyu, kafin messenger yayi mata sammaci. 
Bata office dinta tana wani dan daki dake kamar parlour. Da sallama ta shiga kanta a kasa. Guri ta nuna mata ta zauna kan wata sofa, itama zaune take tana shan coffee, sai da ta gama tas! Sannan suka gaisa har tana tambayar ta ina Hajiyar?. Kanta ta sauke kasa tana wasa da yatsunta kafin wani abu sai hawaye shar! Kamar an bude  famfo. Sosai hankalin Dr ya tashi, sai da tayi mai Isar ta sannan ta fara.
  "Dr. Ina cikin matsala ne.. Na duba kaf wanda Hajiya ke mu'amala dasu ke daya ce kawai zaki rufe asiri na, shi yasa na taho gurin ki don Allah wannan ya zama sirri tsakani na dake da kuma Allah, kin tona shikenan..........." Bata boye komai ba ta fada mata tana hawaye tare da fadin "tsautsayi ne, wallahi tsautsayi ne Dr, amma wallahi na tuba kuma ban sake ba. Hajiya zargi na take yi gani take duk laifi nane bayan tana da nata kason a ciki...." "Dukka na fahimce Raliya amma kafin nan, why kika saka kanki a wannan harkar?  Nan fahimta tun ranar da aka kawo ki nan sai dai ban tabbatar da cewar hakan bane. Tabbas jikinki bai nuna alamar mu'amala da namiji ba amma kin riga da kin _rasa budurcin ki_...." Wani kuka Raliya ta saka wanda ya katse maganar Dr. Sosai take kukan na dumbin dana sani da rashin madafa tilas ta bawa mai sauraron ta tausayi. Duk iya lallashin Dr tayi amma taki shiru hakan ya tilasta mata fara fada
  "Akan me ba zaki yi shiru ba? To ki ci gaba da kukan idan har kukan zai dawo da hannun agogo baya, ya kuma canja abinda ya faru" ta fada tana shirin mikewa. Hannunta ta rike tare da fadin "kiyi hakuri" ta kuma share hawayen ta. 
  "Raliya, ki nutsu kuka na nake bane kinga Allah babu laifin da baya yafewa matsawar an tuba kuma ba shirka bace, kuma yana hukunci ga karamin laifi matsawar an dawwama cikinsa. Kar hakan ya taba damunki kowa yana kuskure mafi kyawu shine kawai ka tuba. Ki dage ki tuba ga Allah shi kuma zai yafe laifin da kika masa. Abinda nake so dake shine ki saka a ranki cewar wannan abun ba mai kyau bane it always result in rasa budurci, kamar ke kenan. Idan har tuban zaki yi to fa lallai  sai kin kiyaye ga duk wani abu da zai tuna maki waccar harkar ki kuma guji shiga bandaki ki bata lokaci hakan zai tuna maki da shaidan zai kuma kawata maki jikinki, gurin tsarki ma ki kiyaye ki wanke jikinki sosai amma kar ki dade.  Batun Hajiya kuma insha Allah gobe ba sai jibi ba zan je na same ta... Kuma ko babu komai akwai sirri tsakanin likita da patient. Kuma ni kika zaba na san sirrin ki why zan tona?" Sosai suka yi hira kafin tayi mata sallama zata tafi. Dubu tabata ta amsa da kyar. Har gate ta rako ta ta tarar mata napep ta kuma bashi kudin da zai kai ta har kofar gida, sosai kuwa taji dadi dama bata da na zuwa makaranta gobe.

Da yamma bayan laasar ta gama duk wani abu da tasan zata yi a asibitin. Gidan Hajiya Baraka ta nufa don tana da yakinin yanxun ai ta dawo gida.
  Tayi saa dawowar ta kenan daga gantalin ta. A bedroom ta same ta tana kwalliya. Sun gaisa sosai tana fadin
  "Dr, kice gidana ba ciwo ba mutuwa an ya baki yi batan kai ba kuwa?"
Murmushi tayi kawai tace"wata magana ce ta kawo ni shi yasa ma na biyo ki har nan"
"Kice ta samu kenan?" Ta fada tana dariya. "Kusan haka" Dr ta bata amsa.
Sai da ta gama kwalliyar sannan suka nutsu.

"Jiya Raliya taje har asibiti ta same ni ta kuma fada min duk halin da kuke ciki"
"Ki ce kara ta ta kai maki"
"Ko daya.... Ki saurare ni mana Hajiya tukun. Kar ki mance cewar hannun ka fa baya rubewa ka yanke ka yar"
"Ai wannan da ne kifa likita ce ku kuke yanke hannun in ya rube"
"Tabbas muna yankewa in ya rube ko ya damu mutum da ciwo amma daga nan sai an yaki bari na jikinsa an yi dashi kuma ya tashi daga ciwo zuwa nakasa wanda baa fata.
  Hajiya ina fada maki ke uwar zamani ce dole ki tafi tare da zamani, lokaci na kunya tsakanin uwa da yaya ya wuce tun tuni yanzu jawo su a jiki don sanin wani hali suke kin gane? Kwace mota da waya da kuma fushi da ita dukka ba zai gyara komai ba sai ma sake lalatawa abinda bata yi a da ba to wallahi yanzu zata iya. Tana cikin rudu da damuwa sosai kinga zata iya fadawa shaye shaye ko ta fara tunanin laifin ta yafi girman yafiya tunda ke mahaifiyar ta kin yi fushi da ita to yaya ga ubangijin ta fa?.
   Wannan abu ai *KALUBALEN MU* ne gaba daya kowa yana da sa hannu a ciki wanda magana ta fisabilillahi naki dana mahaifin ta yafi yawan. Kin hana ta aure saboda kina tunani yadda kika yi mulki a gidan ki itama dole sai tayi? Ba zai yiwu ba. Da kin bar ta tayi aure tun da darajar ta ta auri wanda take so su tashi tare ai yafi, ai yanzu lokacin sharadin aure ya riga da wuce, in har ka samu nagari to kawai ka aura sauran abubuwa kuma Allah zai iya mana.
Ni dai yanzu so nake a naki bangaren ki kiyaye wasu abubuwan.
1. Hira da ita da janyo a jiki kamar bata labarin yaya kasuwancin ki yake ita kuma yaya makarantar su? Bata labarin yadda yanayin makaranta yake a da, da dai sauran su. Kamar kuyi girki tare, fita unguwa tare, raka ta makaranta da sauran su. Abinda dai zai saka ku shaqu ya zama babu wani sirri da zata iya boye maki ko da ta boye ya zamana ke da kanki zaki iya ganewa.
2. Ki sa ido sosai akanta, waccar wayar kar kiyi bincike kanta, saboda gudun bacin rai. Ki canja wata, ki hana ta saka waya a password ko wani pin ta hakan zaki san wani amfani take yi da waya? Amma kar ki tsaurara bincike, kema kina iya bata taki kamar ki nuna mata wani video kice kalli aka yi kaza aka yi kaza. Ki amshi time table dinsu daga gurin level coordinator don yaran yanzu suna iya baki ba daidai ba, yadda zaki san lokacin fitar ta da kuma dawowar ta. Ki kuma rinka yawan kai mata ziyarar ba zata makaranta.
3. Na karshe ki saka ta a cikin addu'a, don adduar uwa zuwa Allah babu hijabi, ki dage, ki dage sosai."
  Sosai jikin Hajiya yayi sanyi, hakika Dr bata yi karya ba duk kusan laifi nta ne ita da gani take ai bata da lokaci na wannan abubuwan amma yanzu an haska mata taga haske sosai kuma zata kiyaye sosai. Hatta tsakanin ta da Umar zata gyara amma wannan da kanta.
  "Dr kulu hakika na gode sosai ban ma san ta ina zan fara ba, nagode, nagode kwarai kuma insha Allah zan yi duk yadda kika ce"
"Nike da godiyar amsar da na samu... Amma wannan sirrin mu ne kar ki nuna mata kunsan taje gurina"
"Baki da matsala da wannan.... Amma bara a kawo maki abun sha ko"
"A'a nagode nasan yanzu yara sun dawo suna can suna jira na.... Kuma don Allah ki mance wannan abun"
"Insha Allah".
Har gate ta raka ta gami da jefa mata tsaraba don ta kaiwa yara.
  Maimakon ta wuce dakinta sai ta wuce dakin Raliya, tun daga kofa take iya juyo sautin karatun ta na alqur'an wanda ya cakude da kuka cikin raunanniyar murya. A hankali ta tura kofar tausayin yar ta yana dada ratsa ko wace gaba ta jikinta. Kujera ta samu ta zauna. Itama tana ganinta ta katse karatun tare da zuwa gurinta ta kifa kanta kan cinyar ta gami da sakin sabon kuka tana fadin
  "Hajiya, ki yafe ni don Allah ki yafe ni, kiyi min afuwa wallahi na tuba tsakani na da Allah kuma na daina..." Wani kukan ne ya sake cin karfinta. Hajiya ta shiga bubbuga bayanta tana fadin"ya wuce Raliya Allah ya shige mana gaba baki daya..."
  Toilet ta raka ta ta wanke fuskar ta sannan ta fito suka tafi kitchen tare da ita. Girki suka yi tare tana ta kokarin janta a jiki kamar yadda Dr ta fada mata.

Yau ta kama asabar ta karshen wata don haka yau Hajiya ke zuwa stores don sayen abubuwan amfani. Tare da Raliya .. Ta shirya yin tafiyar don haka da yan mintuna sun fice. A mota tana ta kokarin jan ta da hira amma ta lura har yau ta kasa sakewa da ita sosai.
  Shop rite suka fara zuwa inda suka fara sayayyar anan ta kayan masarufi da sauran su. Kamar daga sama take jiyo kamshin sa amma bata tabbatar da hakan ba. Tana juyawa kuwa suka yi ido hudu dashi. Ras! Ras!! Gabanta ya fadi ganinshi tare da wata mata da tsohon ciki tana tafiya da kyar! Alamar haihu ko yau ko gobe. Babu ko tantama wannan itace matar tashi. _Ibrahim_.............


*AMMIN SU'AD* ✍✍



*SHATUU* ❤

KALUBALEN MU! Where stories live. Discover now