PART 25

1.8K 148 3
                                    


✨ *KALUBALEN MU* ✨

   *AMMIN SU'AD* ✍

🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

     *25*

Nigeria se Baba! Se Baba!! Se Baba...... APC ce a Raye ~PDP~ ta mutu...... Yeeeeeeee

Na yunkura zan mike ya ya sake rike ni. Cakulkuli ya shiga yi min wanda ya saka tilas muka dara daga nan kuma ya sauya alalar zancen.
   Sai bayan shudewar awanni muka sararawa junan, sosai wannan abun ya faranta raina ban ji ko lokacin amarcin mu mun sake sosai haka da farin ciki. Mun gwada yadda muka yi missing juna da kuma yadda muke kaunar junan mu. Wanka kanshi tare muka yo muka shirya sannan ne muka samu nutsuwar more gajiyar mu. Sai dana ji saukar numfashin sa sannan ne na tashi na nufi toilet sam daren nan bai dace da barci ba kamata yayi na zauna nayi ta godewa Allah. Na fito na iske shi tsaye shima yana dakon fitowa. "Daban tashi ba haka zaki samu ladan ke daya ko?" Ya fada yana dan rankwashi na. Dariya kawai nayi.
  Rakaa biyar muka da dogayen sujadda kowa yana fadar tasa bukatar zuwa gun mai duka. Sosai hakan ya sake saka nutsuwa da farin ciki a zukatan mu. Muna komawa gado kuwa muka sake fadawa ruwa......

***    ****       *****

Tun daga wannan rana shima ya tattara shirgin ta ya watsar yana son gwada mata fushi da boren ta ba zai saka ya fasa abinda yake yi ba. Wanda hakan ya sake tunzura ta ainun dan abubuwan da yake ma ya daina su gaba daya.
 
Dama yana jiran wasu yan kudade da yayi planing wasu gidaje wa wani dan kwangila cikin satin kuwa kudin suka fito da sauran abinda ke hannunsa zai hada wajen yin hidima dasu. Wata Hajiya Fatima zarewa yar office dinsu da suke dan gaisawa matar kuma na sare sare daga Kano zuwa Lagos tana yin Business ita yabi Lagos yaje ya ebo laces da atampopi don an ce masa acan sun fi sauki har ma da materials masu kyau. Sai dare lis ya dawo gida da uban kaya, tana nan zaune parlour tana ta kallo Bibie dake koyan zama tana cikin keken ta tana wasa da kacau kacau. Da jin sallamar uban ta fara waige waige sai da ya gama shiga da kayan tsab ya rufo ko ina sannan ne yaje ya dauke ta yana mata wasa ita kuma sai bangala dariya take tayi abinta.
  Kusa da Habiba ya zauna yana fadin "sweet, baki ganni bane ko sannu?" Ko kallon shi bata yi bare ya samu amsa. TV din ya kashe nan ma tayi masa banza, kallon ta ya sake yi yace "bani abinci" ban yi da kai ba" ta fada a tsiwace. Bai ce komai ba ya danne fuahinsa yace "ga kaya can ki raba uku ki dau kaso daya ki ajje min biyun kin ji?" Na meye?" Ta tambaya "na kine da Raliya" ya fada "to ai sai ka kai mata baki daya don ni kam ai da sutura ta. Ita din dai da kake so ba matar hadi ba sai ka kai mata" tana gama fadin haka ta shige ciki. Kan gadon ta ta fada tana rusar kuka ta rasa  yaushe ne zata fara daina jin haushin Ibrahim ta san ba zata iya cire zazzafan kushinsa a ranta ba, tana jin kuna duk sa'adda ta tuna zai yi aure ne bayan ita. 
  Bayan ta yabi da kallo har ta bace masa a gani ya dawo da kallonsa kan Bibie  dake ta wasan ta. Ajje ta yayi nufin yi amma fur taki zama, zani ya dauka ya goya ta ya nufi kitchen don nemawa kansa abinda zai saka a bakinsa. Flasks guda biyu ya tarar da plate da spoon yana budewa ya iske tuwo ne sai miyar kubewa busshashiya.  Stool ya janyo dake kitchen Ya zauna ya cinye tuwon tas! Sannan ya sha  ruwa. Fitowar sa har tayi barci abayansa ba tare ma da ya sani ba. Sai dayaje daki ya kunto tukun ya kwantar. Shima bandaki ya shiga don yayi wanka, Ko da ya fito sai ya iske bata nan hakan ya tabbatar masa Habiba tazo ta dauke ta.
  Da safe kam Kano yayi jirgin karfe shida da rabi ya bi shi daya.  Yana son saka yan uwansa a ciki amma bashi da magoyin baya kaf cikinsu. Sabon gari ya fara shiga yayo sayayyar sa gaba daya ta kayan shafa sai yan abubuwa da suka rage masa  ya bari kawai gobe ya karasa message ya tura mata
  _Biba na, kiyi hakuri sai gobe zan dawo saboda ayyuka sun rike min kai ne nayi zaton dukka zan gama yau amma ban samu karasawa ba kuma office suna son report gobe_

Ba jimawa ita ma ta turo masa nata.
_Ka gama kunbiya kunbiyar ka ka fadi gaskiya ma....ko da yake in kaso ka dawwama a can ma_
Idonsa ya runtse sam bai ji dadin kalaman ta ba amma abun bai yi masa dadi ba, amma babu komi wata rana sai labari....

KALUBALEN MU! Where stories live. Discover now