PART 07

1.6K 188 3
                                    


✨ *KALUBALEN MU* ✨

       *AMMIN SU'AD* ✍

                  *8*

shatuuu095@wattpad

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

_United we stand and succeed our ambition is to entertain and motivate the mind of readers_

Babu yadda zan yi haka na hada kayansu tsaf, ranar ban runtsa ba sai daya. Na shiga kitchen bayan na gama hada kayan tafiyar su.  Kaza na dauka guda hudu nayi mata dambu dashi sai Meat pie da doughnuts, nayi na saka cikin robobi.
  Tun asuba na tashi, nayi masu wanka tsaf! Passport din Nana na dauko mata, ita kam Maama bata dashi kila in sun je can zasu yi mata.
  Tea kawai suka sha Mallam Tanimu ya tafi kai su karfe shida da rabi. Haka na dawo gida ni daya kamar mayya, na gyara gidan na gama. Nayi wanka ina tunanin menene next line of action dina? Tunani ne yazo min akan kawai na fara Sana'a kila hakan na iya kore damuwar raina na daina kadaicewa amma kuma ai ba wannan nake bukata ba.....
   Ina nan zaune kiran Alhaji ya shigo min na daga da sallama ya amsa, na gaida shi nan ma ya amsa.
    "Kiran ki nayi nace in kina da lokaci gobe ki zo gida ina neman ku"
  "To" kawai nace dashi ya kashe wayar sa. Ajiyar zuciya nayi ina tunanin ko menene Alhaji ke neman mu? Oho.
  Tun safe nayi shiri na tafi, acan na iske dukkansu a side din Hajiya har Nadiya, acan na karya ma muna ta hirar zumunci har da yaransu duk sun zo baki daya ana ta tambayar ina su Nana sai dai nace suna Kaduna.
  Sai da muka gama komai muka nufi  side dinsa. Yana nan kwance kan sofa, yana karatun jarida _daily trust_ . Guri muka samu muka zauna, sai da muka gaisa yake tambayar mu daya bayan kowa yaya gidan ta da kuma yaranta?. Sai da ya gama tukun ya gimtse fuska gami da fadar
    "Na san duka kun yi mamaki kan tara kun da nayi anan ko? To ba wani abu bane illa magana nake so muyi daku shi yasa na tara ku gaba daya a tare. Wato ribar  gona ta nayi ta tarawa har na tsawon shekara uku, kuma alhamdulillah kudi sun taru miliyan goma shif! Sanin kanku ne babu abinda na iya sama da kasuwanci yadda nagada to kuma haka nake so na koya maku shi. Na yanke shawarar ba ko waccen ku miliyan daya daya ta ja jari don bana son zaman banza sauran hudun kuma zan rabawa iyayen ku daya crew daya matan yayan ku kuma na basu rabin miliyan miliyan.... Amma ya kuke gani?"
  "Duk yadda kace haka zaa yi Alhaji. Mun gode sosai jazakha Allah khairan"
  "Amin" ya amsa. Dukkan mu muka yi masa godiya. Bank cheque ya bawa kowa muka tafi. Dukkan mu muna murna da abinda yayi mana.

Kwana biyu tsakani na shirya kayana zuwa Lagos, jirgin yamma na bi na tafi, taxi na samu har quarters din su Ahmad kafin na karasa na tsaya wani babban pharmacy Don kudirar da Abinda zuciya ta ke raya min, sede Duk yadda naso su bani maganin kara libido suka ki a cewarsu prescription only drug ne basa dispensing se idan daga Asibiti aka turo aka, inaji haka na wuto gidan da yake zaune. A kofar gidansa nayi parking, na sallami mai mota na bubbuga gidan, Allah ya taimake ni aka bude amma ba shi bane. Mai masa gyaran gida ne da girki wai shi Adekunle, sosai muka gaisa dashi nake tambayar shi
  "Ina Ogan ka?"
"Ai tun shekaran jiya ya tafi Delta Madam, amma ina zato yau zai dawo"
"OK" na amsa masa. Muka shiga gidan, ina ajje kayan  na fito nace
"Adekunle, kaje kawai ka bar min  aikin zan karasa masa"
  "OK, madam thank you"
  Kitchen din na shiga don ganin me zan yi masa. Adekunle ya riga da ya fara yankan vegetables don haka kawai sai nayi masa taliya da miyar ganye, kafin isha har na gama. Wanka nayo nayi sallar isha ina dakon dawowar sa.
  Karar mota, don haka na leka ta window din bedroom dinsa, shi aka sauke a mota. Ban fito ba saboda ina son ganin irin tarbar da zai min.
    A takun nutsuwar sa ya bude gidan. Tun a parlour yake jin kamshin ta amma ya tabbatar ba ita bace. Suit dinsa ya cire daga shi sai singlet. Ya cire wandon da takalmi ya bar sock kawai da boxer wani mahaukaci yunwa yake ji, saboda haka dining Ya nufa. Abincin ya fara zubawa amma tabbas ya san wannan girkin bana Adekunle bane kamar na _Maryam_ to amma ai yasan _maryam_ tana gida. Sai da ya kammala ci sannan ya daura alwala a sink yayi sallolinsa sa.
Bai shiga daki ba sai sha biyu da mintuna.
Yana kunna fitila suka yi ido hudu, Allah kadai yasan farin cikin da yayi amma yaki nunawa.
  "Ke kuma titse kika zo yi min?"
"Titse kuma?"
"Eh mana". Dan murmushi kawai nayi. Shi kuma ya zari towel sai toilet ya jima kafin ya fito.
Mai kawai ya shafa da turare, ya zura dogon wando.  Gadon ya hayo ya kwanta, na matsa kusa da shi na dora kaina kan kirjinsa, wani Yarr! Naji kamar yadda na tabbata shima yaji, saboda yaushe rabon da muyi haka?
  "Honey, kamar baka yi farin ciki da zuwa na ba"
   "Ba haka bane kawai dai na gaji ne ba wani abinda zan iya" naji haushi sosai ne yake nufi bani da wani buri sai bukata?
   "Nima bashi nake nufi ba.... Zuwa nayi mu yi wata magana" nayi mamakin ganin yadda yake murmushi sai nake tunanin anya ko Ahmad yana da lapiya? Babu wani abun dake damun shi kuwa?
  "Ina jin ki"
"Baba ya bamu kudi yace mu fara juyawa shine nazo na fada maka kuma muyi shawara"
"Yayi, ya kyauta sai ki shirya ki sabi ina zaki ko?"
"Da Oman nace zani na sayo turaruka da dogayen riguna". Dan kiss yayi min
  "That's Mairo na, insha Allah gobe Victor zai kai ki sai kiyi abinda ya kamata like jibi ma sai ki tafi" ina son magana amma kawai na hakura.
   Fitila Ya kashe mana  sannun ya gyara mana kwanciya. Ina jin saukar numfashin sa alamar yayi barci. Jikina na janye nayi gefe can, ban san ta kuma wace hanya zan bi wajen gyara tsakanin mu, Allah ka kawo min dauki.
     Danayi sallar asuba bamu koma, lokacin ya bijiro min da nashi bukatun. Nayi murna ba yar kadan saboda nasan duk ranar da tashi ta kawo shi ana shan zuma...... Mun yi nisa wayar shi ta fara, a zatona bai ji, sai naga ya sauka a kaina. Sai da ta katse aka sake kira sannan ya daga, da kyar yake iya magana. "Hello....., what? ...........serious?......... Ok bani minti ashirin haka...... I'm very happy gaskiya" yana kokarin tashi, na rike shi gam!. Ture ni yaya "Maryam, ba ki ji kirana ake yi ba?" Cikin kuka nace "please Ahmad kar ka bar ni a wannan yanayin" "oh no! Maryam in na zauna zan rasa millions ne kiyi hakuri mana". Yana fadar haka ya fada toilet, bai jima ya fito ya shirya a gagauce ya fice.
  Na fi awa ina kuka, kafin na yunkura na fada toilet. Kuka nake sosai saboda aikata abinda zuciyata ke tunzura nayi, ban yi wani dogon tunani ba. Na tsinci kaina a biyan bukatar kaina da kaina. Abun rudin shedan sai naji duk damuwar raina ta yaye har ina tuhumar kaina me yasa tun farko na kulle kaina na kasa aikata hakan. Sai da nayi wanka na fito amma kasan raina ina jin babu dadi sosai.  
   Cikin riga da zani na shirya ta atampa vlisco mai kyau. Ina yafa mayafi naji bugun gida, naje na bude. Ashe Victor ne, na dawo na shirya muka tafi. Nayi booking jirgi amma sai jibi zai tashi, sai yamma muka dawo, a zato na ma ya dawo ashe yana can. Sai goma ya shigo yayi sallah yaci abinci sannan ya kwanta, ban wani damu ba inda sabo ai na riga dana saba.
   Washe gari na yini shirin tafiya ta, ba laifi ya dan bani shawarar abinda ya kamata nayi.   Har da bani additional two million. Ranar tafiya bai je office ba, ya tsaya raka ni, sai da na shiga jirgi tukun ya tafi.    A cikin *Etihad Airways* muka tafi. Ba jimawa sai gamu mun sauka a *Muscat international Airport* Bayan bincike da komai. Na fito nan bakin airport na tari Taxi sai  *Al Qurum street* nan *Coral Muscat Hotels and Apartment*. Daki nayi booking tun ina Lagos, Allah ya taimake ni saura dakuna hudu. Suka bani key na tafi. Ranar su suka ta kawo min abinci har dare. Washe gari tun safe na shirya nayi *All Wilaj st.* naje can *Jawaher Oman Jewelries* tabbas kam suna yan kunnaye da yari masu kyau tun nasu na gargajiya. Sun kuma ji dadin gani na. Da Marketing Developing Manager dinsu muka yi ta zagaye tana nuna min sabbabin  abubuwa da kuma tsofaffin, sun burge na kuma saya. Ranar kam can na yini. Sai yamma na kammala na basu komai nace su aika min shi can Nigeria.
  Ko washe gari ma ban zauna ba can *City center* dake *All Seeb* na je na saro turaruka direct daga hannun kamfanin *Amouage* turaruka ne gani na fada wanda suke daya daga cikin best brands da suke saida turaruka ba na shafawa kai har wuta na abin baa cewa komai. Shima dana gama na basu su aika min gida.
  Da safe kuma na tafi shagon saida abaya. A nan *Anarkali* na saya masu kyau sannan naje  *Dohat All adab st.* nan *Muscat Grand Mall* nayo siyayya ta.
  Kwana biyu na kara inda na zaga gidajen tarihi nsu kamar su  *Bait All zufair* gurin bajakolin girke girke na mata, sai na kuma je *Funtazmo* nan ma na sha kallo abuna.
  Ranar litinin na bar Muscat zuwa Dubai. A *Fukhruddin Hotels Apartment* na sauka.  Bana son na dade don haka ranar da naje ranar na fita sari *Ibn Batutta* kawai naje nayi sari na na koma.
  Kwana biyu na dauko hanyar dawowa. Nayi niyya sauka Lagos amma naga babu wani amfani don haka jirgi mai zuwa Abuja na bi na tafi kano.
Sai da na isa nake saidawa Ahmad dawowa ta yace" babu matsala ai, nima ina zato cikin week din nan zan je *Robot Gordon University* ta _Scotland_ zan yi wani career course akan _Oil and Gas mining_ kamar na sati tara, so nama yi zaton kiran ki in kin gama mu sai ki zo mu taho tare ko"
  "A'a ai kaga gasu Nana kuma saboda school"
"Good... Dame dame kika siyo?"
"Kayan mata ne na sakawa da turaruka haka"
"Iye good..... May be dai baki sake jina saboda zan tafi Warri da Niger Delta na kwana biyar, daga nan kuma zan wuce"
"Amma ba zaka zo ba _Honey_ wata tara fa ba kwana tara ba ai ya kamata mu hadu". Na fada cikin damuwa sosai saboda ina hango kaina na tsawon wata tara babu wata kulawa yanzu ma na watannin baya na kasa.....
  Dan tsakin da yayi ne ya katse ni kafin yaci gaba "Zan aiko maki all the necessaries and I know zai ishe ki har ki dawo......... Bye Baby ana jira na"
     Bai jira ba naji _dif! Dif!! Dif!!!_ alamar ya katse kiran baki daya. Dan guri na samu na zauna bakin kujera saboda ji nake kamar ba zan iya tsayuwa ba.
  Wasu hawaye masu zafi naji a kunci na sun fara zubo mun, ko sau daya ban taba hango ranar da Ahmad zai zabi wani abu a duniya fiye dani ba. Ashe zancen iyayen mu gaskiya ne da suke cewa _Namiji hankaka gabansa fari bayan sa baki..._ yau kam na gani da gaske a kaina. Duk ina soyayya, kulawa da kunar dake tsakanin mu dashi? Me yasa Ahmad ke yi min haka zaton shi kudin shi shi zai wadace ni a rayuwa ta. Ni kam A'a shi din nake s _AHMAD MUHAMMAD BATURE_..........

Amma is like Maryam ta manta abu kwaya daya? Ina tunanin da tayi focussing akanshi da ta samu rangwamen wasu abubuwan.

Vote

Comment

Recommend

Share d love and keep the chain moving


*_Shatuuu ♥️_* ✍✍

KALUBALEN MU! Where stories live. Discover now