PART 19

1.5K 166 6
                                    

✨ *KALUBALEN MU* ✨

*AMMIN SU'AD* ✍

🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

           *19*

A kanta yayo da sauri ganin tana ta wani fisge fisge, kanta ya daga sai ta fara wani karaji wanda ya janyo hankulan mutanen dake tsaye. Hakan ya tilasta shi daukar ta tare da taimakon wasu yan mata guda wanda yake tunani ko yan MSS ne tunda shigar su da kamalar su kadai zata fada maka hakan.
  Shi ya taimaka masu saka ta a baya, ya kuma shiga gaba da sauri a rikice gaba daya.
Sai da ya hau kan titi sannan ya fara tunanin ina zasu je kuma? Ko Ya kai ta gida? A'a, take kuma ya juya kan motar ta sa. A bakin wani islamic hospital wanda suke treating it in matsalar ta ya faka. Jaddada masu yayi da su rike ta da kyau bara ya fito. Ciki ya shiga yayi masu bayanin komai, da wasu mata aka hado su suka fito da ita tare.
  Wani daki aka kaita, sai ga mai rukiyya yazo, goshin ta ya dafe yana karanto mata wasu addu'o'i a zuci yana tofa mata akai akai. Nan da nan kuwa ta ci gaba da karajin. Ya dade yana yi mata karatun kafin kuma barci ya dauke ta. Turare ya akai aka kawo ya tukake ta dashi take ta sake hawa, ya ebo wani ruwan addu'a yana ta tofa wanda shima ya dau lokaci sosai. Sai da ta dawo daidai sannan ya kira Ibrahim din wani office. Farko ya tambaye shi nasabar sa da ita tare da tambayar abinda ya jefa ta cikin wannan yanayi? Ya kuma bashi amsa. Kafin ya fara cewa
  "Kamar dai yadda na gani akwai aljanu a jikinta wanda suka aure ta, shi ya saka a duk lokacin da wani ya furta maganar auren gare ta hakan yana iya faruwa. Amma idan kai har da gaske kake auren ta zaka yi din to mu kuma muna da magungunan da har dai ta dage to insha Allah zaa samu waraka a jikinshi" "Malam tabbas a shirye nake sosai auren ta zan yi babu wasa. Yanzu sai ka fada min kudin sai na biya"
"Masha Allah... Akwai na hayaki sha da kuma wanka sai turare sai dai ka san sha'ani na maganin mu akwai kudi" ya fada yana zaro wata doguwar takarda. Marking magungunan yayi tare da mika masa. Ibrahim ya amsa ya gani kafin yace "gaskiya Malam ba zaa samu kudin duka ba, saboda yanzu ina cikin yanayi mai daki ce ta kusa haihuwa saboda haka duk na bada kudin wajen siyayya..... Sai dai ka bada rabi in yaso daga baya sai na dawo na sayi rabin"
"To hakan ma yayi madallah.. Yanzu sai muje na baka ko?"
  Tare suka fita ya hado masa magunguna gaba daya ya sha mamaki amma malamin yace ya bar kudin fatan su ai su Allah ya bata lafiya. Sosai yaji dadi tare da yi masa godiya mai tarin yawa ya taho.
    A kofar gida ya tsaya wannan sisters din suka taimaka mata wajen shiga gida. Yace suyi masa magana da Hajiyar ta. Tana zaune suna ciniki aka shigo da ita, daki ta ce su wuce da ita kafin ta biyo su. Duk yadda abin ya faru ta zayyana mata sannan ta fita. Cikin mutunci sosai suka gaisa dasu  yayi mata bayanin magungunan sannan ya wuce. Tana dawowa suma suka ce tafiya zasu yi sosai tayi masu godiya tare da saka Driver ya maida su school.  Yau da kanta ta tsaya bata magunguna don yanzu ta fara shiga hankalin ta duk tafi zargin kanta da janyo masu wannan abun wata kila da ta maida hankali kan role dinta na uwa da duk hakan bata faru ba.
  "Raliya, waye wannan yaron?" Ta tambaya itama ganin banu amfanin boyewa ya saka tace "shine Ibrahim dina" "Ibrahim din ki? Ya dawo alhamdulillah" ta fada da murna, ita kuma sai hawaye sha! Tana fadin "Hajiya, ba dawowa yayi ba fa ban san me yazo yi a makaranta ba kila program yazo gani. Hajiya yaushe zai aure ni a wannan yanayin? Kuma shi yana ma da matar sa... Sune fa wanda muka hadu dasu a Store har muka yi canjin riga to matar ta sa ce" wasu hawayen ne suka sake bin kumatun ta tana jin ina ma baya ya dawo ta gyara kurakuran ta. Ashe dai musulunci abu ne mai sauki in ka bi sharadin sa, idan kuma ka haura kayi ta haduwa da matsala kenan? Gaskiya ne dazu da malam yace _.....babu amfani a cikin duk abinda Islam ya hana...._ tabbas zancen sa haka ne. Da tun farko bata ni son zuciyar ta ba da ta dace a rayuwar ta.
  Ita kanta Hajiya yanzu nadama mai tsanani ta shige ta yanzu gashi don wani dalili nata suna cikin wahala. Kafadar ta ta dafa tace" Raliya, kar ki damu da hakan ko wani bawa da tasa kalar qaddarar wadda baya iya tsere mata... Ki yarda da Allah, ki yarda ba zai taba cutar ki a rayuwa ba. Kin manta Allah shi daya ne sarkin da bawansa zai yi masa laifi ya tuba shi kuma ya yafe masa har ma ya maida wannan tuban lada ya saka cikin aljannah" hannun ta ta saka ta goge mata hawaye tace "nasan Allah yana tare da yata shine gatan ta ko da yaushe" sosai ta kwantar mata da hankali duk da ita can ranta a takure take.

KALUBALEN MU! Where stories live. Discover now