✨ *KALUBALEN MU*✨*AMMIN SU'AD* ✍
*10*
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
_United we stand and succeed our ambition is to entertain and motivate the mind of readers_Hello my people....... My wattpaddians d page is yours and thanks for the votes
Cikin kwanakin nan sosai ciwon yake damuna na kuma tabbatar yana daga cikin kewar Ahmad da nake ciki.. Hakan yasa na fara exposing kaina to social media sosai, a haka na fara developing interest akan abubuwan da na san ko daya basu dace ba. Amma yaya zan yi? Hakan nan nake ki abuna, kadaici ba sosai yake damuna ba saboda nakan yi abinda nake so.
Cikin haka Ahmad ya cika sati tara ya dawo. Ranar da zai dawo shiri kam kamar wadda zata tari sabon ango haka na dinga yi. Jikina kam ya sha gyara sosai don ina zaune ni daya sai naji kamar ana tsokano ni. Girki kam na san yayi masa yawa amma don farin cikinsa haka nayi masa. Su Nana ma duk mun yi gayu abun mu, sai wani murna muke sosai.
Karfe uku Malam Tanimu yaje tahowa dashi daga airport amma bai karaso ba sai bayan magriba. Lokacin nayi kyakkyawar shiga ta cikin wata yar riga orange tsayin ta iya guiwa armless.
A kasaitance ya shigo, cikin suit navy blue yayi kyau har ya gaji, da gudu na taho na rungume shi. Ya shafa bayana tare da fadin "sannu da gida"
Murmushin da nake ya hana ni amsawa ma. Ya kama su Nana daya bayan daya suna masa sannu da zuwa ya amsa musu tare muka hau sama ina ta yi masa surutu.
Shi kan shi yayi kewar ta kuma yaji dadin ganinta sai dai bashi da wannan time din. Ya san so ya kuma san illar so, ba zai taba bari ya bawa so damar da zai bata masa duk wani harka tashi gani yake da ace tun da bai yi aure ba to fa da yanzu ba zai yi din shi yanzu mace bata wani burge shi business dinsa ya fiye mashi komai.
Muna cin abinci yana ta danne danne nace "Honey, it seems kamar baka yi murnar ganin mu ba ko? Instead of irin ka rinka tambayar yaya muke how was the life in your absence amma kana ta danna waya?" Bai ce dani komai ba bai kuma fasa abinda yake yi ba. Maama ce tace"Daddy, Mummy fa bata da lafiya kullum tana kuka a daki" kallo nayayi ni kuma da kauda ido na ina kallon Maama ina son sanin yaushe ta san ina kuka ne?....,.,....... Muryar shi ce ta katse ni
"Mamana, tell me me ya samu Mummy?"tace"I don't know... Tana kuka ne kawai a daki"
Tashi nayi na basu guri, dakin shi na tafi nayi shirin barci tunda nayi masa magana ya share ni to nima zai zo ya same ni.
Kamar awa sai gashi ya shigo. Toilet ya shiga ya fito yazo ya feffesa turare a kowacce gaba ta jikinsa sannan ya hayo gadon. A zato na zai neme ni amma sai ya share ni kuma gashi turaren ya cika min hanci ala dole nazo gurin shi tare da dora kaina akan kirjinsa.
Hannunsa ya kai ciki na yana dan latsawa tare da fadin "me ke damun ki?" Ban bashi amsa ba illa sake shigewa jikinsa da nayi cikin wani salo.... "Look! Yace dani.... Kafin yaci gaba da ke nake magana fa ko?" Tashi nayi na zauna har lokacin bance dashi komai ba.
Ina shirin mikewa ya fardo hannu na, naje na bugu da fuskar gadon. "Da ke nake magana ko?" Kukan da nake boyewa ne ya fito sarari nace "amma ai kaji na buge hannu na ko da katako? Ba kayi min sannu ba sai tambayoyi ni babu abinda ke damuna"
"Karya kike... Ki fada min ina sauraron ki"
Cikin hasala nace "me zai dame ni a rayuwa ta bayan kai Ahmad, babu? Me nayi maka ka canja min baki daya baka kula ni baka shiga sabga ta akan wani dalili tun ina nuku nuku har na aje kunya, daraja da kuma aji na na fada maka abinda nake so amma ko sau daya me ka taba yi akan hakan...... Ahmad tabbas da mutum kan iya ganin gabansa da ban aure ka ni ban wani san wani farin ciki a aure ba...."
Shima a hasale yace dani "ni kika yi da kin sanin aura?" Cikin fushi nace "eh". Ban taba ganin bacin rai cikin idonsa kamar yau ba tunda shi mutum ne da karya kaga bacin ransa.
Cikin wata murya ta tsantsar bakin ciki ya fara magana "it's alright Maryam ban taba zaton hakan daga gare ki ba all I thought is you're my greatest support ashe duk abin ba haka bane....... Hannuna ya ja da nake tunanin ya tsinke ya kaini gaban mirror "kalli kanki...," Ban gama nazari ba yaja hannuna. Sai daki na nan ya bude wardrobe dina mai kofa takwas da ke cike da kaya. Kuma jani kasa har na bubbuge kafata saboda sauri, kitchen ya kaini na ga ko ina sannan ya dawo dani parlour ya yardar kan kujera.
"Kin ga gidan nan gaba daya komai a wadace nake baki shi Maryam ki fada min meye bana maki da kike tunanin har kin yi da kun sanin aure na"
Kamar nayi shiru saboda na gama tsorata dashi amma na dake "girman gidan da ka ajje ni ne farin ciki? Ko kuma duniyar ka? To ka sani indai wannan ne farin ciki to gara nayi zamana a gidan ubana don ka san goman gidan zai shiga saboda kai shaida ne baa a talauci ka auro ni bare kayi min gori kace don duniyar ka na aure ka..... Ahmad ni kai nake so kai kadai kayi wa zuciyoyin my adalci ka bari su sake ka dawo nawa don Allah. Ina cikin bukatar ka....." Na karshen ina rungume shi. Ture ni yayi gami da fadin
"Kin yi magana yanzu... I don't know when kika koma sex addict all you care is sex to bara kiji har yau ni na auro ki na biya sadaki ba ke kika auro ni sannan ki sani cewa ko uwar da ta haife ni bata matsa min bare da kike karkashin iko na........"
Jin motsin su Nana yasa ni tafiya gurin su, kila hayaniyar mu ce ta tada su. Hannunsu na kama muka koma dakin su, bani da bukatar ya biyo mu don haka na sakawa dakin key. Nana tace "lafiya mummy?" Dan yake nayi nace "cikina ke ciwo shine Daddy yace muje asubiti ni kuma bana son allura naki shine yake fada... Amma yanzu kuyi barci sai naje na bashi hakuri" "to" kawai suka amsa min.
Anan dakin na kwanta amma barci ya gagare ni, haka na tashi na nufi abubuwan da na sha da nufin yau mu ji dadi yana neman zamar min wahala gaba daya ji nake kamar nayi me...... Haka na dinga safa da marwa naje kitchen na samo kanwa na kafa kaina na fara sha sai dai bata je ko ina ba ta dawo gaba daya da kanta.
Wani sama sama na dinga jin kaina, na kankame jikina guri daya. Zuciyata ke tayi min zuga a kan na aikata wani abu... Zuciya ta ke ta neman biyan bukatar ta ta ko wani hali.... Kuka na sha ina son aikata abun da zuciyata ke zuga ni sai dai ina shaku..... Cikin kankanin lokaci na ji ba zan iya jurewa ba.
Hakan yasa na fada Toilet....... Kimanin kamar awa na gama abinda nake, wanka nayo na fito na jima gaban mirror na kifa kaina ina ta kuka, tabbas na san abinda nake aikatawa _istimna'i_ na san haramcin sa na kuma san illolin sa... Amma yaya zan yi? Ya Allah ka yafe ni, cikin yardar ka ba zan sake...
Ban tashi ba sai da aka kira asuba. Alwala nayo nayi sallah abuna na jima kan sallaya kafin na tashi... Dakin su Nana na shiga na tarar basu nan, parlour na dawo na same su suna kallo.
"Ya kuke kallo? Kun yi sallah da azkar ne?"
"Mummy, mun yi sallah amma ba muyi azkar ba"
"To maza ku tashi kuje kuyi"
"To" suka mike su duka... Ina tsaye naji takun sa ban juya ba bare na kalle shi gaba daya haushi yake bani ji nake yau da Alhajin zai bar ni na zauna gida to da tabbas na bar gidan sa.
YOU ARE READING
KALUBALEN MU!
General FictionKALUBALEN MU! It's all about masturbation..... How does it feels that you have desires, sexually aroused and your parents said you must finish your A level before aure? How do you feel when lust covered u and your husband said business first? How do...